‘KU RERA WAKA DA MURNA’ GA JEHOBAH

Mata Masu Aminci (Waka ta 137)

Hausa
Mata Masu Aminci (Waka ta 137)
/assets/ct/fa815d8e9f/images/syn_placeholder_sqr.png
sjj waƙa ta 137

WAƘA TA 137

Mata Masu Aminci

Mata Masu Aminci

(Romawa 16:2)

  1. 1. Saratu, Esther, Maryam, Ruth da sauran,

    Dukansu na da aminci fa sosai.

    Suna ƙaunar Jehobah Maɗaukaki.

    Sun kasance da aminci har ƙarshe.

    Ba a ambata sunan wasu ba

    A Kalmar Jehobah, su amintattu ne.

  2. 2. Suna da ƙauna, kirki da alheri,

    Har da bangaskiya da gaba gaɗi.

    Sun yi hidima da dukan zuciya.

    Sun kafa mana misalai masu kyau.

    A yau muna da ’yan’uwa mata

    Da ke nuna irin waɗannan halayen.

  3. 3. ʼYan’uwa mata, yara da gwauraye,

    Duk kuna hidima da ƙwazo sosai.

    Kuna ladabi da kuma biyayya.

    Allah na ƙaunar ku, kar ku ji tsoro.

    ’Yan’uwa mata bari Jehobah,

    Ya albarkace ku da rai har abada.