Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 16

Mu Yabi Jehobah Domin Dansa

Ka Zabi Sauti
Mu Yabi Jehobah Domin Dansa

(Ru’ya ta Yohanna 21:2)

 1. 1. Jehobah ya zaɓi Ɗansa

  Ya sarauci mutane.

  Zai yi sarauta da adalci

  Don nufin Allah ya cika.

  (AMSHI)

  Bari mu yabe ka Jehobah.

  Da Ɗanka Yesu Sarkinmu,

  Muna yabon ka da duk zuciya

  muna bin umurninka.

  Bari mu yabe ka Jehobah,

  da Ɗanka Yesu Sarkinmu,

  Wanda ka zaɓa don ya ɗaukaka

  sunanka da ikonka.

 2. 2. An naɗa ’yan’uwan Yesu

  Don su zama shafaffu.

  Za su yi sarauta da Yesu

  Su sabonta duniyar nan.

  (AMSHI)

  Bari mu yabe ka Jehobah.

  Da Ɗanka Yesu Sarkinmu,

  Muna yabon ka da duk zuciya

  muna bin umurninka.

  Bari mu yabe ka Jehobah,

  da Ɗanka Yesu Sarkinmu,

  Wanda ka zaɓa don ya ɗaukaka

  sunanka da ikonka.

(Ka kuma duba Mis. 29:4; Isha. 66:​7, 8; Yoh. 10:4; R. Yoh. 5:​9, 10.)