Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 132

Yanzu Mun Zama Daya

Ka Zabi Sauti
Yanzu Mun Zama Daya
DUBA

(Farawa 2:​23, 24)

 1. 1. A ƙarshe ga kamanina,

  Da jikina, ina godiya.

  Allah ya ba ni mai so na

  Da mataimakiya.

  Yau mun zama iyali fa,

  Za mu riƙa samun albarka.

  Za mu bauta wa Jehobah

  Don shi ne Allahnmu.

  Kalmarsa na taimaka mana,

  Kalmar tana sa

  Mu riƙa ƙaunar juna.

  Wa’adi ne, za mu cika,

  Hakan zai sa mu riƙa murna.

  Idan mun daraja Allah

  Za mu so junanmu sosai.

(Ka kuma duba Far. 29:18; M. Wa. 4:​9, 10; 1 Kor. 13:8.)