Ka Zama Abokin Jehobah​​—Ayyuka

Za ku ji dadin yin ayyukan nan da yaranku.

Ka Taimaki Kaleb Ya Tsabtace Wuri!

Ka sauko da shi ko kuma ka gurza aikin kuma ka taimake shi ya nemi kayan wasa guda 5 da ya kamata ya tattara waje ɗaya.

Wane Littafi ne Kaleb Yake Karantawa?

Ka kalli bidiyon nan, “Sata Bai da Kyau.” Sai ka gurza wannan aikin kuma ka yi masa kala.

Ka Shirya Jakar Fita Wa’azi!

Me ya kamata ka fita wa’azi da su? Wannan aikin zai taimaka maki ki shirya jakarki.

Ka Yi Addu’a Kowane Lokaci: Waƙa da Kalmomi

Ka sauko da fallen waƙa da kalmomin waƙa da ake iya gurzawa. Yara za su so wannan waƙa mai-sauƙin-koyawa!

Lokaci Ya Yi na Shiri!

Za ku iya zaban tufa da Kaleb da Safiya za su sanya zuwa wa’azi?

Jehobah Ya Halicci Dabbobi!

Ka sauko da wannan shafin kuma ka kalli bidiyon nan “Jehobah . . . Ne Ya Halicci Kome” don ka san dabbobin da aka fara halitta.

Ka Haddace Yohanna 3:16

Ka koya abin da Yohanna 3:16 ya ce, sai ka yi amfani da shi sa’ad da ka je wa’azi.

Ka Zana Motar Kaleb

Gurza, yanke, kuma ka hada motar wasa na Kaleb.

Ka Haddace Zabura 83:18

Me ya sa Jehobah ne ‘Madaukaki bisa dukan duniya’?

Me Ya Kamata Ka Yi?

Ka kali bidiyon nan “Ku Rika Yafe Wa Juna” sai ka gurza ayyukan kuma ka sa wa hoton da ya dace kala.

Ka haddace Zabura 133:1

Sa’ad da muka hadu tare, Jehobah yana albarkace mu da salama da kuma hadin kai.

Alamar Shafi da Za a Adana!

Ka sa shi cikin shafi littattafanka da ka ke karantawa!

Ka Nuna Bambancinsu: Aiki na Taron Yanki

Ku gwada hotunan. Me zai taimaka maka ka saurara a taro?

Ka Gwada: Rayuwa a Yau da Nan Gaba

Wadanne alkawuran Littafi Mai Tsarki ne za su cika a Aljanna?

Me Ya Sa Ya Dace Ka Rika Saurara a Taro?

Ka nuna hoton da ya yi daidai da abin da ke hoton. Ta yaya za ka zama kamar Yesu wajen koyo game da Allah?

Ka Haddace Littattafan Baibul (Sashe na 2)

Ka yi amfani da wannan takardar wajen haddace sauran littattafan Nassosin Ibrananci daga littafin Irmiya zuwa Malakai.

Ta Yaya Za Ka Zama Mai Hakuri?

Ka yi tunanin wasu abubuwan da ya kamata ka yi hakuri a kai?

Tsarin Jehobah Game da Aure

Labarin wadanne ma’aurata ne yake cikin Littafi Mai Tsarki?

Jehobah Ya Halicci Abubuwa Masu Ban Mamaki!

Abubuwa nawa da Jehobah ya halitta ne ka gani a wannan hoton?

Yin Wa’azi ga Dukan Mutane

Su waye ne ya kamata mu yi wa wa’azi game da Mulkin Allah?

Ka yi Abokai na Kwarai!

Me ya sa ya dace ka yi abokantaka da tsofaffi?

Taimakawa a Inda Akwai Bukata

Har yanzu ana bukatar wadanda za su ba da kansu don su taimaka wa mutane su san Jehobah. Mene ne za ka iya yi?

Fansar Yesu

Me ya sa muke bukatar fansar da Yesu ya ba da?

Ka Bari Jehobah Ya Horar da Kai

Allah zai iya horar da kai ka yi karfi kuma ya karfafa ka.

Rayuwar Yesu

Karanta Nassosin da aka ambata kuma ka maka nassin da ya yi daidai da zanen.

Ka Rike Gaskiya

Wadanne abubuwa ne za ka iya yi don ka rike gaskiya?

Ku Rika Nuna Kauna

Ta yaya za mu yi koyi da Yesu a yadda muke kaunar mutane?

Ka Ga Kanka a Aljanna

Wane abu ne ka fi dokin gani a Aljanna?

Ka Jimre Idan An Yi Maka Rashin Adalci

Me ya kamata mu yi sa’ad da aka mana rashin adalci?

Yin Tafiya Tare da Abokan Jehobah

Ka yi amfani da wannan aikin don ka soma naka nazarin Littafi Mai Tsarki.

Ka Zama Mai Tawali’u

Ka koyi nuna tawali’u daga wajen mutane dabam-dabam a Littafi Mai Tsarki.

Dalilan da Suke Sa Mu Murna

Wace dabba ce za ka so ka yi wasa da ita a sabuwar duniya?

Ku Jimre Idan Aka Yi Muku Rasuwa

Mene ne zai taimaka mana mu rika farin ciki sa’ad da wani ya rasu?

Mu Yi Wa’azi Gida-Gida

Wanne ne daga cikinsu za ka so ka yi amfani da shi a wa’azi?

Ka Rika Addu’a a Madadin Wasu

Su waye ne za ka iya yin addu’a a madadinsu?

Ka Daraja Gidan Jehobah

Ka yi iya kokarinka don ka tsabtace gidan Allah

Abubuwa na Musamman

Jehobah yana so mu kafa makasudai a hidimarsa. Wadanne makasudai kake da su?

Mu Bauta wa Jehobah da Kuruciyarmu

Ta yaya za mu rika nuna godiya?

An Halicce Mu a Hanya Mai Ban Al’ajabi

Wadanne abubuwa masa ban al’ajabi ne za ka iya yi?

Ka Sa Jehobah Farin Ciki

Za mu iya faranta ran Allah ta wajen yi masa biyayya da kuma tsai da shawarwari da suka dace.

Ka Nuna Halin Kirki a Wa’azi

Ta yaya za ka rika nuna hali mai kyau a wa’azi?

Ku Rika Yafe wa Juna

Mene ne zai taimaka maka ka rika yafe wa mutane?

“Na Yarda”

Yesu yana son taimaka wa mutane. Ta yaya za ka iya yin hakan?

Muna Son Yin Ibada ta Iyali

Ta yaya iyalinka za su sa yin ibada ta iyali ya yi dadi?

Ku Rika Taimaka wa Mutane

Kamar yadda Yesu ya taimaki wani kuturu, za ka iya taimaka wa ’yan’uwanmu da suke bukatar taimako.

Ka Yi Amfani da Lokaci Yadda ya Dace

Ta yaya littafin Afisawa 5:​15, 16 zai taimaka maka ka yi amfani da lokaci yadda ya dace?

Ayyukan Allah Suna da Ban Al’ajabi

Dabbobi nawa ne za ka iya ambata sunansu?

Za Mu Rika Jimrewa

Yin tunani a kan abubuwa masu kyau da za su faru a nan gaba zai taimaka mana mu jimre matsaloli.

Rut Abokiyar Kirki Ce

Za ka iya koyi da Rut ta wurin zama abokin kirki.

Dauda Ya Nuna wa Matasa Misali Mai Kyau

Dauda ya kulla abota na kud da kud da Jehobah saꞌad da yake matashi, kuma hakan ya taimaka masa a rayuwa.

Jehobah Yana Amsa Adduꞌa Kuwa?

A wasu lokuta Jehobah yana amsa adduꞌoꞌinmu a hanyoyin da ba mu yi tsammani ba.

Mu Rika Adduꞌa ga Jehobah Koyaushe

Kulla abota da Jehobah yana daukan lokaci, amma yin hakan yana amfanar mu!

Dana

Yara suna da daraja ga Jehobah.

Kada Ka Gaji

Kaleb da Safiya sun bi misalin da Yesu ya kafa na rashin gajiya da wuri, kai ma za ka iya.