Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Bari Furucinka Ya Kasance da Dadin Ji

Bari Furucinka Ya Kasance da Dadin Ji

“Bari batutuwan bakina, . . . su zama abin karɓa a gareka, Ya Ubangiji.”—ZAB. 19:14.

WAƘOƘI: 82, 77

1, 2. Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yin magana da wuta?

A SHEKARA ta 1871, dajin da ke arewa maso gabashin jihar Wisconsin a Amirka ta kama wuta. Nan da nan, wutar ta yaɗu kuma ta ƙona itatuwa biliyan biyu ƙurmus. Ƙari ga haka, wutar ta halaka mutane fiye da 1,200 kuma wataƙila wutar ta soma da tartsatsi ne lokacin da wani jirgin ƙasa yake wucewa kusa da dajin. Hakan ya tuna mana abin da aka rubuta a Yaƙub 3:5 cewa: “Duba yadda wuta ƙanƙanuwa ta kan kunna babban kurmi!” Me ya sa wannan marubucin Littafi Mai Tsarki ya yi irin wannan magana?

2 An bayyana abin da Yaƙub yake nufi a aya ta 6 cewa: “Harshe kuwa wuta ne.” Harshe a wannan ayar yana nufin maganar da muke yi, kamar wuta, furucinmu yana iya ɓarna sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce “mutuwa da rai suna cikin ikon harshe.” (Mis. 18:21) Shin hakan yana nufin cewa za mu daina yin magana domin kada mu ɓata wa wani rai ne? A’a. Ba za mu daina yin amfani da wuta don kada ta ƙona mu ba. Maimakon haka, za mu mai da hankali ga yadda muke amfani da wuta. Alal misali, za mu iya yin amfani da wuta mu dafa abinci, mu ji ɗumi kuma mu haskaka gidanmu. Hakazalika, idan muka mai da hankali ga yadda muke magana, za mu iya yin amfani da furucinmu  don mu yabi Jehobah kuma mu amfani wasu.—Zab. 19:14.

3. Waɗanne batutuwa uku ne game da yin magana za mu tattauna?

3 Jehobah ya ba mu baiwar bayyana ra’ayinmu da kuma yadda muke ji, kuma muna amfani da wannan baiwar ta wurin yin magana ko kuma ta yin yaren kurame. Saboda haka, ta yaya za mu yi amfani da wannan baiwa mai kyau don mu ƙarfafa wasu? (Karanta Yaƙub 3:9, 10.) Za mu tattauna abubuwa uku masu muhimmanci sa’ad da muke yin magana, wato lokacin da ya kamata mu yi magana, abin da ya kamata mu faɗa da kuma yadda za mu yi magana?

LOKACIN DA YA KAMATA KA YI MAGANA

4. Ka ba da misalin lokacin da ya dace mutum ya yi “shiru.”

4 Duk da cewa muna yin magana kullum, bai dace mu riƙa yin magana a kowane lokaci ba. Littafi Mai Tsarki ya ce akwai “lokacin shiru.” (M. Wa. 3:7) Yin shiru a lokacin da wasu suke magana yana nuna cewa muna daraja su. (Ayu. 6:24) Ƙari ga haka, bai dace mu riƙa magana a kan abin da bai shafe mu da kuma abin da bai dace mutane su sani ba. (Mis. 20:19) Ya dace mu kame kanmu sa’ad da mutane suka ɓata mana rai.—Zab. 4:4.

5. Ta yaya za mu nuna godiya ga baiwar yin magana da Allah ya ba mu?

5 Amma kuma Littafi Mai Tsarki ya ce akwai “lokacin magana.” (M. Wa. 3:7) Idan abokinka ya ba ka kyautar wani abu mai kyau, shin za ka ɓoye shi ne? A’a, maimakon haka, za ka nuna godiya ta wajen yin amfani da kyautar. Saboda haka, muna nuna godiya ga baiwar yin magana da Jehobah ya ba mu ta wajen yin magana a hanyar da ta dace. Hakan ya ƙunshi furta ra’ayinmu da kuma faɗan abin da muke bukata. Ƙari ga haka, za mu ƙarfafa mutane ta furucinmu kuma mu yabi Allah. (Zab. 51:15) Ta yaya za mu san lokacin da ya dace mu yi “magana”?

6. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna muhimmancin yin magana a lokacin da ya dace?

6 Kalaman da ke rubuce a Misalai 25:11 sun nuna muhimmancin yin magana a lokacin da ya dace: “Magana a kan kari tana kama da tuntuwa na zinariya cikin kwanduna na azurfa.” Aful na zinariya suna da kyau sosai, amma sun fi kyau idan aka yi zubin a kan azurfa. Hakazalika, yin magana a lokacin da ya dace zai sa mutane su saurari maganarmu kuma su bi shawararmu. Ta yaya za mu yi hakan?

7, 8. Ta yaya ’yan’uwanmu da ke Japan suka yi koyi da misalin Yesu ta wajen yin magana game da tashin matattu a lokacin da ya dace?

7 Wataƙila abin da muke so mu faɗa yana da daɗin ji, amma idan ba mu yi hakan a lokacin da ya dace ba, mutane ba za su fahimci ko kuma amince da abin da muke faɗa ba. (Karanta Misalai 15:23.) Alal misali, a watan Maris, 2011, girgizar ƙasa da tsunami sun addabi wasu wurare a gabashin ƙasar Japan kuma birane da yawa sun halaka sanadiyyar haka. Mutane fiye da 15,000 ne suka mutu. Ko da yake Shaidun Jehobah da ke wurin sun yi rashin danginsu da abokansu, suna son su yi amfani da Littafi Mai Tsarki don su taimaka wa waɗanda suke cikin irin wannan yanayin. Ƙari ga haka, sun san cewa yawancin mutanen suna bin addinin Budha kuma ba su san koyarwar Littafi Mai Tsarki ba. ’Yan’uwanmu sun fahimci cewa wannan ba lokacin gaya wa masu makoki game da tashin matattu ba. Maimakon haka, sun yi musu ta’aziyya da kuma bayyana musu dalilin da ya sa mutanen kirki suke shan wahala.

8 Yesu ya san lokacin yin shiru da kuma lokacin da ya dace ya yi magana. (Yoh. 18:33-37; 19:8-11) Akwai lokacin da ya gaya  wa almajiransa: “Ina da sauran zance da yawa da zan yi maku tukuna, amma ba ku iya ku ɗauke su yanzu ba.” (Yoh. 16:12) Shaidu da ke gabashin ƙasar Japan sun bi misalin Yesu. Bayan shekara biyu da rabi da tsunamin ya faru, sun yi kamfen na rarraba warƙa Bishara ta Mulki na 38, mai jigo “Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?” A wannan lokacin, mutane da yawa sun karɓi warƙar kuma abin da suka karanta game da tashin matattu ya ƙarfafa su sosai. Ya kamata mu ma mu yi tunani game da al’ada da imanin mutane da ke yankinmu don mu san lokacin da ya dace mu yi musu magana.

9. A waɗanne yanayi ne ya kamata mu yi magana?

9 Ya kamata mu san yanayin da ya dace mu yi magana. Alal misali, wani yana iya ɓata mana rai, ko da bai da niyyar yin hakan. A wannan lokacin ya kamata mu yi tunani ko ya dace mu ba da amsa don abin da ya faɗa. Idan muna son mu yi magana, ba zai dace mu yi hakan sa’ad da muke fushi don wannan zai sa mu yi magana da garaje. (Karanta Misalai 15:28.) Ko kuma wataƙila muna son mu gaya wa danginmu game da Jehobah, wajibi ne mu kasance da haƙuri kuma mu yi tunani sosai a kan abin da muke son mu faɗa. Ƙari ga haka, muna bukatar mu yi hakan a lokacin da za su so su saurare mu.

ABIN DA YA KAMATA KA FAƊA

10. (a) Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga abin da muke faɗa? (b) Wace hanyar yin magana ce ya kamata mu guji?

10 Abin da muka faɗa zai iya sa mutane farin ciki ko kuma ya sa su baƙin ciki. (Karanta Misalai 12:18.) Mutane da yawa a duniya suna amfani da kalmomi da za su sa mutane baƙin ciki. Suna koyan wannan daga fina-finai ko shirye-shiryen talabijin da ke sa su “wasa harshensu kamar takobi” kuma su yi amfani da “kibawunsu, wato maganganu masu-zafi.” (Zab. 64:3) Ya kamata Kirista ya guji wannan halin. Alal misali “maganganu masu zafi” sun ƙunshi yin baƙar magana da ke sa a raina ko tsauta wa wasu. Wasu suna yin hakan don su sa mutane dariya, amma yana kawo cin mutunci. Baƙar magana yana cikin furuci da ya kamata Kiristoci su daina amfani da su. Yana da kyau mu yi furuci na ban dariya, amma bai kamata mu yi hakan ta wajen yin magana da zai ɓata wa mutane rai ko kunyantar da su ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada kowane ruɓaɓɓen zance shi fita daga cikin bakinku, sai irin abin da ke mai-kyau garin ginawa yayin da ake bukata, domin shi ba da alheri ga waɗanda suke ji.”—Afis. 4:29, 31.

11. Mene ne zai taimaka mana mu yi maganar da ta dace?

11 Yesu ya ce “daga cikin yalwar zuciya baki ya kan yi magana.” (Mat. 12:34) Wannan yana nufin cewa abubuwan da muke faɗa yana nuna abin da ke cikin zuciyarmu. Saboda haka, idan muna son mutane kuma mun damu da su da gaske, hakan zai sa mu yi amfani da furucin da suka dace sa’ad da muke musu magana. Ƙari ga haka, zai sa mu yi maganganu masu daɗi da kuma ban ƙarfafa.

12. Mene ne zai taimaka mana mu yi amfani da kalmomin da suka dace?

12 Muna bukatar mu yi ƙoƙari sosai don mu yi amfani da kalmomin da suka dace. Ko Sarki Sulemanu mai hikima ya yi tunani da kuma bincike sosai don “ya sami magana masu-daɗin ji” da kalmomin gaskiya da suka dace. (M. Wa. 12:9, 10) Shin mene ne zai taimaka mana mu yi amfani da kalmomi “masu-daɗin ji”? Muna iya karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu don mu ga yadda ake yin amfani da kalmomi. Muna iya koyan ma’anar furuci  da ba mu fahimta ba. Ƙari ga haka, muna iya koyan faɗin magana a yadda furucinmu zai amfani mutane. Sa’ad da Littafi Mai Tsarki yake magana game da dangantakar da ke tsakanin Jehobah da Ɗansa na fari, ya ce: “Ubangiji Yahweh ya ba ni [Yesu] harshe na koyayyun mutane, domin in san yadda zan tokare da magana wanda ya gaji.” (Isha. 50:4) Yin tunani sosai a kan abin da muke so mu faɗa zai taimaka mana mu yi amfani da kalmomi masu daɗin ji. (Yaƙ. 1:19) Muna iya tambayar kanmu, ‘Idan na yi wannan maganar, shin mutumin zai fahimci abin da nake gaya masa? Ta yaya abin da na faɗa zai shafe shi?’

13. Me ya sa yin magana da yake da sauƙin fahimta yake da muhimmanci?

13 Ana busa ƙaho a ƙasar Isra’ila don a gaya wa taron jama’a su haɗu ko kuma su koma tantinsu. Ƙari ga haka, ana busa ƙahoni don a gaya wa sojoji su yi shirin yaƙi. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da busa ƙaho don ya kwatanta amfanin yin magana da ke da sauƙin fahimta. Idan aka busa ƙaho da ba a fahimta ba, hakan zai iya kasance da lahani ga sojoji. Hakazalika, idan ba mu yi magana a yadda mutane za su fahimta ba, hakan zai iya rikitar da su ko kuma su gaskata abin da ba daidai ba. Duk da haka, ya kamata mu mai da hankali don kada abin da muke faɗa ya zama raini ko kuma mu kasance da rashin mutunci.—Karanta 1 Korantiyawa 14:8, 9.

14. Ka ba da misalin yadda Yesu ya yi amfani da furuci mai sauƙin fahimta.

14 An nuna misali mai kyau a yadda Yesu ya yi amfani da kalmomi masu sauƙin fahimta a cikin Matta sura 5 zuwa 7. A jawabinsa, bai yi ƙoƙari ya burge mutane ta wajen yin amfani da kalmomi masu wuya da ba su dace ba. Kuma bai faɗi abubuwa da za su ɓata wa mutane rai ba. Yesu ya koyar da abubuwa masu muhimmanci da suke da ma’ana masu zurfi, amma ya yi hakan a hanyar da take da sauƙin fahimta. Alal misali, lokacin da Yesu yake son ya tabbatar wa almajiransa cewa bai kamata su damu game da abinci da za su ci a kowace rana ba, ya bayyana musu cewa Jehobah yana ciyar da tsuntsaye, kuma ya tambaye su: “Ku ba ku fi su daraja da yawa ba?” (Mat. 6:26) Ta yin amfani da waɗannan kalmomi masu sauƙin fahimta, Yesu ya taimaka musu su fahimci wani darasi mai muhimmanci kuma hakan ya ƙarfafa su sosai. Bari mu tattauna batu na uku na furucinmu da yake da muhimmanci.

YADDA YA KAMATA KA YI MAGANA

15. Me ya sa ya kamata mu yi maganar alheri ga mutane?

15 Yadda muke wa mutane magana yana da muhimmanci sosai. Sa’ad da Yesu ya ba da jawabi a majalisar da ke garinsu a Nazarat, mutane sun yi ‘mamaki da zantattukan alheri da suka fito daga bakinsa.’ (Luk. 4:22) Idan muka yi wa mutane magana a hanyar da ta dace, za su saurare mu kuma su amince da abin da muka faɗa. (Mis. 25:15) Idan muna daraja mutane kuma mun damu da yadda suke ji, za mu riƙa yi musu maganar alheri. Abin da Yesu ya yi ke nan. Alal misali, sa’ad da Yesu ya ga yadda taron jama’a suke ƙoƙari su je su sami shi don su ji koyarwarsa, sai ya ji tausayinsu kuma “ya fara koya masu abu da yawa.” (Mar. 6:34) Ko a lokacin da ake zaginsa, Yesu bai rama ba ta wajen yin baƙar magana.—1 Bit. 2:23.

16, 17. (a) Ta yaya za mu yi koyi da Yesu sa’ad da muke magana da iyalanmu da kuma abokanmu a cikin ikilisiya? (Ka duba hoton da ke shafi na 18.) (b) Ka ba da misali da ya nuna amfanin yin maganar alheri.

16 Ko da yake muna ƙaunar iyalanmu da abokanmu, bai kamata mu yi musu baƙar  magana don mun san su sosai ba. Muna iya ganin cewa ba ma bukatar mu mai da hankali a yadda muke musu magana. Shin Yesu ya yi wa abokansa baƙar magana? A’a! Sa’ad da suka ci gaba da musu a kan wanda ya fi girma, Yesu ya yi musu gargaɗi da maganar alheri kuma ya yi musu kwatanci da ƙaramin yaro. (Mar. 9:33-37) Dattawa suna iya yin koyi da Yesu ta wajen ba da gargaɗi “cikin ruhun tawali’u.”—Gal. 6:1.

17 Sa’ad da wani ya faɗi abin da ya ɓata mana rai, zai fi kyau mu amsa ta yin furuci mai kyau. (Mis. 15:1) Alal misali, ɗan wata ’yar’uwa yana yin abubuwan da ba su dace ba kuma yana nuna cewa yana bauta wa Jehobah. Sai wata ’yar’uwa ta ce mata: “Allah-sarki, ba ki tarbiyyartar da ɗanki da kyau ba.” Ta faɗi hakan ne ba don ta ɓata wa mahaifiyar rai ba. Sai mahaifiyar yaron ta yi tunani kuma ta ce: “Da gaske ne cewa, abubuwa sun ɓace a yanzu, amma har ila ina kan tarbiyyartar da shi. Ki tambaye ni bayan Armageddon, sai mu san ko abin da kika faɗa gaskiya ne.” Amsar da mahaifiyar ta ba da ya sa sun ci gaba da abokantaka. Ƙari ga haka, ɗanta yana sauraronsu sa’ad da suke wannan maganar kuma hakan ya ƙarfafa shi. Ya fahimci cewa har ila mahaifiyarsa ta tabbata da shi, sai ya daina cuɗanya da abokan banza. Da shigewar lokaci sai ya yi baftisma kuma daga baya ya yi hidima a Bethel. Ko muna magana ga ’yan’uwanmu ko iyalanmu ko kuma mutane da ba mu sani ba, ya kamata maganarmu “ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri.”—Kol. 4:6.

18. Ta yaya bin misalin Yesu zai taimaka mana mu yi amfani da kalmomi masu daɗin ji?

18 Hakika, gaya wa mutane abin da muke tunaninsa da kuma yadda muke ji, baiwa ce mai kyau daga Jehobah. Idan muka bi misalin Yesu, za mu san lokacin da ya kamata mu yi magana, mu san abin da ya kamata mu faɗa kuma furucinmu ya kasance da daɗin ji. Idan muka yi hakan, furucinmu zai ƙarfafa mutane kuma mu faranta wa Jehobah rai, wanda ya ba mu baiwar yin magana.