Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 109

Mu Kasance da Kauna ta Gaske

Ka Zabi Sauti
Mu Kasance da Kauna ta Gaske
DUBA

(1 Bitrus 1:22)

 1. 1. Allah zai yi murna da mu

  In muna yin ƙauna sosai.

  Ƙauna na da muhimmanci,

  Halin Jehobah ne.

  In muna ƙauna da gaske

  Abokantaka zai yi kyau,

  Za mu mutunta mutane

  In muna da ƙauna.

  Zai dace mu taimaka

  In ’yan’uwa na da bukata,

  Domin hakan zai nuna

  Mun san yadda suke ji.

  Yesu ya nuna mana duk

  Irin ƙauna ta Allahnmu,

  Don mu riƙa nuna ƙauna,

  Ƙauna ga duk mutane.

  Mu zama masu ƙauna.

(Ka kuma duba 1 Bit. 2:17; 3:8; 4:8; 1 Yoh. 3:11.)