Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 1

Babu Wani Kamar Jehobah

Ka Zabi Sauti
Babu Wani Kamar Jehobah
DUBA

(Ru’ya ta Yohanna 4:11)

 1. 1. Jehobah Allah, Mai iko duka,

  Mahaliccin rai, rana da taurari.

  Sararin sama da duniyar nan,

  Za su wanzu har abada fa.

 2. 2. Sarautar Allah, babu kamarta.

  Kai ka koya mana duk dokokinka.

  Karanta Kalmarka na sa mu yi

  Hikima da hankali sosai.

 3. 3. Ƙauna kyauta ce mai muhimmanci,

  Mun gode Allah domin wannan kyauta.

  Halayenka har da sunanka ma,

  Za mu yi shelar su da ƙwazo.

(Ka kuma duba Zab. 36:9; 145:​6-13; M. Wa. 3:14; Yaƙ. 1:17.)