Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MAHAYA HUƊU—YADDA SUKE SHAFAN RAYUWARKA

Su Wane ne Mahaya Hudun?

Su Wane ne Mahaya Hudun?

Ko da yake ana iya ganin waɗannan mahaya huɗu a matsayin abin ban tsoro ko kuma abin da ba za a iya fahimta ba amma hakan ba gaskiya ba ne. Domin Littafi Mai Tsarki da kuma abubuwan da suke faruwa a yau sun taimaka mana mu san ma’anar waɗannan mahayan. Duk da cewa fitar su tana wakiltar bala’i ga duniya, kai da iyalinka za ku iya amfana daga hakan. Amma ta yaya? Da farko, bari mu san abin da kowannensu yake wakilta.

MAHAYIN FARIN DOKI

Wannan wahayin ya fara da cewa: “Na duba kuma, ga farin doki; wanda yake zaune a kansa kuma yana da baka; kuma aka ba shi rawani: a kan nasara ya fita, garin yin nasara kuma.”Ru’ya ta Yohanna 6:2.

Wane ne mahayin wannan farin dokin? Za mu iya samu amsar wannan tambayar a cikin littafin Ru’ya ta Yohanna. Littafin ya kira mahayin nan “Kalmar Allah.” (Ru’ya ta Yohanna 19:11-13) Yesu Kristi ne ake kira da laƙabin nan Kalma, domin shi kakakin Allah ne. (Yohanna 1:1, 14) Ƙari ga haka, ana kiransa “Sarkin sarakuna, da Ubangijin Iyayengiji,” kuma ana kwatanta shi a matsayin “Amintacce” da kuma “Mai-gaskiya.” (Ru’ya ta Yohanna 19:16) An ba shi iko kuma a matsayinsa na sarki, ba zai yi amfani da wannan ikon a hanyar da ba ta dace ba. Amma da akwai wasu tambayoyi kuma da za mu iya yi.

Wane ne ya ba Yesu wannan ikon? (Ru’ya ta Yohanna 6:2) A wani wahayi, annabi Daniyel ya ga “Wanda Yake Tun Dā,” wato Jehobah * ya ba wa “ɗan mutum,” wato Almasihu “sarauta da ɗaukaka da kuma mulki.” (Daniyel 7:13, 14, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Don haka, Allah Mai iko duka ne ya ba Yesu ikon yin sarauta da kuma yanke hukunci. Littafi Mai Tsarki yana yawan amfani da farin kala don ya kwatanta adalci. Don haka, farin dokin yana wakiltar yaƙi na adalci da Ɗan Allah zai yi.Ru’ya ta Yohanna 3:4; 7:9, 13, 14.

Yaushe ne mahayan suka soma tafiyarsu? Yesu ya soma nasa tafiyar sa’ad da aka naɗa shi sarki. (Ru’ya ta Yohanna 6:2) Yaushe ne aka naɗa Yesu sarki a sama? Ba a naɗa Yesu nan da nan sa’ad da ya koma sama bayan mutuwarsa ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ya ɗan jira. (Ibraniyawa 10:12, 13) Yesu ya gaya wa mabiyansa alamar da za ta nuna cewa ya soma mulki a sama. Ya ce idan ya soma sarauta, yanayin duniya za ta taɓarɓare. Za a yi yaƙe-yaƙe da ƙarancin abinci da kuma munanan cututtuka. (Matta 24:3, 7; Luka 21:10, 11) Jim kaɗan bayan Yaƙin Duniya na Ɗaya da aka yi a shekara ta 1914, yanayin duniya ya nuna cewa Yesu ya soma sarauta kuma mun shiga lokacin da Littafi Mai Tsarki ya kira “kwanaki na ƙarshe.”2 Timotawus 3:1-5.

Amma me ya sa abubuwa sai ƙara muni suke yi tun da Yesu ya soma sarauta a 1914? Domin a lokacin, Yesu ya soma sarauta ne a sama ba a duniya ba. An soma yaƙi a sama, sai sabon Sarkin da aka naɗa, wato Yesu wanda ake ce da shi Mika’ilu ya jefar da Shaiɗan da kuma aljanunsa zuwa ƙasa. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-9, 12) Tun daga lokacin, Shaiɗan yana fushi sosai domin ya san cewa kwanansa ta kusan ƙarewa. Hakika, nan ba da daɗewa ba, Allah zai halaka Shaiɗan. (Matta 6:10) Yanzu, bari mu ga yadda sauran mahaya ukun suka ƙara ba mu tabbacin cewa muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe.” Amma waɗannan mahayan ba sa wakiltar mutum, kamar mahayi na farko. Maimakon haka, suna wakiltar abubuwan da ke faruwa a duniya.

MAHAYIN JAN DOKI

“Sai wani jan doki ya fito, aka kuma ba mahayinsa izni ya ɗauke salama daga duniya, don mutane su kashe juna, aka kuma ba shi babban takobi.”Ru’ya ta Yohanna 6:4, Littafi Mai Tsarki.

Mahayin wannan dokin yana wakiltar yaƙi. Ka lura cewa wannan mahayin ya ɗauke salama daga dukan duniya ba wasu ƙasashe kawai ba. A shekara ta 1914 ne aka yi yaƙin da ta shafi duniya gabaki ɗaya. Bayan wannan, sai aka sake yin wani yaƙin da ta fi na farko muni. Wasu bincike sun nuna cewa mutane fiye da miliyan 100 sun rasa rayukansu sanadiyyar yaƙe-yaƙen da aka soma yi tun 1914! Ban da haka, mutane da yawa sun ji rauni sosai a sakamakon hakan.

Amma ta yaya yaƙi ya nuna irin yanayin da muke ciki a yau? Wannan lokaci na farko ne da ‘yan Adam suka ƙirƙiro makaman da za su iya halaka mutane gabaki ɗaya. Ko Majalisar Ɗinkin Duniya da suke da’awar cewa za su kawo salama a duniya, ba su iya dakatar da wannan mahayin ba.

MAHAYIN BAƘIN DOKI

“Da na duba, ga baƙin doki, mahayinsa kuwa da mizani a hannunsa. Sai na ji kamar wata murya a tsakiyar rayayyun halittan nan huɗu tana cewa, ‘Mudun alkama dinari guda, mudu uku na sha’ir dinari guda, sai dai kada ka ɓāta māi da kuma ruwan inabi!’”Ru’ya ta Yohanna 6:5, 6, LMT.

Wannan mahayin yana wakiltar ƙarancin abinci. Wahayin ya nuna cewa farashin abinci zai hau sosai da har kofi huɗu da rabi na alkama zai kai dinari ɗaya. A ƙarni na farko, dinari ɗaya shi ne albashin da lebura yake karɓa a rana! (Matta 20:2) A lokacin, alkama ta fi sha’ir daraja domin mutum zai iya amfani da dinari ɗaya ya sayi kofi goma sha huɗu na sha’ir. Amma shin hakan zai iya ciyar da babban iyali ne? Saboda haka, sai aka gargaɗi mutane da su lallaɓa da abincinsu na yau da kullum har da mai da kuma ruwan anab.

Muna da tabbacin da ya nuna mana cewa wannan mahayin baƙin dokin ya soma nasa tafiyar tun daga 1914. A ƙarni na 20, mutane wajen miliyan 70 sun mutum a sakamakon rashin abinci. Wani bincike ya ce: “A shekara ta 2012-2014, aƙalla mutane miliyan 805 ba su ci abinci mai gina jiki ba.” Wani kuma ya ce: “A kowace shekara, yunwa tana kashe mutane da yawa fiye da cutar sida da zazzabin cizon sauro da kuma tarin fuka.” Duk da cewa gwamnati tana iya ƙoƙarinta don ta ga cewa mutane sun sami isashen abinci, har yanzu ana fama da ƙarancin abinci.

MAHAYIN KOƊAƊƊEN DOKI

‘Da na duba, sai ga wani doki wanda kalarsa ta koɗe. Sunan mai hawansa kuwa Mutuwa ce, Kabari kuma yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na mazaunan duniya, domin su kashe su ta wurin takobi, da yunwa, da bala’i, da kuma namomin daji.’Ru’ya ta Yohanna 6:8, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.

Mahayi na huɗun yana wakiltar mutuwa wadda cututtuka da dai sauran su suka jawo. Jim kaɗan bayan 1914, miliyoyin mutane sun mutu a sakamakon cutar da ake kira massassara. Wataƙila mutane wajen miliyan 500 sun kamu da cutar, wato mutum ɗaya a cikin 3 da ke rayuwa a lokacin!

Amma cutar massassara ba ta kai cutar zanzana illa ba. Masu bincike sun gano cewa a ƙarni na 20, fiye da mutane miliyan ɗari uku sun mutum don cutar zanzana. Har a yau, cutar sida da tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro sun ɗauke rayukan mutane da yawa duk da ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiya.

Mutane da yawa sun mutum sanadiyyar yaƙi da yunwa da kuma cututtuka. A kabari ne ake binne waɗannan mutanen kuma ba su da mafita.

KOME ZAI GYARU A NAN GABA!

Nan ba da daɗewa ba matsalolinmu za su ƙare. Ka tuna cewa a shekara ta 1914, Yesu “a kan nasara ya fita” kuma ya jefo Shaiɗan duniya. Amma bai kammala aikinsa ba tukuna. (Ru’ya ta Yohanna 6:2; 12:9, 12) Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai yi amfani da yaƙin Armageddon wajen halaka Shaiɗan da magoya bayansa a duniya. (Ru’ya ta Yohanna 20:1-3) Ba kawai yaƙe-yaƙe da yunwa da kuma cututtuka ne Yesu zai cire ba amma zai mai da duniyar nan aljanna. Ta yaya? Ka ga wasu alkawuran da ke cikin Littafin Mai Tsarki.

Maimakon yaƙi, za mu zauna lafiya. Jehobah zai sa “yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya; Ya karya baka, ya daddatse māshi.” (Zabura 46:9) Masu son zaman lafiya za su “faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”Zabura 37:11.

Maimakon ƙarancin abinci, za mu samu abinci da yawa. “Za a yi albarkar hatsi a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu.”Zabura 72:16.

Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai mai da duniyar nan aljanna

Maimakon ciwo da kuma mutuwa, dukanmu za mu sami ƙoshin lafiya da kuma rai na har abada. Allah “zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”Ru’ya ta Yohanna 21:4.

Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nuna mana irin abubuwan da zai yi sa’ad da ya soma sarauta. Ya zauna lafiya da mutane, ya ciyar da dubban mutane ta mu’ujiza, ya warkar da cututtuka kuma har ya tayar da matattu.Matta 12:15; 14:19-21; 26:52; Yohanna 11:43, 44.

Shaidun Jehobah za su yi farin cikin nuna maka a cikin Littafi Mai Tsarki yadda za ka kasance a shirye sa’ad da waɗannan mahayan suka kammala tafiyarsu. Za ka so samun ƙarin bayani?

^ sakin layi na 7 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.