Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 11

Halittun Allah Suna Yabon Sa

Ka Zabi Sauti
Halittun Allah Suna Yabon Sa
DUBA

(Zabura 19)

 1. 1. Muna ganin ikonka, Ya Allah,

  Halittunka na yabon ka sosai.

  Muna ganin hakan a ko’ina,

  Suna nuna mana hikimarka.

  Muna ganin hakan a ko’ina,

  Suna nuna mana hikimarka.

 2. 2. Jin tsoron ka hikima ce babba,

  Yana sa mu riƙa yin biyayya.

  Dokokinka suna amfanar mu,

  Suna da kyau, sun fi zinariya.

  Dokokinka suna amfanar mu,

  Suna da kyau, sun fi zinariya.

 3. 3. Za mu yi rayuwa har abada,

  In mun san ka da kuma Kalmarka.

  Babu wanda zai sami albarka,

  Kamar duk mai tsarkake sunanka.

  Babu wanda zai sami albarka,

  Kamar duk mai tsarkake sunanka.

(Ka kuma duba Zab. 12:6; 89:7; 144:3; Rom. 1:20.)