Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 112

Jehobah Allah Ne Na Salama

Jehobah Allah Ne Na Salama

(Filibiyawa 4:9)

  1. 1. Jehobah, Allahnmu,

    Allah na salama ne.

    Muna so mu kasance da

    Halayen da kake so.

    Kai ka ba mu gata

    Mu zama aminanka,

    Domin mun ba da gaskiya

    Ga ƙaunataccen Ɗanka.

  2. 2. Kana amfani da

    Ruhunka da Kalmarka

    Don ka kāre mutanenka

    A cikin duniyar nan.

    Kafin lokacin da

    Za a daina yin yaƙi.

    Bari ruhunka mai tsarki

    Ya sa mu yi salama.

  3. 3. Kana da al’umma

    A sama da duniya.

    Ka shirya mu da ruhunka

    Don mu shaida Mulkinka.

    Mulkin da ka shirya

    Zai share duk wahala.

    Masu tawali’u kuma

    Za su more salama.

(Ka kuma duba Zab. 4:8; Filib. 4:​6, 7; 1 Tas. 5:23.)