Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ƘA’IDODIN LITTAFI MAI TSARKI DA ZA SU AMFANE MU A YAU

Ka Rika Gafartawa

Ka Rika Gafartawa

ƘA’IDAR LITTAFI MAI TSARKI: “Kuna gafarta ma juna, idan kowane mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku, hakanan kuma sai ku yi.”—Kolosiyawa 3:13.

Mene ne hakan yake nufi? A cikin Littafi Mai Tsarki, an kwatanta zunubi da bashi, gafartawa kuma da yafe bashi. (Matta 18:21-35) Wani bincike ya nuna cewa a cikin Nassosi, kalmar Helenancin nan “gafarta” tana nufin “yafe wa mutum bashi kwatakwata.” Saboda haka, idan muka yafe wa wani bai kamata mu sake tuna da abin da ya yi ba. Gafarta wa mutum da zuciya ɗaya ba ta nufin cewa mun amince da abin da ya yi ko kuma kamar laifin bai ɓata mana rai ba. Maimakon haka, mun yafe wa mutumin ne kawai ko da yake muna da dalilin yin gunaguni.

Yana da amfani a yau kuwa? Muna yin zunubi domin dukanmu ajizai ne. (Romawa 3:23) Saboda haka, hikima ce a gare mu mu riƙa gafartawa don mu ma wata rana za mu bukaci wasu su gafarta mana. Ƙari ga haka, za mu amfana idan muka gafarta wa mutane. Ta yaya?

Idan muka riƙe mutane a zuci kuma muka ƙi gafarta musu, kanmu muke wa lahani. Irin wannan halin da bai dace ba zai iya sa mu baƙin ciki da hana mu sakewa da kuma sa mu shiga wani yanayin mai ban taƙaici. Za mu iya yin ciwo mai tsanani sanaddiyar hakan. Wani rahoto da ke littafin nan Journal of the American College of Cardiology, da Dakta Yoichi Chida da kuma Farfesan Binciken Halin ’Yan Adam Andrew Steptoe suka rubuta ya ce: “Binciken kwanan nan ya nuna cewa yin fushi da gāba yana da haɗari sosai kuma hakan zai iya haifar da ciwon zuciya.”

Akasin haka, ka yi la’akari da amfanin gafartawa. Idan muka gafarta wa mutane, za mu kasance da haɗin kai da salama kuma hakan zai ƙarfafa abotarmu da mutane. Mafi muhimmanci ma, za mu nuna cewa muna yin koyi da Allah wanda yake gafarta wa masu zunubi kuma yake so mu ma mu yi hakan.—Markus 11:25; Afisawa 4:32; 5:1.