Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 144

Mu Rika Dokin Samun Ladan!

Mu Rika Dokin Samun Ladan!

(2 Korintiyawa 4:18)

  1. 1. A aljanna a duniyar nan,

    Allah za ya cire duk cuta.

    Waƙar yara, murna, salama,

    Duk za su cika ko’ina,

    Kuma za a ta da matattu

    Domin su zauna har abada.

    (AMSHI)

    Allah zai yi abubuwan nan,

    In muna ɗokin ladan nan.

  2. 2. A aljanna dukan dabbobi

    Za su kasance da mutane.

    Ƙaramin yaro zai bi da su,

    Duk za su bi umurninsa.

    Jin tsoro da kuma mutuwa,

    Za su daina damun mutane.

    (AMSHI)

    Allah zai yi abubuwan nan,

    In muna ɗokin ladan nan.

(Ka kuma duba Isha. 11:​6-9; 35:​5-7; Yoh. 11:24.)