Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 142

Mu Jimre, Aljanna Ta Kusa

Ka Zabi Sauti
Mu Jimre, Aljanna Ta Kusa
DUBA

(Ibraniyawa 6:​18, 19)

 1. 1. ’Yan Adam sun daɗe suna shan wahala,

  Ba za su iya taimakon kansu ba.

  Muna ganin hakan ta ayyukansu

  Domin dukansu ajizai ne.

  (AMSHI)

  Mu gode wa Allah don Mulkinsa!

  Yesu Kristi zai ’yantar da dukanmu.

  Zai cire duk masu yin mugunta,

  Mu jimre domin ranar nan za ta zo.

 2. 2. Mu sanar cewa ranar Allah na zuwa.

  Ba wanda zai ce wa Allah: “Har yaushe?”

  Domin zai ceci dukan halittunsa.

  Mu yabi Allah da waƙarmu.

  (AMSHI)

  Mu gode wa Allah don Mulkinsa!

  Yesu Kristi zai ’yantar da dukanmu.

  Zai cire duk masu yin mugunta,

  Mu jimre domin ranar nan za ta zo.

(Ka kuma duba Zab. 27:14; M. Wa. 1:14; Joel 2:1; Hab. 1:​2, 3; Rom. 8:22.)