Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Juyin 2013 na New World Translation

Juyin 2013 na New World Translation

A SHEKARUN da suka wuce, an kyautata fassarar New World Translation of the Holy Scriptures na Turanci da dama, amma an fi yin gyara a wadda aka fassara a shekara ta 2013. Alal misali, yanzu a Turanci an rage wasu kalmomin da aka yi amfani da su a wannan juyin kuma an kyautata wasu muhimman kalmomin Littafi Mai Tsarki. An canja tsarin wasu surori kuma aka rubuta su kamar yadda ake rubuta waƙa. A wannan talifin, za mu tattauna kaɗan daga cikin wasu canje-canjen da aka yi a cikin New World Translation na 2013.

Waɗanne muhimman kalmomi na Littafi Mai Tsarki ne aka canja? Kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, an canja yadda ake rubuta “Sheol,” da kuma “Hades.” Ƙari ga haka, an gyara wasu kalmomi da dama.

Alal misali, an canja kalmar nan “rataye” zuwa “an kashe shi a kan gungume” ko kuma “an kafa shi a kan gungume” don mutane su fahimci yadda aka kashe Yesu. (Mat. 20:19; 27:31) Wannan kalmar, “tsawon jimrewa” da aka yi amfani da shi a dā zai iya nufin shan wahala na tsawon lokaci. Saboda haka, an yi amfani da “haƙuri” don hakan yana da sauƙin fahimta a yau. (Gal. 5:19-22, New World Translation) An sauya “ƙauna ta alheri” da “aminci.” Hakan ya yi daidai da ma’anar kalmar da aka yi amfani da shi a rubuce-rubucen asali da aka fassara zuwa “bangaskiya” a wasu wurare.—Zab. 36:5; 89:1NW.

 An yi amfani da kalma guda a Turanci wajen fassara wasu kalmomin Ibrananci a dā, amma yanzu an fassara su bisa ga yadda aka yi amfani da su a mahallin. Alal misali, kalmar Ibrananci ʽoh·lamʹ, da aka fassara zuwa “fil azal” a dā yana iya nufin “har abada.” Ka gwada yadda hakan ya shafi ayoyi kamar Zabura 90:2 da kuma Mikah 5:2 a juyin New World Translation na 2013.

Kalmomin Ibrananci da Helenanci da aka fassara zuwa “iri” zai iya nufin irin da ake shukawa da kuma “zuriya.” A dā, an yi amfani da kalmar nan “iri” a juyin New World Translation na Turanci a ayoyi da yawa kuma hakan ya haɗa da Farawa 3:15. Amma yanzu, ba a amfani da kalmar nan “iri” idan ana maganar “zuriya.” Saboda haka, an sauya kalmar nan iri da “zuriya” a Farawa 3:15 da kuma wasu ayoyi da hakan ya shafa. (Far. 22:17, 18; R. Yoh. 12:17, NW) A wasu wurare da aka yi amfani da kalmar, an fassara ta bisa ga mahallin.—Far. 1:11; Zab. 22:30; Isha. 57:3NW.

Me ya sa aka kyautata wasu fassara da aka yi kai tsaye? Apendix A1 na sabon juyin 2013 na New World Translation a Turanci ya bayyana cewa fassarar Littafi Mai Tsarki mai kyau “tana tanadar da ainihin ma’anar kalma ko kuma kalamai idan fassara kai tsaye ba zai sa mutane su fahimci ainihin abin da ake nufi a ayoyin ba.” Idan karin maganar da aka yi amfani da ita ta fitar da ma’anar, ana iya fassarawa kai tsaye. Saboda haka, ana iya fahimtar ainihin ma’anar furucin nan, “bincika zuciya” da ke Ru’ya ta Yohanna 2:23 (NW) idan aka fassara shi kai tsaye a wasu harsuna. A Kubawar Shari’a 32:14, an fassara karin maganar nan, “romo na zangarniyar alkama” zuwa yadda zai yi sauƙin fahimta, wato “alkama mafi kyau.” Ƙari ga haka, wannan furucin “ba a yi wa leɓena kāciya ba” yana da wuyar fahimta, saboda haka, an fassara shi zuwa “ni mai i’ina ne.” (Fit. 6:12, NW.) An sauƙaƙa kalmomin Ibrananci da yawa a Turanci domin ayoyin su kasance da sauƙin fahimta.

Me ya sa aka fassara “’ya’yan Isra’ila” zuwa “Isra’ilawa”? A wasu wurare a cikin ayoyin Littafi Mai Tsarki, “’ya’yan Isra’ila” ya ƙunshi maza da mata, shi ya sa yanzu aka fassara shi zuwa “Isra’ilawa.”—Fit. 1:7; 35:29; 2 Sar. 8:12.

An bi tsarin waƙa a yadda aka rubuta wasu surori a cikin Littafi Mai Tsarki don a bi tsarin yadda aka rubuta su a rubuce-rubuce na dā

Me ya sa aka bi tsarin waƙa a yadda aka rubuta wasu surori? A rubuce-rubucen asali, an rubuta yawancin Littafi Mai Tsarki yadda ake rubuta waƙa. A harsuna na zamani, ana yawan bambanta waƙa da ƙara. Amma abin da ya fi muhimmanci a waƙar Ibrananci shi ne tsarin rubutu da kuma bambancinsa. A waƙar Ibrananci ana nanata abubuwan da suka fi muhimmanci ta yadda aka tsara su ba ta kalmomin ba.

 A fassarar New World Translation na dā, an bi tsarin yadda ake rubuta waƙa a littafin Ayuba da kuma Zabura don tun asalin ya kamata a rera su kamar waƙa. Hakan yana nanata wasu kalmomi na waƙar kuma yana sa a iya tunawa da su. A juyi na 2013, an canja tsarin littattafan Misalai da Waƙar Waƙoƙi da kuma wasu littattafan annabci zuwa tsarin waƙa. An yi hakan ne don a nanata muhimman abubuwa da kuma bambancinsu. Alal misali, a Ishaya 24:2, an yi amfani da kalmomi da kishiyoyinsu don a nanata cewa babu wanda zai iya tsira daga hukuncin Allah. Wannan tsarin waƙar ya nuna cewa marubucin ba kawai yana maimaita abubuwan da ya faɗa ba ne amma yana amfani da wannan tsarin waƙa don ya nuna saƙon da Allah ya bayar yana da muhimmanci.

Ba shi da sauƙi a san bambancin da ke tsakanin waƙoƙin Ibrananci da rubutunsu. Saboda haka, fassarar Littafi Mai Tsarki sun bambanta a yadda suka bi tsarin waƙa a fassararsu. Masu fassara ne za su tsai da shawara a kan waɗanne ayoyi ne ya kamata a bi tsarin waƙa. A wasu rubuce-rubuce da aka bi tsarin waƙa, an yi amfani da karin magana da kuma maimaita muhimman kalmomin don a nanata wani batu.

Sabon tsarin da ake kira Outline of Contents (Abubuwan da Ke Ciki) da ke farkon kowane littattafan Littafi Mai Tsarki da ke cikin wannan juyin New World Translation na 2013 yana da muhimmanci sosai don yana sa a san waɗanda suka yi furuci a littafin Waƙar Waƙoƙi.

Ta yaya bincika rubuce-rubuce na ainihi ya kyautata fassarar? An ɗauko fassarar New World Translation na asali daga rubuce-rubucen Ibrananci na dā da kuma rubuce-rubucen Hellenanci da Westcott da kuma Hort suka yi. An ci gaba da yin bincike a kan rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā kuma hakan ya taimaka sosai wajen samun ƙarin bayani game da wasu ayoyi na asali. An sami wasu littattafai daga Tekun Gishiri, kuma hakan ya sa aka ƙara yin bincike a kan rubuce-rubucen Hellenanci na dā. Ana iya samun sababbin asalin rubutun Littafi Mai Tsarki da aka gano kwana-kwanan nan a cikin kwamfuta, kuma hakan ya sa yana da sauƙi a gwada na Ibrananci da Helenanci don a san wanda ya fi dacewa. Kwamitin Fassara Littafi Mai Tsarki na New World Translation sun yi amfani da wannan zarafi don su yi bincike a kan wasu ayoyi, kuma hakan ya sa aka yi wasu canje-canje.

Alal misali, game da littafin 2 Sama’ila 13:21, littattafai na Septuagint a yaren Girka suna ɗauke da waɗannan kalmomin: “Amma ba ya son ya ɓata wa ɗansa rai, yana ƙaunarsa domin shi ne ɗansa na fari.” Babu waɗannan kalmomin a Juyin New World Translation na dā domin ba sa cikin rubuce-rubuce na dā. Amma akwai waɗannan kalmomin a littattafai na Tekun Gishiri kuma an haɗa su a juyin New World Translation na 2013. Hakazalika, an mayar da sunan Allah a wurare biyar a cikin littafin Sama’ila ta Fari. Bincike da ake yi a littattafan Hellenanci ya sa aka yi wasu canje-canje a yadda aka bayyana abubuwa a littafin Matta 21:29-31. Saboda haka, an yi wasu canje-canje bisa ga abubuwa da aka gano a rubuce-rubuce na dā, ba wai an bi rubuce-rubucen Hellenanci kawai ba.

Waɗannan ne kaɗan daga cikin canje-canje da aka yi a juyin New World Translation na 2013. Hakan zai taimaka wa waɗanda suka ɗauki wannan kyautar daga Allah mai ma’amala da mutane su ji daɗin karanta Kalmar Allah kuma su fahimci abin da suka karanta.