Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 110

‘Farin Cikin’ da Jehobah Yake Bayarwa

Ka Zabi Sauti
‘Farin Cikin’ da Jehobah Yake Bayarwa
DUBA

(Nehemiya 8:10)

 1. 1. Nan ba da daɗewa ba Mulkin Allah,

  Zai cire dukan mugaye.

  Mu gargaɗe su fa, mu yi bishara

  Don su rayu har abada!

  (AMSHI)

  Jehobah Allah ya ba mu ’yanci,

  Mu tashi, mu rera yabo.

  Mu rera don aljanna ya yi kusa,

  Dukanmu mu yabi Allahnmu.

  Jehobah Allah ya ba mu ’yanci,

  Mu ɗaukaka girmansa fa.

  Mu girmama Allahn sama mai ƙauna

  Domin mu riƙa murna sosai.

 2. 2. Mu amince, mu bi Allah Jehobah

  Don shi mai iko ne sosai.

  Mu Shaidunsa mu ɗaga muryoyinmu,

  Mu rera waƙa ta yabo!

  (AMSHI)

  Jehobah Allah ya ba mu ’yanci,

  Mu tashi, mu rera yabo.

  Mu rera don aljanna ya yi kusa,

  Dukanmu mu yabi Allahnmu.

  Jehobah Allah ya ba mu ’yanci,

  Mu ɗaukaka girmansa fa.

  Mu girmama Allahn sama mai ƙauna

  Domin mu riƙa murna sosai.

(Ka kuma duba 1 Laba. 16:27; Zab. 112:4; Luk. 21:28; Yoh. 8:32.)