Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TARIHI

Na Kyautata Dangantakata da Allah da Kuma Mahaifiyata

Na Kyautata Dangantakata da Allah da Kuma Mahaifiyata

MAHAIFIYATA ta ce: “Me ya sa ba za ki bauta wa kakanninmu ba? Ba ki san cewa su ne suka ba ki rai ba? Ba za ki gode musu ba? Me ya sa za ki ƙi bin al’adar iyayenmu? Idan kika ƙi ki girmama kakanninmu, kina gaya mana cewa bautarmu banza ce.” Sai mahaifiyata ta fara kuka.

Na yi mamaki da mahaifiyata ta faɗi hakan don ita ce ta ce Shaidun Jehobah su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Ta yi haka ne don ba ta son su yi nazari da ita, duk da haka, ina yi mata biyayya a koyaushe kuma ina bin umurninta. Amma yanzu, dole ne na ƙi bin umurninta don na faranta wa Jehobah rai. Da a ce Jehobah bai taimaka min ba, da ban iya na yin hakan ba.

NA KOYA GAME DA JEHOBAH

Muna bin addinin Buddha ne kamar yawancin mutane a Japan. Amma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah suka yi da ni cikin wata biyu, ya tabbatar min cewa abin da nake koya gaskiya ne. Sanin cewa ina da Uba a sama ya sa na yi marmarin koya game da shi. Nakan gaya wa mahaifiyata abin da nake koya kuma ta yi farin ciki. Sai na fara halartar taro a Majami’ar Mulki ranar Lahadi. Yayin da nake ci gaba da koyo game da Jehobah, na gaya wa mahaifiyata cewa ba zan ci gaba da saka hannun a bukukuwa na addinin Buddha ba. Nan take sai halinta ya canja kuma ta ce: “Abin kunya ne a ce wani a cikin iyalinmu ba ya ƙaunar kakanninmu.” Kuma ta ce in daina nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma halartan taro. Ban taɓa tsammani cewa mahaifiyata za ta yi wannan maganar ba. Sai ka ce ba ita ba.

Na koya a cikin littafin Afisawa sura 6 cewa Jehobah yana so na yi wa iyayena biyayya. Mahaifina ya goyi bayan mahaifiyata. Da yake ina so mu sami zaman lafiya a iyalinmu, sai na yi tunani cewa idan na yi musu biyayya, za su amince in ci gaba da nazari da kuma halartar taro. Ban da haka, ina bukatan in yi shiri don an kusa soma jarabawar shiga aji huɗu na makarantar sakandare. Saboda haka, na gaya wa iyayena cewa zan daina halartar taro na tsawon wata uku. Amma na yi wa Jehobah alkawari cewa zan soma halartar taro da zarar na gama jarabawar.

Wannan shawarar da na yanke ba ta taimaka ba a hanyoyi biyu. Da farko na yi tunanin cewa a cikin watanni uku, ƙaunar da nake yi wa Jehobah ba za ta ragu ba. Amma a maimakon haka, dangantakata da shi ta fara sanyi. Na  biyu, iyayena sun ƙara yin iya ƙoƙarinsu su ga cewa na daina duk wani abin da ya shafi ibadata ga Jehobah.

NA SAMI TAIMAKO KUMA NA FUSKANCI HAMAYYA

Na haɗu da ’yan’uwa da yawa a Majami’ar Mulki da suka fuskanci irin wannan hamayya. Sun ƙarfafa ni kuma sun ce Jehobah zai ba ni ƙarfin jurewa. (Mat. 10:34-37) Kuma sun gaya min cewa idan na kasance da aminci, iyayena za su iya soma bauta wa Jehobah. Saboda haka, na soma addu’a sosai kuma na dogara ga Jehobah.

Iyayena sun tsananta min a hanyoyi dabam-dabam. Mahaifiyata ta roƙe ni in daina nazarin kuma ta bayyana min dalilan da suka sa take so in yi hakan. Yawancin lokaci, ba na magana. Amma a duk lokacin da na yi magana, mukan yi rigima domin kowa yana son ya nuna cewa maganarsa ce daidai. Amma yanzu na gane cewa da abubuwa sun yi mana sauƙi da a ce na fahimci mahaifiyata kuma na daraja addinin da take bi. Iyayena sun ƙara min aikin da nake yi a gida don kada na riƙa fita waje. A wani lokaci, sukan kulle ni a gida ko kuma su hana ni abinci.

Mahaifiyata ta fara neman taimako daga wurin mutane. Ta roƙi malamina ya yi min magana amma ya ce ba ruwansa. Sai mahaifiyata ta gaya wa manajansu a wurin aiki ya gaya min cewa dukan addinai ba su da amfani. Mahaifiyata ta ƙira dangina tana kuka kuma tana roƙonsu su taimake ta. Hakan ya ɓata min rai sosai. Amma a taro, dattawa sun gaya min cewa a duk lokacin da mahaifiyata take gaya wa mutane game da batun, tana musu wa’azi ne ba da sanin ta ba.

 Iyayena suna so in je jami’a don na sami aiki mai kyau. Tun da muna yawan rigima a duk lokacin da muke tattauna wasu batutuwa, sai na soma rubuta musu wasiƙa don na bayyana musu maƙasudina. Hakan ya sa mahaifina ya ji haushi kuma ya ce: “Idan kina gani za ki iya sami aiki to ki samu kafin gobe ko kuma ki bar gidan nan.” Na yi addu’a ga Jehobah game da hakan. Washegari, ina wa’azi sai wasu ’yan’uwa mata biyu suka ce in zo in riƙa koyar da yaransu mata biyu. Mahaifina bai jin daɗin hakan ba kuma ya daina magana da ni. Mahaifiyata ta ce ta gwammace in zama gagararriya da in zama Mashaidiyar Jehobah.

Jehobah ya taimaka mini in daidaita tunanina kuma in san abin da zan yi

A wani lokaci, ina shakka ko Jehobah ya amince da jayayyar da nake yi da iyayena saboda wannan matakin da na ɗauka. Saboda haka, na yi addu’a ga Jehobah kuma na yi bimbini a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ƙaunarsa. Hakan ya taimaka mini na kasance da ra’ayin da ya dace kuma na fahimci cewa iyayena suna tsananta mini ne don sun damu da ni. Jehobah ya taimaka mini in daidaita tunanina kuma in san abin da zan yi. Ƙari ga haka, ina jin daɗin wa’azi sosai kuma hakan ya sa na fara sha’awar yin hidimar majagaba.

YADDA NA SOMA HIDIMAR MAJAGABA

Da wasu ’yan’uwa mata suka ji cewa ina so in soma hidimar majagaba sai suka shawarce ni in bari sai hankalin iyayena ya kwanta. Na roƙi Jehobah ya ba ni hikimar yin abin da ya dace. Na yi wasu bincike kuma na yi tunanin abin da ya sa nake so in soma hidimar majagaba. Ƙari ga haka, na tattauna da wasu ’yan’uwa mata da maza da suka manyanta. Bayan haka, sai na yanke shawara cewa ina son in faranta wa Jehobah rai. Na fahimci cewa ko da na jira na ɗan lokaci kafin in fara hidimar majagaba, iyayena za su ci gaba da tsananta mini.

Na soma hidimar majagaba sa’ad da nake aji shaida a makarantar sakandare. Ba da daɗewa ba da na soma yin hidimar majagaba, sai na soma sha’awar zuwa idan ake bukatar masu wa’azi sosai. Amma iyayena ba sa son in yi nesa da gida. Saboda haka, na jira sai na kai shekara 20 tukuna. Na gaya wa ofishin Shaidun Jehobah cewa su tura ni hidima a Japan ta kudu kusa da inda danginmu suke don hankalin mahaifiyata ya kwanta.

Yayin da nake wannan hidimar, na yi farin ciki sa’ad da wasu da na yi nazari da su suka yi baftisma. Da yake ina so na faɗaɗa hidimata, sai na koyi Turanci. Akwai wasu ’yan’uwa biyu majagaba na musamman a ikilisiyarmu. Ganin ƙwazonsu da kuma yadda suke taimaka wa mutane ya sa na soma sha’awar yin hidimar majagaba ta musamman. Sau biyu, mahaifiyata ta yi rashin lafiya mai tsanani. A duk lokacin da hakan ya faru nakan koma gida don na kula da ita. Hakan ya ba ta mamaki sosai kuma sai ta ɗan soma shiri da ni.

JEHOBAH YA ALBARKACE NI SOSAI

Bayan shekaru bakwai, ɗaya daga cikin majagaba na musamman da na ambata ɗazu mai suna Atsushi ya aiko mini da saƙo. Ya ce yana so ya yi aure amma yana tunanin ko mene ne ra’ayina game da shi. Ban taɓa tunanin soyayya da Atsushi ba kuma ban yi zaton shi ma yana so na ba. Bayan wata ɗaya, sai na gaya masa cewa na yarda mu soma fita zance. Sai na zo na gane cewa muna da maƙasudi ɗaya. Muna so mu yi hidima ta cikkaken lokaci kuma muna a shirye mu yi hidima a duk idan aka aika mu. Da shigewar lokaci, muka yi aure kuma na yi farin cikin cewa iyayena da kuma wasu danginmu sun halarci bikin aurenmu!

Nepal

Bayan aurenmu, mun ci gaba da hidimar majagaba na kullum tare kuma ba da daɗewa ba aka naɗa Atsushi a matsayin wakilin mai kula da da’ira. Jim kaɗan bayan haka, mun sake samun  wata albarka. An naɗa mu majagaba na musamman, bayan haka maigidana ya zama mai kula da da’ira. Bayan mun gama ziyarar dukan ikilisiyoyin da ke da’irar, sai aka kira mu a waya daga ofishin Shaidun Jehobah kuma aka tambaye mu ko za mu so mu yi hidimar mai kula da da’ira a ƙasar Nepal.

Yin hidima a ƙasashe dabam-dabam ya sa na koyi abubuwa da yawa game da Jehobah

Na yi ta tunanin yadda iyayena za su ji idan na gaya musu cewa za mu je hidima a wata ƙasa. Saboda haka, na kira su a waya kuma na gaya musu. Mahaifina ya ce: “Za ku tafi wuri mai kyau.” Ashe wani abokinsa ya ba shi wani littafi game da Nepal mako ɗaya kafin na kira su, kuma mahaifina yana tunanin cewa Nepal ƙasa ce mai kyau da zai so ya je yawon buɗe ido.

Yayin da muke yin hidimarmu da farin ciki tare da ’yan’uwa da ke ƙasar Nepal, mun sami wata albarka. An haɗa ƙasar Bangladesh a da’irarmu. Ƙasar ba ta da nisa daga Nepal amma sun bambanta da juna sosai. Mun yi wa mutane dabam-dabam wa’azi. Bayan shekara biyar, aka ce mu koma yin hidima a ƙasar Japan. Har yanzu, muna jin daɗin hidimarmu a matsayin mai kula da da’ira.

Na koyi abubuwa da yawa game da Jehobah a hidimar da muka yi a ƙasashe Japan da Nepal da kuma Bangladesh! Kowace ƙasa tana da nata tarihi da kuma a’lada. Kuma a cikin kowace ƙasa mutane sun bambanta da juna. Na ga cewa Jehobah yana kula da mutane, yana taimaka musu da kuma yi musu albarka.

Ina da dalilai da yawa na gode wa Jehobah don ya ba ni gatan saninsa, ya ba ni aikin yi da kuma mijin kirki. Ya taimaka mini in yanke shawarwari masu kyau kuma yanzu ina da dangantaka mai kyau da shi da kuma iyalina. Ina godiya ga Jehobah cewa na shirya da mahaifiyata. Yanzu mu abokai ne na kud da kud. Ina matuƙar godiya cewa na sami gatan kyautata dangantakata da Allah da kuma mahaifiyata.

Muna farin ciki sosai a hidimar mai kula da da’ira