Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MAHAYA HUƊU—YADDA SUKE SHAFAN RAYUWARKA

Yadda Mahaya Hudun Suke Shafan Ka

Yadda Mahaya Hudun Suke Shafan Ka

Sun fito a guje, ƙafafunsu na ƙara sosai! Wahayin waɗannan dawakai masu ƙarfi da kuma mahayansu sanannen wahayi ne a cikin Littafi Mai Tsarki. Doki na farko fari ne kuma mahayinsa sabon sarki mai ɗaukaka ne da aka naɗa. Daga shi, sai doki mai jan kala kuma mahayinsa ya zo ne don ya ɗauke salama daga duniya. Bayan wannan, sai wani baƙin doki wanda mahayinsa na riƙe da sikeli kuma yana yin shela marar daɗi game da ƙarancin abinci. Doki na huɗu koɗaɗɗe ne wanda yake wakiltar munanan cututtuka kuma Mutuwa ce da kanta mahayinsa. Biye da dokin kuma Kabari ne, wanda yake kwashe rayukan dubban mutane!Ru’ya ta Yohanna 6:1-8.

“Na ji tsoro sosai a lokacin da na fara karanta game da waɗannan mahayan. Na ji kamar ranar hukunci ta kusa. Kuma ba zan tsira ba tun da ba na yin abu mai kyau.”—In ji Crystal.

“Wahayin mahaya huɗun nan ya burge ni sosai. Da na fahimci ma’anar wahayin, sai ya kasance da ma’ana sosai a gare ni.”—In ji Ed.

Ra’ayinka game da waɗannan mahayan ya zo ɗaya da na Crystal? Ko kuma ra’ayinka ɗaya ne da na Ed? Ko da yaya kake ji, wannan wahayin ya kasance ɗaya daga cikin sanannun wahayoyin da ke littafin Ru’ya ta Yohanna. Shin ka san cewa za ka iya amfana daga wannan wahayin? Amma ta yaya? Allah ya yi alkawari cewa za ka yi farin ciki sosai a rayuwa idan kana karanta wannan littafin kuma kana aikata abubuwan da aka rubuta a cikinsa.Ru’ya ta Yohanna 1:1-3.

Duk da cewa wasu suna jin tsoron wannan wahayin, amma ba a rubuta shi don ya tsoratar da kai ba. Gaskiyar ita ce, miliyoyin mutane sun gano cewa wannan wahayin ya ƙarfafa bangaskiyarsu kuma ya sa sun kasance da bege cewa za su ji daɗin rayuwa a nan gaba. Kai ma zai iya amfanar ka! Don Allah, ka ci gaba da karatun.