Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 106

Mu Rika Nuna Kauna

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Nuna Kauna
DUBA

(1 Korintiyawa 13:​1-8)

 1. 1. Jehobah muna miƙa roƙo

  Domin mu kwaikwayi halinka.

  Ƙauna ce ta fi muhimmanci,

  Ƙauna ce muke so mu nuna.

  Ko da muna da baiwa sosai,

  Rashin ƙauna aikin banza ne.

  Uba muna son taimakonka,

  Ka sa mu zama masu ƙauna.

 2. 2. Ƙauna na sa mu yi alheri

  Da kuma marabtar mutane.

  Ƙauna tana sa mu jimrewa

  Da yafe zunuban mutane.

  Ƙauna ba ta riƙe laifofi,

  Na sa mu jimre wahaloli.

  A fannonin rayuwarmu fa,

  Muna bukatar ƙauna sosai.

(Ka kuma duba Yoh. 21:17; 1 Kor. 13:13; Gal. 6:2.)