Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 115

Mu Rika Godiya Don Hakurin Allah

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Godiya Don Hakurin Allah

(2 Bitrus 3:15)

 1. 1. Allah Jehobah, Maɗaukaki,

  Kana son adalci sosai.

  Duniya tana nan cike

  Da mugaye, azzalumai.

  Ka kusan hallaka dukansu,

  Kai Allah ne mai yin adalci.

  (AMSHI)

  Mun ƙosa ganin ranar nan,

  Muna yabon ka, Ya Allahnmu.

 2. 2. Kwana dubu wurin ’yan Adam,

  Na kamar ɗaya wurinka.

  Ranarka ta kusa sosai,

  Za ta zo ran da kake so.

  Allah Jehobah mun san cewa

  Kana son mugaye su canja.

  (AMSHI)

  Mun ƙosa ganin ranar nan,

  Muna yabon ka, Ya Allahnmu.

(Ka kuma duba Neh. 9:30; Luk. 15:7; 2 Bit. 3:​8, 9.)