Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wannan dutsen yana ɗauke da sunan nan Tattannu a gefensa

Wani Karin Tabbaci

Wani Karin Tabbaci

Shin akwai wasu hujjojin da ‘yan tarihi suka samo da suka ƙara tabbatar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki? A shekara ta 2014, an amsa wata tambaya a mujallar nan Biblical Archaeology Review cewa: “Shin tarihin mutane nawa ne da aka ambata a Nassosin Ibrananci da ‘yan tone-tone suka amince da su?” Amsar ita ce: “Aƙalla guda 50!” Amma ba a ambata sunan Tattenai a mujallar ba. Wane ne shi? Bari mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da shi.

A dā, Urushalima tana ƙarƙashin Daular Fasiya. Birnin yana ta yammancin Yufiretis kuma mutanen Fasiya suna kiran shi Across-the-River (Hayin Kogi). Bayan Fasiyawan sun ci ‘yan Babila a yaƙi, sai suka ce Yahudawan da suke zaman bauta a Babila su koma ƙasarsu don su sake gina haikalin Jehobah a Urushalima. (Ezra 1:1-4) Amma sai maƙiyan Yahudawan suka yi ƙoƙarin hana su aikin kuma suka zarge su da cewa sun yi wa Fasiyawan tawaye. (Ezra 4:4-16) A lokacin sarautar Darius na Ɗaya (daga shekara ta 522-486 kafin haihuwar Yesu), an ce wani ma’aikacin fādar Fasiya mai suna Tattenai ya yi bincike a kan batun. Littafi Mai Tsarki ya kira shi “mai-mulkin Ƙetaren Kogi.”Ezra 5:3-7.

An samo wasu duwatsu da ke ɗauke da sunan Tattenai kuma wataƙila iyalinsa ne suka adana duwatsun. Ɗaya daga cikin dutsen ya ambaci bawan “Tattannu, mai-mulkin Ƙetaren Kogi,” wanda ya yi shaidar wani aiki da aka yi. A shekara ta 502, sa’ad da Darius na Ɗaya ya yi shekara 20 da sarauta ne aka ba Tattannu mulki. Wannan shi ne Tattenai da littafin Ezra ya yi magana a kansa.

Mene ne matsayin wannan mutumin? A shekara ta 535 kafin haihuwar Yesu, Sairus Mai Girma ya canja yadda yake sarautarsa kuma ya raba daularsa zuwa lardi-lardi. Ana kiran ɗaya daga cikin lardin Babila da kuma Hayin Kogi. Bayan wani lokaci, sai aka raba lardin zuwa kashi biyu, kuma aka kira ɗaya Hayin Kogi. Wannan lardin ya ƙunshi Coele-Syria da Finikiya da Samariya da kuma Yahuda. Amma wataƙila daga Dimaska ne ake mulkansu. Tattenai ne ya mulki waɗannan yankunan daga shekara ta 520 zuwa 502 kafin haihuwar Yesu.

Bayan Tattenai ya je Urushalima kuma ya yi bincike a kan zargin da aka yi wa Yahudawa, sai ya gaya wa Darius cewa Sairus ne ya ba Yahudawan umurnin sake gina haikalin Jehobah. Kuma littattafan da aka adana a fādar sun nuna cewa hakan gaskiya ne. (Ezra 5:6, 7, 11-13; 6:1-3) Don haka, sai aka ce wa Tattenai ya ƙyale Yahudawan kuma abin da ya yi ke nan.Ezra 6:6, 7, 13.

Ko da yake tarihin “Tattenai, mai-mulkin Ƙetaren Kogi” ba wani abin a zo a gani ba ne. Amma duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya kira shi da ainihin laƙabin da ake kiransa da shi. Hakan ya ƙara ba mu tabbacin cewa abubuwan da ‘yan tarihi suke ganowa suna sa mu ƙara gaskata da Littafi Mai Tsarki.