WAƘA TA 13
Mu Rika Bin Misalin Yesu
Ka Zabi Sauti
(1 Bitrus 2:21)
1. Jehobah mai ƙauna,
Ya albarkace mu,
Ya aiko Yesu domin ya cece mu.
Ɗansa Yesu Kristi,
Ya zo duniyar nan,
Don ya ɗaukaka Jehobah Allah.
2. Kalmar Jehobah ce,
Ta taimaki Yesu.
Ya zama mai hikima da basira.
Ɗan Allah ya nuna,
Shi bawan kirki ne,
Yana jin daɗin yin nufin Allah.
3. Mu bi misalin da
Ɗan Allah ya kafa
Don ayyukanmu su yabi Jehobah.
Mu riƙa bin gurbin
Da Yesu ya kafa
Domin mu more rai har abada.
(Ka kuma duba Yoh. 8:29; Afis. 5:2; Filib. 2:5-7.)