Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 104

Allah Yana Ba Mu Ruhunsa Mai Tsarki

Ka Zabi Sauti
Allah Yana Ba Mu Ruhunsa Mai Tsarki

(Luka 11:13)

 1. 1. Allah Jehobah, kai mai jinƙai ne,

  Kana ƙaunar mu halittunka.

  Ka taimaka ka tallafa mana,

  Ka ƙarfafa mu muna roƙanka.

 2. 2. Allahnmu muna yin kurakurai,

  Mukan bijire daga hanya.

  Uba Jehobah, muna roƙan ka,

  Ka ja-gorance mu da ruhunka.

 3. 3. Idan mun faɗi ko sanyi gwiwa,

  Ruhun Allah zai taimake mu,

  Zai sa mu tashi kamar gaggafa.

  Ka ba mu ruhunka ya Ubanmu.

(Ka kuma duba Zab. 51:11; Yoh. 14:26; A. M. 9:31.)