Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 122

Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!

Ka Zabi Sauti
Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!
DUBA

(1 Korintiyawa 15:58)

 1. 1. Mutane suna wahala sosai,

  Suna tsoron abin da zai faru.

  Mu yi gaba gaɗi, babu tsoro,

  Mu bauta wa Jehobah.

  (AMSHI)

  Mu riƙa dagewa fa,

  Mu ƙi halin duniya.

  Mu riƙe aminci

  Don mu sami ceto.

 2. 2. Shaiɗan na jarraba mu koyaushe,

  Amma ba za mu shiga tarkon ba.

  In muna yin ayyukan nagarta,

  Za mu yi ƙarfin hali.

  (AMSHI)

  Mu riƙa dagewa fa,

  Mu ƙi halin duniya.

  Mu riƙe aminci

  Don mu sami ceto.

 3. 3. Mu riƙa bauta wa Maɗaukaki.

  Mu riƙa yin wa’azi koyaushe.

  Mu yi shi ban da tsoron mutane,

  Mulkin Allah ya kusa.

  (AMSHI)

  Mu riƙa dagewa fa,

  Mu ƙi halin duniya.

  Mu riƙe aminci

  Don mu sami ceto.

(Ka kuma duba Luk. 21:9; 1 Bit. 4:7.)