Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 129

Za Mu Rika Jimrewa

Ka Zabi Sauti
Za Mu Rika Jimrewa
DUBA

(Matta 24:13)

 1. 1. Me zai taimaka

  Mu jimre da matsaloli?

  Yesu ya jimre,

  Ya kafa mana misali.

  Jehobah, Allah ne

  Ya taimaka masa.

  (AMSHI)

  Sai mu riƙa jimrewa,

  Mu riƙe aminci.

  Jehobah na ƙaunar mu,

  Za mu riƙa jimrewa har ƙarshe.

 2. 2. Duniyar Shaiɗan

  Tana baƙanta zucinmu,

  Amma nan gaba

  Za mu ji daɗin aljanna.

  Zama a cikinta

  Ne muke ɗokin yi.

  (AMSHI)

  Sai mu riƙa jimrewa,

  Mu riƙe aminci.

  Jehobah na ƙaunar mu,

  Za mu riƙa jimrewa har ƙarshe.

 3.  3. Shakka ko tsoro

  Ba zai sa mu bar Allah ba.

  Za mu ci gaba

  Har sai ranar Allah ta zo.

  Mu riƙa jimrewa

  Domin ƙarshe ya zo.

  (AMSHI)

  Sai mu riƙa jimrewa,

  Mu riƙe aminci.

  Jehobah na ƙaunar mu,

  Za mu riƙa jimrewa har ƙarshe.

(Ka kuma duba A. M. 20:​19, 20; Yaƙ. 1:12; 1 Bit. 4:​12-14.)