Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Ya Sa Yankan Zumunci Tsari Ne Mai Kyau?

Me Ya Sa Yankan Zumunci Tsari Ne Mai Kyau?

WANI ɗan’uwa mai suna Julian ya ce: “Sa’ad da aka yi sanarwa cewa an yi wa ɗana yankan zumunci, sai na rasa abin da ke yi min daɗi a duniyar nan. Shi ne ɗanmu na fari kuma mun shaƙu sosai, muna yin abubuwa da yawa tare. Shi ɗa ne mai hankali, amma farat ɗaya sai ya soma yin wasu abubuwan da ba su da kyau. Matata ta yi ta kuka kuma na rasa yadda zan ba ta haƙuri. Mun yi ta tunani cewa ko ba mu yi masa tarbiyya mai kyau ba.”

Ta yaya za a ce yankan zumunci tanadi ne mai kyau da yake yana sa mutum baƙin ciki sosai? Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya umurta cewa ya kamata a ɗauki wannan babban matakin? Mene ne yake sa a yi wa mutum yankan zumunci?

ABUBUWA BIYU DA SUKE SA A YI WA MUTUM YANKAN ZUMUNCI

Abubuwa biyu ne suke sa a yi wa Mashaidin Jehobah yankan zumunci kuma sai an tabbata da waɗannan abubuwa biyun. Na farko, wani da ya yi baftisma ya yi babban zunubi. Na biyu, ya ƙi tuɓa.

Ko da yake Jehobah ya san cewa mu ajizai ne, amma ya kafa ƙa’idodi da yake so bayinsa su bi. Alal misali, Jehobah ya ce mu guji zunubai kamar fasiƙanci da bautar gumaka da sata da ƙwace da kisan kai da kuma sihiri.—1 Kor. 6:9, 10; R. Yoh. 21:8.

Babu shakka mun gaskata cewa ƙa’idodin Jehobah suna da kyau kuma suna kāre mu, ko ba haka ba? Shin akwai wanda ba zai so ya zauna a cikin mutane masu kirki, masu riƙon amana da suke zaman lafiya da juna ba? Irin wannan yanayin ne muke mora a tsakanin ’yan’uwanmu Shaidun Jehobah. Muna jin daɗin irin wannan yanayin ne don muna cika alkawarin da muka yi na ba da kanmu don yin nufin Jehobah da kuma bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.

To, idan wani Mashaidin Jehobah ya aikata babban zunubi saboda wata kasawa fa? Bayin Jehobah a dā sun aikata manyan zunubai, amma Jehobah bai ƙi su gaba ɗaya ba. Sarki Dawuda ɗaya ne daga cikinsu. Dawuda ya yi zina da kuma kisan kai, duk da haka, annabi Nathan ya gaya masa: “Ubangiji . . . ya kawar da zunubinka.”—2 Sam. 12:13.

Allah ya yafe zunuban Dauda don ya tuba da gaske. (Zab. 32:1-5) Hakazalika, za a yi wa bawan Jehobah yankan zumunci idan ya ƙi ya tuba ko kuma ya ci gaba da yin zunubin. (A. M. 3:19; 26:20) Idan mai zunubin bai nuna a gaban dattawa da suka yi shari’ar cewa ya tuba da gaske ba, wajibi ne a yi masa yankan zumunci.

Da farko, za mu iya ɗauka cewa an yi hanzari wajen yi wa mai zunubin yankan zumunci ko kuma ba a yi adalci ba, musamman ma idan  mutumin danginmu ne ko kuma abokinmu. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ba da dalilai masu kyau da suka nuna cewa ya dace a ɗauki irin wannan matakin.

ME YA SA YANKAN ZUMUNCI YAKE DA AMFANI?

Yesu ya ce “hikima kuwa ta barata bisa ga ayyukanta.” (Mat. 11:19) Mataki mai kyau da aka ɗauka na yanke zumunci da wanda ya yi zunubi kuma ya ƙi tuba yana haifar da sakamako masu kyau. Ka yi la’akari da uku cikinsu:

Yi wa masu laifi yankan zumunci yana ɗaukaka sunan Jehobah. Da yake an san mu da sunan Jehobah, halinmu yana shafan sunan. (Isha. 43:10) Kamar yadda halin yaro yake sa a ɗauki iyayensa da mutunci ko kuma a raina su. Hakazalika, abubuwan da bayin Jehobah suke yi za su iya sa mutane su girmama Jehobah ko kuma su yi watsi da shi. A zamanin Ezekiyel, da yake Yahudawa suna bauta wa Jehobah, al’ummai sun san su da sunan Jehobah. (Ezek. 36:19-23) Hakazalika a yau, mutane sun san mu da sunan Jehobah. Saboda haka, idan muka bi ƙa’idodinsa, za mu sa a ɗaukaka shi.

Idan muka yi lalata za mu ɓata sunan Allah mai tsarki. Manzo Bitrus ya shawarci Kiristoci cewa: “Kamar ’ya’yan biyayya, ba za ku daidaita kanku bisa sha’awoyinku na dā a zamanin jahilcinku ba: amma yadda shi wanda ya kira ku mai-tsarki ne, ku kuma ku zama masu-tsarki cikin dukan tasarrufi; domin an rubuta, Ku za ku zama masu-tsarki; gama ni mai-tsarki ne.” (1 Bit. 1:14-16) Hali mai kyau yana sa a ɗaukaka sunan Allah.

Idan wani Mashaidin Jehobah ya aikata laifi, wataƙila abokansa da kuma wasu za su iya sanin zunubin da ya yi. Yi wa mutum yankan zumunci yana nuna cewa Jehobah yana da mutane masu tsabta da suke bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don su kasance da hali mai kyau. Wani mutum ya taɓa zuwa Majami’ar Mulki a ƙasar Siwizalan kuma ya ce yana so ya zama Mashaidin Jehobah. Me ya sa? An yi wa ’yar’uwarsa yankan zumunci don ta yi fasiƙanci. Ya ce yana so ya yi tarayya da ƙungiyar da “ba ta amincewa da mummunar ɗabi’a.”

Yankan zumunci yana kāre ikilisiyar Kirista daga ɗabi’u marasa kyau. Manzo Bulus ya gargaɗi ’yan’uwa a ikilisiyar Korinti cewa bai kamata su riƙa tarayya da waɗanda suke yin laifi da gangan ba. Ya kwatanta halin waɗannan mutanen da yisti da yake sa ƙullu ya kumbura. Bulus ya ce: ‘Yisti ƙanƙani ya kan gama dukan curi.’ Bayan haka, sai ya gaya musu su: “Fitar da mugun nan daga cikinku.”—1 Kor. 5:6, 11-13.

Wataƙila wannan “mugun” mutum da Bulus ya yi maganarsa ya yi fasiƙanci kuma ya ƙi tuba. Har ma wasu a cikin ikilisiya sun soma da’awa cewa abin da ya yi ba laifi ba. (1 Kor. 5:1, 2) Idan ba a ɗauki mataki a kan babban zunubin da ya yi ba, wasu za su soma yin koyi da lalata da ake yi a birnin Korinti. Idan aka ƙyale masu yin laifi da gangan su ci gaba da kasancewa a ikilisiya, ’yan’uwa ba za su ɗauki ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da muhimmanci ba. (M. Wa. 8:11) Ƙari ga haka, masu zunubi da suka ƙi tuba za su zama kamar ‘ɓoyayyun’ duwatsu da za su iya sa ’yan’uwa tuntuɓe, wato, su daina bauta wa Jehobah.—Yahu. 4, 12.

Yankan zumunci zai iya taimaka wa wanda ya aikata babban zunubi ya gane kurensa. Yesu ya taɓa yin magana game da wani matashi da ya bar gidan Ubansa ya tafi wani wuri kuma ya ɓarnatar da dukiyarsa wurin masha’a. Ɗa mubazzari ya fahimci cewa yin rayuwa ba tare da bin ja-gorar mahaifinsa ba bai da wani amfani ko kaɗan. Daga baya, yaron ya gane kurensa kuma ya tuba sai ya dawo gida. (Luk. 15:11-24) Kwatancin nan da Yesu ya yi na yadda uban ya yi farin ciki don yaron ya tuba ya taimaka mana mu fahimci halin Jehobah. Allah ya ce: “Ba ni da wani jin daɗi cikin mutuwar mugu ba, gwamma dai shi mugun shi juyo ga barin hanyarsa shi yi rai.”—Ezek. 33:11.

Hakazalika, waɗanda aka yi musu yankan zumunci kuma suka rabu da ikilisiya za su iya gane kuskurensu kuma su fahimci abin da suka yi hasararsa. Sakamakon zunubin da suka yi da kuma tunanin yadda suka ji daɗin kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma tarayya da ’yan’uwa zai iya motsa su su dawo cikin hankalinsu.

 Ƙauna da kuma ƙarfin hali suna da muhimmanci wajen taimaka wa waɗannan. Marubucin zabura Dawuda ya ce: “Bari mai-adalci shi buga ni, alheri ke nan; Shi tsauta mani, za ya zama kamar mai a kai.” (Zab. 141:5) Alal misali: A ce wani mai tsere ya faɗi kuma ya goce ƙafarsa. Hakan zai hana shi yawo. Ya san cewa idan bai yarda likita ya taimaka masa ba, ƙafar za ta iya kumbura kuma ta soma ruɓewa. Saboda da haka, ya amince likita ya taimaka, ko da yake zai ji zafi yayin da likitan yake saita ƙafar, amma ya san cewa ƙafar za ta warke da shigewar lokaci. Hakazalika, Dawuda ya fahimta cewa wajibi ne mai adalci ya yi masa horo don ya amfana.

A yawancin lokaci, yankan zumunci yana iya sa mai zunubin ya fahimci kuskurensa. Bayan shekara goma, ɗan Julian da aka ambata a farkon wannan talifin ya gyara halinsa kuma ya dawo cikin ikilisiya, yanzu shi dattijo ne. Ya ce: “Da aka min yankan zumunci sai na soma shan wahala sakamakon irin rayuwar banza da na yi. Wannan horon ya taimaka mini.”—Ibran. 12:7-11.

YADDA YA KAMATA A BI DA WAƊANDA AKA YI MUSU YANKAN ZUMUNCI

Hakika, yankan zumunci yakan ɓata dangantakar mutum da Jehobah, amma bai kamata hakan ya sa mai zunubin ƙin dawowa ba. Dukanmu muna da hakkin tabbata cewa yankan zumuncin ya cim ma sakamako mai kyau.

Ana ɗaukan matakai don taimaka wa waɗanda suka tuba su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah

Dattawa ne suke da hakkin gaya wa mai zunubin da ya ƙi tuba cewa an yi masa yankan zumunci kuma ya kamata su yi hakan da ƙauna kamar yadda Jehobah yake yi. Sa’ad da suke gaya wa mai zunubin shawarar da suka tsai da, ya kamata su gaya masa dalla-dalla matakan da zai ɗauka don a dawo da shi cikin ikilisiya. Dattawa za su iya ziyarar waɗanda suka nuna cewa sun tuba loto-loto don su tuna musu matakan da za su ɗauka don su sake ƙulla dangantaka da Jehobah. *

Mambobin iyali za su iya nuna ƙauna ga ’yan’uwa a ikilisiya da kuma wanda aka yi masa yankan zumunci ta wajen amincewa da shawarar da dattawa suka tsai da. Julian da aka ambata ɗazun ya ce: “Ko da yake ɗana ne, amma halinsa ya sa mun raba dangantaka da shi.”

Dukan ’yan’uwa a cikin ikilisiya suna nuna ƙauna ta wajen daina cuɗanya da wanda aka yi masa yankan zumunci. (1 Kor. 5:11; 2 Yoh. 10, 11) Ta hakan, suna tabbatar da cewa horon da Jehobah ya yi wa mai zunubin ta wurin dattawa ya dace. Ƙari ga haka, ’yan’uwa a ikilisiya za su iya ƙarfafa da kuma tallafa wa iyalin wanda aka yi masa yankan zumunci da yake sun sha wahala sosai don kada su ɗauka cewa su ma an yi watsi da su.—Rom. 12:13, 15.

Julian ya kammala cewa: “Yankan zumunci tsari ne mai kyau da yake taimaka mana mu bi ƙa’idodin Jehobah. Ko da yake da farko yakan sa baƙin ciki, amma yana haifar da sakamako mai kyau daga baya. Da a ce na ƙyale ɗanmu ya ci gaba da yin halin banza, da bai dawo cikin hankalinsa ba.”

^ sakin layi na 24 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 1991, shafuffuka 21-23 a Turanci.