Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 103

Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya

Ka Zabi Sauti
Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya

(Afisawa 4:8)

 1. 1. Allah ya ba mu makiyaya

  Don su kula da mu.

  Suna kafa misali mai kyau

  Da za mu riƙa bi.

  (AMSHI)

  Allah ya yi mana tanadi,

  Tanadin makiyaya.

  Suna ƙauna da kula da mu,

  Mu ƙaunace su sosai.

 2. 2. Makiyayan nan na da ƙauna

  Da kuma sauƙin kai.

  In mun fuskanci matsaloli

  Suna kula da mu.

  (AMSHI)

  Allah ya yi mana tanadi,

  Tanadin makiyaya.

  Suna ƙauna da kula da mu,

  Mu ƙaunace su sosai.

 3. 3. Suna yi mana ja-goranci

  Don kar mu bijire.

  Don mu ci gaba da bauta wa

  Allahnmu koyaushe.

  (AMSHI)

  Allah ya yi mana tanadi,

  Tanadin makiyaya.

  Suna ƙauna da kula da mu,

  Mu ƙaunace su sosai.

(Ka kuma duba Isha. 32:​1, 2; Irm. 3:15; Yoh. 21:​15-17; A. M. 20:28.)