Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Mene ne ya nuna cewa ba a kewaye birnin Yariko na dā na tsawon lokaci kafin a ci ta da yaƙi ba?

A cikin littafin Joshua 6:10-15, 20, an ambata cewa sojojin Isra’ilawa sun zagaya birnin Yariko sau ɗaya kowace rana a cikin kwanaki shida. A rana ta bakwai, sun zagaya birnin sau bakwai kuma Allah ya sa garun birnin ya faɗi. Hakan ya ba Isra’ilawa dama su shiga birnin kuma su halaka shi. Shin masu tonon ƙasa sun sami hujja da ta nuna cewa ba a ɓata lokaci ba wajen halaka Yariko kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ambata ne?

A zamanin dā, kafin sojoji su kai hari a wani birni, sukan kewaye garun. Idan sun kewaye birnin na tsawon lokaci, mazauna birnin za su cinye yawancin abincin da suke da shi. Ƙari ga haka, sa’ad da sojoji suka ci wani gari da yaƙi, sukan kwashe dukan abubuwan da suke so, har da abincin da ya rage a garin. Shi ya sa masu tonon ƙasa ba su sami raguwar abinci sosai ba a biranen Falasɗinu da aka ci da yaƙi. Amma, littafin Biblical Archaeology Review ya ce game da kangayen Yariko: “Ban da tukwane, an sami hatsi mai yawan gaske. . . . Ba a samun hatsi kamar haka a wasu biranen da aka ci da yaƙi.”

Littafi Mai Tsarki ya ce Isra’ilawa ba su kwashe hatsin birnin Yariko ba domin Jehobah ya ba su umurni cewa kada su yi hakan. (Josh. 6:17, 18) Isra’ilawa sun kai musu hari a lokacin kaka, jim kaɗan bayan sun gama girbi kuma sun tara hatsi mai yawa. (Josh. 3:15-17; 5:10) Hakika, tun da yake an sami hatsi mai yawa, hakan ya nuna cewa, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ambata, sojojin Isra’ilawa sun kewaye birnin Yariko na ɗan lokaci ne kafin su halaka birnin.