Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 136

Jehobah Zai Ba Ka “Cikakkiyar Lada”

Ka Zabi Sauti
Jehobah Zai Ba Ka “Cikakkiyar Lada”
DUBA

(Ruth 2:12)

 1. 1. Jehobah ya san da dukan bayinsa

  Masu yi masa biyayya.

  Ya san da sadaukarwar da suka yi

  Don su iya bauta masa.

  In ka bar iyalinka ko abokai,

  Jehobah zai kula da kai.

  Zai ba ka iyali a ƙungiyarsa

  Da kuma rai har abada.

  (AMSHI)

  Bari Allah ya albarka ce ka,

  Don abubuwan da ka yi masa.

  Ka dogara gare shi sosai.

  Jehobah Allahnmu, mai aminci ne.

 2. 2. A wasu lokuta mukan ji kamar

  Wahalarmu ta yi yawa,

  Kuma mu ga kamar ba za mu iya

  Jimre matsalolinmu ba.

  Allah mai ƙauna ba zai yashe mu ba,

  Zai amsa addu’o’inmu.

  Zai yi mana tanadin ruhunsa fa,

  Da kuma abokan kirki.

  (AMSHI)

  Bari Allah ya albarka ce ka,

  Don abubuwan da ka yi masa.

  Ka dogara gare shi sosai.

  Jehobah Allahnmu, mai aminci ne.

(Ka kuma duba Alƙa. 11:​38-40; Isha. 41:10.)