Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 17

“Na Yarda”

Ka Zabi Sauti
“Na Yarda”
DUBA

(Luka 5:13)

 1. 1. Da Kristi yake duniya,

  Ya tausaya wa mutane.

  Bukatun mutane

  Ya biya musu;

  Ya ciyar da mayunwata.

  Ya warkar da naƙasassu,

  Guragu har da makafi.

  Kamar yadda zai yi a Mulkinsa,

  Da ƙauna ya ce: “Na yarda.”

 2. 2. Muna yin koyi da Kristi

  A rayuwarmu koyaushe.

  Muna nuna ƙauna

  Ga maƙwabtanmu,

  Don su san Jehobah sosai.

  Muna taimakon waɗanda

  Suke cikin matsaloli.

  In mabukata suka roƙe ka,

  Da murna ka ce: “Na yarda.”

(Ka kuma duba Yoh. 18:37; Afis. 3:19; Filib. 2:7.)