Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 130

Mu Rika Gafartawa

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Gafartawa
DUBA

(Zabura 86:5)

 1. 1. Ubanmu mai ƙauna

  Ya aiko da Yesu fa,

  Domin ya yafe zunubi,

  Ya cire mutuwa ma.

  Idan mun yi tuban gaske,

  Zai yafe zunubanmu.

  Allah zai gafarta mana

  Don fansar Yesu Kristi.

 2. 2. Allahnmu Jehobah

  Zai nuna mana jinƙai

  In mun koyi halayensa

  Na yafe wa mutane.

  Nuna tausayi ga kowa

  Da kuma yin haƙuri,

  Mu riƙa girmama juna,

  Mu ƙaunaci junanmu.

 3. 3. Ya dace dukanmu

  Mu riƙa nuna jinƙai.

  Domin kar mu riƙe juna

  A cikin zuciyarmu.

  In mun yi koyi da Allah

  Wanda shi mai ƙauna ne,

  Za mu riƙa nuna jinƙai

  Kamar Mahaliccinmu.

(Ka kuma duba Mat. 6:12; Afis. 4:32; Kol. 3:13.)