Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Yi Hattara, Shaidan Yana So Ka Bijire!

Ka Yi Hattara, Shaidan Yana So Ka Bijire!

Ku yi zaman tsaro: magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.”1 BIT. 5:8.

1. Ta yaya wani halitta ya zama Shaiɗan?

HALITTAN nan da ya zama Shaiɗan, a dā shi mala’ika ne mai aminci. Amma daga baya ya soma sha’awar bautar da ’yan Adam suke wa Jehobah. Maimakon ya daina irin wannan sha’awar, sai ya ci gaba da yin tunanin a kai har ya kai shi ga yin zunubi. (Yaƙ. 1:14, 15) Saboda haka, Shaiɗan “ba ya tsaya a kan gaskiya ba.” Ya yi tawaye kuma ya zama “uban ƙarya.”—Yoh. 8:44.

2, 3. Mene ne ma’anar “Shaiɗan” da “Iblis” da kuma “maciji,” wato sunayen da aka ba wa babban abokin gāban Jehobah?

2 Tun ya yi tawaye, Shaiɗan ya zama babban abokin gaban Jehobah da kuma na ’yan Adam. Laƙabi da aka ba Shaiɗan ya nuna irin mugun halinsa. Shaiɗan yana nufin “Mai tsayayya” kuma hakan ya nuna cewa wannan mugun ba ya goyon bayan sarautar Allah, maimakon haka, yana matuƙar gāba da shi. Burin Shaiɗan shi ne ya kawo ƙarshen sarautar Jehobah.

3 Kamar yadda aka nuna a Ru’ya ta Yohanna 12:9, an kira Shaiɗan, Iblis wato “Mai tsegumi.” Hakan ya tuna mana cewa Shaiɗan ya ɓata sunan Jehobah sa’ad da ya kira shi maƙaryaci. Furucin nan ‘tsohon maciji’ ya tuna mana ranar da Shaiɗan ya  yi amfani da maciji a Adnin don ya yaudari Hawwa’u. Kalaman nan “babban maciji” ya kwatanta Shaiɗan da kyau. Me ya sa? Don shi azzalumi ne da kuma mugu. Burinsa shi ne ya hana nufin Allah cika kuma ya halaka bayin Allah.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Hakika, da yake muna bauta wa Jehobah da aminci, Shaiɗan ya mai da kansa babban abokin gabanmu. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi mana kashedi: “Ku yi hankali shimfiɗe, ku yi zaman tsaro: magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bit. 5:8) Bisa ga wannan kashedin, a wannan talifin za a tattauna halayen Shaiɗan guda uku da ya nuna dalilin da ya sa ya kamata mu kāre kanmu daga wannan babban magabcin Jehobah da kuma na ’yan Adam.

SHAIƊAN YANA DA IKO

5, 6. (a) Ka ba da misalan da suka nuna cewa mala’iku “ƙarfafa masu-iko” ne. (b) A wace hanya ce Shaiɗan yake haddasa “mutuwa”?

5 Halittu da ake kira mala’iku “ƙarfafa masu-iko” ne. (Zab. 103:20) Sun fi ’yan Adam iko da basira da kuma ƙarfi. Hakika, mala’iku masu aminci suna amfani da ikonsu don su taimaka. Alal misali, akwai lokacin da wani mala’ika ya halaka sojojin Assuriyawa guda 185,000. Babu ɗan Adam ko rundunar soja da za su iya cim ma hakan. (2 Sar. 19:35) A wani lokaci kuma mala’ika ya yi amfani da ikonsa da basira don ya saki manzannin Yesu daga kurkuku. Ko da yake masu gadin suna wurin, ba su ga lokacin da mala’ikan ya buɗe ƙofofin ya saki manzannin kuma ya rufe ƙofofin ba.—A. M. 5:18-23.

6 Mala’iku masu aminci suna amfani da ikonsu don su taimaka wa mutane, amma Shaiɗan yana amfani da ikonsa don ya aikata mugunta. Babu shakka, Shaiɗan yana da iko kuma yana da tasiri a kan mutane. Littafi Mai Tsarki ya kira shi “mai-mulkin wannan duniya” da kuma “allah na wannan zamani.” (Yoh. 12:31; 2 Kor. 4:4) Shaiɗan Iblis yana da ikon haddasa “mutuwa.” (Ibran. 2:14) Hakan ba ya nufin Shaiɗan yana kashe dukan mutane kai tsaye. Amma halinsa na ƙiyayya da mugunta ya zama ruwan dare. Hawwa’u ta saurari ƙaryar da Shaiɗan ya yi kuma Adamu ya yi wa Allah rashin biyayya. Saboda haka, zunubi da mutuwa suka bi kan dukan mutane. (Rom. 5:12) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Iblis yana haddasa “mutuwa.” Shi mai “mai-kisan kai” ne kamar yadda Yesu ya faɗa. (Yoh. 8:44) Hakika, Shaiɗan babban magabcinmu ne!

7. Ta yaya aljannu suka nuna cewa su masu iko ne?

7 Idan muka yi tsayayya da Shaiɗan muna tsayayya da dukan waɗanda suke goyon bayansa da waɗanda suke tawaye da sarautar Allah. Waɗannan sun ƙunshi wasu halittun da suka yi tawaye, wato aljannu. (R. Yoh. 12:3, 4) Sau da sau waɗannan aljannun suna nuna ikonsu ta wurin gana wa mutane azaba. (Mat. 8:28-32; Mar. 5:1-5) Kada ka raina ikon waɗannan aljannu ko kuma na “sarkin aljanu.” (Mat. 9:34) In ba tare da taimakon Jehobah ba, ba za mu yi nasara da Shaiɗan ba.

SHAIƊAN MUGU NE

8. (a) Mene ne burin Shaiɗan? (Ka duba hoton da ke shafi na 9.) (b) Bisa ga abin da ka lura, ta yaya mutanen duniya suke koyi da Shaiɗan da kuma mugun halinsa?

8 Manzo Bitrus ya kwatanta Shaiɗan da “zaki mai-ruri.” Kalmar Helenanci da aka fassara “ruri” bisa ga wani littafin  bincike yana nufin “kukar da dabbar take yi a daji idan tana jin yunwa sosai.” Hakan ya nuna cewa Shaiɗan mugu ne, ko ba haka ba? Shaiɗan yana neman ƙarin mutane su bijire ko da yake shi ne yake iko da dukan duniya. (1 Yoh. 5:19) Shaiɗan ya mai da hankali ga shafaffu da kuma abokan aikinsu wato, waɗansu tumaki. (Yoh. 10:16; R. Yoh. 12:17) Burin Shaiɗan shi ne ya halaka bayin Jehobah. Irin tsanantawa da ya yi wa mabiyan Yesu tun daga ƙarni na farko har zuwa yanzu ya nuna cewa shi mugu ne.

9, 10. (a) Ta yaya Shaiɗan ya yi ƙoƙarin hana nufin Allah cika game da al’ummar Isra’ila? (Ka ba da misalai.) (b) Me ya sa Shaiɗan ya fi mai da hankali ga al’ummar Isra’ila ta dā? (c) Yaya kake gani Iblis yake ji sa’ad da wani bawan Jehobah ya yi babban zunubi a yau?

9 A ƙoƙarin da yake yi don ya hana nufin Allah cika, Shaiɗan ya nuna cewa shi azzalumi ne a wata hanya. Idan zaki yana jin yunwa, ba ya jin tausayin dabbar da ya kama. Ba ya jin tausayi kafin ya kashe kuma ba ya nadama bayan ya kashe. Hakazalika, Shaiɗan ba ya tausayin waɗanda yake son ya halaka. Alal misali, ka yi tunanin yadda Shaiɗan Iblis ya ji sa’ad da yake kallon yadda Isra’ilawa suka faɗa wa zina da kuma hadama. A lokacin da kake karanta labaran Zimri da ya yi zina da kuma Gehazi mai hadama, da kuma mugun sakamako da suka samu, za ka lura cewa wannan zaki mai-ruri, wato Shaiɗan ya ji daɗi saboda nasarar da ya yi a kansu.—Lit. Lis. 25:6-8, 14, 15; 2 Sar. 5:20-27.

10 Shaiɗan yana da dalili na musamman na fakon Isra’ilawa na dā. Ta wurin zuriyar al’ummar Isra’ilawa ne za a sami Almasihun da zai ƙuje kan Shaiɗan kuma ya tabbatar da cewa Jehobah ne mai ikon sarauta. (Far. 3:15) Shaiɗan ba ya son Isra’ilawa su sami ci gaba shi ya sa ya yi ƙoƙari ya rinjaye su da zunubi. Kar ka ɗauka cewa Shaiɗan ya yi nadama sa’ad da Dawuda ya yi zina ko kuma ya ji tausayin annabi Musa a lokacin da ya yi wani abin da ya hana shi shiga Ƙasar Alkawari. Maimakon haka, Shaiɗan yana farin ciki idan wani bawan Allah ya yi babban zunubi. Hakika, irin  waɗannan abubuwan ne Shaiɗan yake amfani da shi don ya yi sūkar Jehobah.—Mis. 27:11.

11. Me ya sa wataƙila Shaiɗan ya yi fakon Saratu?

11 Shaiɗan yana gāba musamman da zuriyar da Almasihun zai fito daga ciki. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru jim kaɗan bayan da aka gaya wa Ibrahim cewa zai zama “al’umma mai-girma.” (Far. 12:1-3) A lokacin da Ibrahim da matarsa Saratu suke ƙasar Masar, Fir’auna ya sa aka kawo Saratu gidansa wataƙila don ta zama matarsa. Amma Jehobah ya kāre Saratu daga wannan mawuyacin yanayin. (Karanta Farawa 12:14-20.) Irin wannan abin ya faru a Gerar jim kaɗan kafin a haifi Ishaƙu. (Far. 20:1-7) Shaiɗan ne ya ƙulla wannan makirci a waɗannan lokatan? Shin yana ganin cewa abubuwan jin daɗi da ke fādar Fir’auna da kuma na Abimelech za su Saratu ta bijire ne bayan ta bar ƙasar Ur da ke da ni’ima? Shin Shaiɗan yana tunanin cewa Saratu za ta ci amanar mijinta da Jehobah kuma ta auri ɗaya cikin waɗannan sarakuna? Littafi Mai Tsarki bai faɗi haka ba, amma muna da dalili mai kyau na gaskata cewa Iblis ya so ya hana Saratu ta cancanci haifan wannan zuriyar. Shaiɗan bai yi nadama ba cewa zai ɓata aurenta da halinta mai kyau da kuma dangantakarta da Jehobah. Hakan ya tabbatar da cewa Shaiɗan mugu ne.

12, 13. (a) Ta yaya Shaiɗan ya nuna cewa shi mugu ne bayan an haifi Yesu? (b) Yaya kake gani Shaiɗan yake ɗaukan yara da suke ƙaunar Jehobah kuma suna ƙoƙari su yi nufinsa a yau?

12 An haifi Yesu ƙarnuka da yawa bayan Ibrahim. Kar ka ɗauka cewa Shaiɗan ya yi tunani cewa wannan jaririn kyakkyawa ne sosai. Maimakon haka, ya san cewa wannan yaron zai yi girma kuma ya zama Almasihun da aka yi alkawarinsa. Hakika, Yesu ne ainihin zuriyar Ibrahim, wanda zai “halaka ayyukan Shaiɗan.” (1 Yoh. 3:8) Shin Shaiɗan ya yi tunanin cewa laifi ne ya kashe yaro? Shaiɗan bai damu da yin abin da ya dace ba. Shi ya sa bai yi jinkirin kashe Yesu ba. Ta yaya?

13 Sarki Hiridus ya yi baƙin ciki sa’ad da shehuna suka so su san inda “wanda an haife shi Sarkin Yahudawa” yake kuma ya ƙudiri niyya ya kashe jaririn. (Mat. 2:1-3, 13) Don ya tabbata cewa ya idar da nufinsa, ya ba da umurni a kashe dukan yara masu shekaru biyu ko kuma ƙasa da hakan a Baitalami da kuma wasu wuraren da ke yankin. (Karanta Matta 2:13-18.) An ceci Yesu daga wannan kisan gilla, amma mene ne wannan ya koya mana game da magabcinmu Shaiɗan? A bayyana yake cewa a wurin Shaiɗan ran ’yan Adam ba kome ba ne. Ba ya ma jin tausayin yara. Hakika, Shaiɗan “zaki mai-ruri” ne. Kada ku manta cewa shi azzalumi ne.

SHAIƊAN MAI YAUDARA NE

14, 15. Ta yaya Shaiɗan ya “makantar da hankulan marasa-bada gaskiya”?

14 Hanya ɗaya tak da Shaiɗan zai iya sa mutane su daina bauta wa Jehobah ita ce ta wurin yaudarar su. (1 Yoh. 4:8) Shaiɗan yana yaudara mutane don su ɗauka cewa ba sa “bukatar ƙulla dangantaka da Allah.” (Mat. 5:3, New World Translation) Ya “makantar da hankulan marasa-bada gaskiya, domin kada hasken bisharar darajar Kristi, wanda yake surar Allah, ya waye masu.”—2 Kor. 4:4.

15 Hanya mafi tasiri da Shaiɗan yake amfani da ita wajen yaudarar mutane ita ce ta addinin ƙarya. Yana farin ciki idan  ya ga mutane suna bauta wa kakanni da halittu ko dabbobi maimakon su bauta wa Jehobah Allah kaɗai. (Fit. 20:5) Wasu kuma da sun ɗauka suna bauta wa Allah a hanya mai kyau, alhali suna bin koyarwar ƙarya da kuma al’adu marasa amfani. Suna cikin yanayi mai ban taƙaici kamar wanda Jehobah ya faɗa musu cewa: “Don me kuke awon abin da ba abinci ba ne? kuna ɓarnatar da hakkinku domin abin da ba za shi ƙosar da ku ba? Ku sauraro gare ni da kyau, ku ci abin da ke nagari, ranku ya yi daɗi da kitse.”—Isha. 55:2.

16, 17. (a) Me ya sa Yesu ya gaya wa Bitrus: “Ka koma bayana, Shaiɗan”? (b) Ta yaya Shaiɗan zai yaudare mu mu daina yin tsaro?

16 Shaiɗan zai iya yaudarar bayin Jehobah masu aminci ma. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da Yesu ya gaya wa almajiransa cewa za a kashe shi. Manzo Bitrus da yake ƙaunar shi sosai ya ja shi gefe ya ce masa: “Allah shi sawwaƙa maka, Ubangiji: wannan ba za ya same ka ba daɗai.” Amma Yesu gabansa gaɗi ya ce wa Bitrus: “Ka koma bayana, Shaiɗan.” (Mat. 16:22, 23) Me ya sa Yesu ya kira Bitrus “Shaiɗan”? Domin Yesu ya san abin da ke gab da faruwa. Lokaci ya yi da zai ba da kansa hadaya kuma ya nuna cewa Iblis maƙaryaci ne. Ba a wannan mawuyacin lokacin ba ne a tarihin ’yan Adam Yesu zai so Allah ya “sawwaƙe” masa azabar da zai sha ba. Shaiɗan zai yi farin ciki idan Yesu bai yi hattara ba.

17 Ƙarshen wannan zamanin ya kusa, saboda haka, mu ma muna cikin miyagun zamanu. Shaiɗan ba ya son mu kasance a faɗake amma yana son mu “sawwaƙa” wa kanmu ta wurin sa mu mai da hankali ga yin suna a wannan duniyar. Kada ka yarda hakan ya faru da kai. Maimakon haka, ‘ka yi tsaro.’ (Mat. 24:42) Kada ka bar Shaiɗan ya yaudare ka da ra’ayin nan cewa ƙarshen yana da nisa ko kuma ba za ta zo ba ma sam.

18, 19. (a) Ta yaya Shaiɗan zai yaudare mu a yadda muke tunani game da kanmu? (b) Ta yaya Jehobah yake taimakonmu mu yi hankali kuma mu yi hattara?

18 Wata hanya kuma da Shaiɗan yake ƙoƙarin yaudarar mu, ita ce ya sa mu gaskata cewa Allah ba ya ƙaunarmu kuma ba zai taɓa gafarta mana zunubanmu ba. Wannan ɗaya ne cikin ƙaryace-ƙaryacen da Shaiɗan yake yaɗawa. Amma wane ne ainihi bai cancanci ƙaunar Jehobah ba? Babu shakka, Shaiɗan ne. Wane ne Jehobah ba zai taɓa gafarta masa ba? Har ila, Shaiɗan ne. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa.” (Ibran. 6:10) Jehobah yana farin ciki da ƙoƙarin da muke yi don mu bauta masa kuma hidimarmu tana da tamani a gare shi. (Karanta 1 Korintiyawa 15:58.) Saboda haka, kada mu bar Shaiɗan ya yaudare mu da ƙaryace-ƙaryacensa.

19 Kamar yadda muka tattauna Shaiɗan mai iko ne da mugu da kuma mai yaudara. Ta yaya za mu yi nasara a kan wannan babban abokin gāba? Jehobah yana kāre mu. Littafi Mai Tsarki ya koya mana yadda za mu san dabarun Shaiɗan, kuma “ba mu cikin rashin sanin makiɗansa ba.” (2 Kor. 2:11) Za mu iya yin hankali kuma mu kasance a faɗake idan muka fahimci dabarun Shaiɗan. Amma sanin dabarun Shaiɗan kawai ba zai kāre mu ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.’ (Yaƙ. 4:7) A talifi na gaba za mu tattauna hanyoyi uku da za mu iya yin tsayayya da Shaiɗan kuma mu yi nasara.