Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Tsarin Karanta Littafi Mai Tsarki

Tsarin Karanta Littafi Mai Tsarki

Littafi Mai Tsarki yana dauke da abubuwan da za su taimaka mana a rayuwa. Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki da yin bimbini da kuma amfani da abin da ka koya, “za ka yi nasara.” (Yoshuwa 1:8; Zabura 1:1-3) Ban da haka, za ka san Allah da Ɗansa Yesu, kuma hakan zai sa ka sami ceto.—Yohanna 17:3.

Wane tsari ne za ka bi don karanta Littafi Mai Tsarki? Kai za ka zaɓa. Wannan tsarin karanta Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka rika karanta Littafi Mai Tsarki bisa yadda aka tsara su ko kuma ka karanta bisa jigo. Alal misali, kana iya zaɓan littafin da ya ba da tarihin yadda Allah ya yi mu’amala da Isra’ila a dā. Kana iya karanta wasu wurare a Littafi Mai Tsarki don ka ga yadda aka kafa ikilisiyar Kiristoci a karni na farko da kuma yadda ta sami ci gaba. Idan kana karanta jerin surori a kowace rana, za ka iya karance Littafi Mai Tsarki gabaki daya a cikin shekara daya.

Idan kana neman tsarin karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana ko na shekara daya ko kuma domin ba ka taba karance Littafi Mai Tsarki, wannan tsarin karanta Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka. Don ka soma karanta Littafi Mai Tsarki, ka saukar da wannan tsarin karanta Littafi Mai Tsarki.