Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 TARIHI

Albarka a Lokacin Zaman Lafiya da Lokacin Wahala

Albarka a Lokacin Zaman Lafiya da Lokacin Wahala

AN HAIFE ni a watan Maris na shekara ta 1930, a ƙauyen Namkumba kusa da birnin Lilongwe, a ƙasar da ake kira Malawi a yanzu. Iyayena da wasu dangina da abokaina Shaidun Jehobah ne. Na yi baftisma a shekara ta 1942 a wani kyakkyawan kogi da ke ƙauyenmu. Bayan da na yi baftisma, na yi fiye da shekaru 70 ina ƙoƙarin bin shawarar da Bulus ya ba wa Timothawus cewa ya yi wa’azin bishara da ƙwazo “ko da dama, ko ba dama,” wato a lokacin zaman lafiya da lokacin wahala.—2 Tim. 4:2.

Lokacin da Ɗan’uwa Nathan H. Knorr da kuma Milton G. Henschel suka soma zuwa ƙasar Malawi a farkon shekara ta 1948 ne ya sa na soma tunanin yin hidima ta cikakken lokaci. Ba na manta da kalamai masu ban ƙarfafa na waɗannan wakilai da suka zo daga hedkwata na Shaidun Jehobah a birnin Brooklyn na jihar New York. Mu wajen 6,000 ne muka tsaya a wani fili cike da laƙa kuma muka saurari jawabin Ɗan’uwa Knorr mai jigo “Permanent Governor of All Nations,” (Gwamna na Dindindin ga Dukan Al’ummai).

Na haɗu da wata ’yar’uwa mai hankali mai suna Lidasi wadda iyayenta Shaidun Jehobah ne kuma tana da maƙasudin yin hidima ta cikakken lokaci. Mun yi aure a shekara ta 1950 kuma daga lokacin zuwa shekara ta 1953, Allah ya ba mu ’ya’ya biyu. Duk da nawayar renon ’ya’yanmu, yanayin ya ba ni damar yin hidimar majagaba na kullum. Shekaru biyu bayan haka, sai aka tura ni hidimar majagaba na musamman.

Ba da daɗewa ba bayan hakan, na sami gatan zama mai kula da da’ira, ina ziyartar ikilisiyoyi dabam-dabam. Matata ta taimaka mini sosai, kuma hakan ya sa na biya bukatunmu na zahiri da na ibada. * Amma mun fi so dukanmu mu yi hidima ta cikakken lokaci. Mun yi shiri sosai kuma da taimakon ’ya’yanmu biyar, matata ta soma hidima ta cikakken a shekara ta 1960.

Manyan taro sun ƙarfafa mu mu fuskanci tsanantawa da ta biyo baya

Mun ji daɗi a wannan lokacin zaman lafiya yayin da muke yi wa ’yan’uwanmu hidima a ikilisiyoyi dabam-dabam. Muna ziyarar ikilisiyoyi daga gangaren duwatsun Mulanje masu kyan gani zuwa kudancin ƙasar, a bakin tafkin Malawi. Wannan tafkin ya zagaya kusan dukan gabashin ƙasar. Mun shaida yadda masu shela da ikilisiyoyi suka ƙaru a da’irorin da muka yi hidima.

A shekara ta 1962, mun halarci taron gunduma mai jigo “Courageous Ministers,” (Masu Hidima da Ƙarfin Zuciya). A duk lokacin da na tuna da waɗannan taron, na ga cewa sun shirya mu sosai  a ƙasar Malawi don mu jimre wahala da muka fuskanta daga baya. A shekarar da ta biyo baya, Ɗan’uwa Henschel ya ziyarci ƙasar. Aka yi wani taron gunduma na musamman a birnin Blantyre kuma mutane wajen 10,000 ne suka halarta. Wannan taron ya ƙarfafa mu sosai don matsalolin da muka fuskanta daga baya.

LOKACIN WAHALA

Shaidun Jehobah sun fuskanci tsanantawa sosai a shekara ta 1964 don sun ƙi saka hannu a harkokin siyasa. An halaka Majami’un Mulki sama da ɗari da kuma gidajen ’yan’uwa fiye da 1,000 a wannan lokacin tsanantawar. Amma Allah ya sa mun ci gaba da hidimarmu na kula da da’ira har zuwa lokacin da gwamnatin ƙasar ta hana aikin Shaidun Jehobah a shekara ta 1967. An rufe ofishin Shaidun Jehobah da ke Blantyre kuma aka kori masu wa’azi da suka zo daga ƙasashen waje, kuma aka jefa Shaidun Jehovah da yawa a cikin kurkuku, har da ni da matata. Bayan an sake mu, muka ci gaba da hidimar kula da da’ira a ɓoye.

Wata rana a watan Oktoba na shekara ta 1972, wasu ’yan ƙungiyar siyasa mai tawaye da gwamnati da ake kira Malawi Youth League (Ƙungiyar Matasan Malawi) sun shirya su zo gidanmu. Amma wani daga cikinsu ya same ni da wuri kuma ya gaya mini cewa in ɓoye domin suna so su kashe ni. Na gaya wa matata da yarana su ɓoye a cikin itatuwan ayaba da ke kusa da gidanmu. Sai na hau wani babban itacen mangwaro. Daga inda nake, ina kallonsu yayin da suka lalatar da gidanmu da kuma dukan kayayyakinmu gaba ɗaya.

Yayin da ake daɗa tsananta mana a ƙasar Malawi, dubban Shaidun Jehobah suka bar ƙasar. Ni da iyalina mun zauna a sansanin ’yan gudun hijira da ke yammancin ƙasar Mozambique har zuwa watan Yuni na shekara ta 1974. A wannan lokacin ne aka ce ni da matata mu yi hidimar majagaba na musamman a garin Dómue da ke Mozambique, kusa da iyakar ƙasar Malawi. Mun ci gaba da yin hidimar majagaba ta musamman har zuwa lokacin da ƙasar Mozambique ta sami ’yanci kai daga ƙasar Portugal a shekara ta 1975. A wannan shekarar ce aka kore mu da wasu Shaidu daga ƙasar zuwa ƙasar Malawi inda ake tsananta wa Shaidun Jehobah.

Sa’ad da muka isa ƙasar Malawi, an ce in soma ziyartar ikilisiyoyin da ke birnin Lilongwe. Duk da tsanantawa da wahala da muka fuskanta, adadin ikilisiyoyi ya ƙaru a da’irorin da muka yi hidima.

YADDA JEHOBAH YA TAIMAKA MANA

Wata rana, mun ziyarci wani ƙauye, amma a lokacin, ana taron ’yan siyasa. Sa’ad da wasu ’yan siyasan suka lura cewa mu Shaidun Jehobah ne, sai suka tilasta mana mu zauna tare da wasu ’yan ƙungiyar siyasa da ake kira Malawi Young Pioneers. Mun yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka mana a wannan mawuyacin hali. Bayan taron, sai suka  soma dūkan mu. Wata tsohuwa ta zo a guje ta ce: “Don Allah ku bar waɗannan mutanen! Wannan mutumin ɗan yayana ne. Ku bar shi ya yi tafiyarsa!” Sai wanda ya ja-goranci taron ya ce: “Ku bar su su tafi!” Ba mu san abin da ya sa matan nan ta ɗauki wannan matakin ba, da yake ba mu san ta ba. A ganinmu dai, Jehobah ne ya amsa addu’armu.

Katin jam’iyyar siyasa

A shekara ta 1981, mun sake haɗuwa da wasu ’yan ƙungiyar Malawi Young Pioneers. Sun ƙwace kekunanmu da kayayyakinmu da littattafanmu da kuma fayil-fayil da ke ɗauke da bayanai game da ikilisiyoyi da ke da’irar. Mun gudu zuwa gidan wani dattijo. Mun sake yin addu’a ga Jehobah don yanayin. Mun damu ƙwarai don bayanan da ke cikin fayil da suka ƙwace daga hannunmu. Yayin da ’yan ƙungiyar suka buɗe fayil ɗin, sai suka ga wasiƙu da aka aika mini daga wurare dabam-dabam na ƙasar Malawi. Hakan ya tsoratar da su don sun ɗauka cewa ni wani babban ma’aikacin gwamnati ne. Sai suka mai da abubuwan da suka ƙwace ga dattawan ikilisiya da ke garin. Ba abin da suka ɗauka daga ciki.

A wani lokaci kuma sa’ad da muke haye kogi a cikin kwalekwale, sai mai kwalekwalen ya soma cajin dukan fasinjojin don ya tabbata cewa suna da katin jam’iyyar siyasa da yake shi ne ciyaman na yankin. Yayin da yake zuwa kusa da mu, sai ya gano wani ɓarawo da hukuma take nema. Hakan ya ta da hayaniya sosai kuma ya sa aka daina binciken. A wannan karon ma, mun tabbata cewa Jehobah ne ya taimaka mana.

AN KAMA NI KUMA AKA JEFA NI A KURKUKU

A watan Fabrairu na shekara ta 1984, sa’ad da nake zuwa Lilongwe don in ba da rahotanni da za a kai ofishin Shaidun Jehobah na ƙasar Zambiya, sai wani ɗan sanda ya tare ni kuma ya caje jakata. Ya ga wasu littattafai a cikin jakar sai ya kai ni ofishin ’yan sanda kuma ya soma dūka na. Sai ya ɗaure ni da igiya kuma ya saka ni a cikin wani ɗaki tare da wasu fursunoni da aka kama su da kayan sata.

Washegari, shugaban ’yan sandan ya kai ni wani ɗaki sai ya yi rubutu a takarda cewa: “Ni Trophim R. Nsomba, ina so a sake ni don na daina zama Mashaidin Jehobah.” Sai na ce: “Na fi so in kasance a ɗaure, har ma in mutu, maimakon in daina zama Mashaidin Jehobah.” Na ƙi in saka hannu a takardar. Hakan ya ɓata ran shugaban ’yan sandan sai ya buga teburi da hannunsa da ƙarfi har hakan ya sa wani ɗan sanda ya zo a guje don ya ga abin da ke faruwa. Sai shugaban ya ce masa: “Wannan mutumin ya ƙi ya saka hannu a takarda cewa ya daina wa’azi. To bari ya sa hannu cewa shi Mashaidin Jehobah ne kuma mu kai shi kurkuku a Lilongwe.” Matata ba ta da masaniya game da abubuwan da ke faruwa da ni. Amma wasu ’yan’uwa sun gaya mata abin da ya faru bayan kwana huɗu.

An bi da ni cikin mutunci sa’ad da nake ofishin ’yan sanda a Lilongwe. Shugaban ’yan sandan ya ce: “Ga shinkafa ka ci da yake an ɗaure ka don wa’azin bishara da kake yi. Sauran mutanen da ke nan ɓarayi ne.” Daga nan sai ya tura ni zuwa gidan yari da ke Kachere inda na yi wata biyar a ɗaure.

 Gandiroba na gidan yarin ya yi farin ciki ƙwarai da zuwana don yana so in zama “fasto” a gidan yarin. Ya cire fasto da yake hidima a lokacin kuma ya ce masa: “Ba na so ka ci gaba da koyar da mutane kalmar Allah a nan, don an ɗaure ka ne don ka saci kuɗin coci.” Don haka, aka ce in riƙa koyar da Littafi Mai Tsarki a taron da ake yi kowane mako da fursunonin.

Daga baya, abubuwa sun yi muni. Ma’aikatan fursuna sun yi mini tambayoyi don suna so su san yawan Shaidun Jehobah da ke ƙasar Malawi. Ban ba su amsa ba, don haka sun yi mini dūka har na sūma. Daga baya, suka tambaye ni inda hedkwatarmu take. Sai na ce, “Kun yi tambaya mai sauƙi kuma zan ba ku amsar.”’Yan sandan sun yi farin ciki kuma suka kunna rakoda don su ɗauki muryata. Na yi musu bayani cewa an kwatanta hedkwatar Shaidun Jehobah a cikin Littafi Mai Tsarki. Sun yi mamaki kuma suka ce, “A ina ne a cikin Littafi Mai Tsarki?”

Sai na ce: “A Littafin Ishaya 43:12.” Sun buɗe Littafi Mai Tsarki kuma suka karanta ayar a hankali: “Ku ne shaiduna, in ji Ubangiji, ni ne Allah kuwa.” Sun karanta wannan ayar sau uku. Sai suka tambaye ni: “Ta yaya ne hedkwatar Shaidun Jehobah zai kasance a cikin Littafi Mai Tsarki amma ba Amirka ba?” Sai na ce musu: “Shaidun Jehobah a Amirka ma sun san cewa wannan ayar tana kwatanta hedkwatarmu ne.” Da yake ban gaya musu abin da suke so su ji ba, sai suka kai ni gidan yari da ke Dzaleka a arewacin Lilongwe.

ALBARKA A LOKACIN WAHALA

A watan Yuli na shekara ta 1984 ne aka saka ni a gidan yarin da ke Dzaleka, inda na haɗu da Shaidu guda 81 da aka ɗaure a wurin. A wajen, an haɗa fursunoni guda 300 a wani wuri mai cunkoso kuma suna kwana a kasa. Da sannu sannu, mu da muke Shaidun Jehobah mun ware kanmu kuma mun raɓa kanmu zuwa ƙananan rukunoni don mu riƙa tattauna wata aya daga Littafi Mai Tsarki da wani daga cikinmu ya zaɓa. Washegari kuma wani ɗan’uwa dabam ne zai zaɓi ayar da za mu tattauna. Hakan ya ƙarfafa mu sosai.

Gandiroban gidan yarin ya ware mu daga sauran fursunonin. Wani ma’aikacin gidan yarin ya ce mana a ɓoye cewa: “Ba wai gwamnati ta ƙi jininku ba. Amma mun saka ku a kurkuku ne saboda dalilai biyu: Na ɗaya, gwamnati ba ta son ’yan ƙungiyar Young Pioneers su kashe ku. Na biyu kuma shi ne, don kuna yin wa’azi cewa za a yi wani yaƙi, don haka, gwamnati tana tsoro cewa za ta rasa sojojinta a yaƙin.”

Ana tafiya da ’yan’uwa bayan an yanke musu hukunci

An kai dukanmu kotu a watan Oktoba na shekara ta 1984. A nan, an yanke wa kowannenmu hukuncin ɗaurin shekara biyu. An haɗa mu da waɗanda ba Shaidu ba kamar yadda aka yi a dā. Amma gandiroban gidan yarin ya yi sanarwa cewa: “Shaidun Jehobah ba sa shan taba. Saboda haka, ku ma’aikata, kada ku matsa musu ta wajen ce su ba ku sigari kuma kada ku ce su kawo muku garwashin wuta don kunna sigari. Su bayin Allah ne!  Ku riƙa ba wa dukan Shaidun Jehobah abinci sau biyu a rana, da yake ba su yi laifi ba, amma an ɗaure su ne don imaninsu.”

Mun amfana sosai a wasu hanyoyi ma don halinmu mai kyau. Ba a barin fursunoni su yi yawo daddare ko kuma sa’ad da ake yin ruwan sama. Amma ana barinmu mu fita a duk lokacin da muke so mu yi hakan. Sun san cewa ba za mu gudu ba. Akwai wani lokaci da wani ma’aikaci da ke lura da mu ya yi ciwo sa’ad da muke yin aiki a gona, mun ɗauke shi muka dawo da shi cikin gidan yarin don a yi masa jinya. Ma’aikatan gidan yarin sun san cewa mu masu riƙe amana ne. Jehobah ya albarkace mu don masu tsananta mana sun ɗaukaka sunansa saboda halin kirki da muke da shi.—1 Bit. 2:12. *

MUN SHIGA LOKACIN ZAMAN LAFIYA

An sake ni daga kurkukun Dzaleka a ranar 11 ga watan Mayu na shekara ta 1985. Na yi farin ciki sosai don na sake haɗuwa da iyalina. Mun gode wa Jehobah don yadda ya taimaka mana mu kasance da aminci a wannan mawuyacin lokaci. Yanayinmu yana nan kamar na manzo Bulus sa’ad da ya rubuta cewa: “’Yan’uwa, ba mu so ku rasa sani zancen ƙuncinmu da ya same mu . . . har ranmu muka fid da zuciya a ciki, labudda kuwa, mu da kanmu muna da hukuncin mutuwa a cikin ranmu, domin kada mu dogara ga kanmu, amma ga Allah wanda ke ta da matattu, wanda ya tsame mu daga cikin mutuwa mai-girma haka.”—2 Kor. 1:8-10.

Hakika, a wani lokaci, mun ɗauka cewa ba za mu tsira ba. Amma mun roƙi Jehobah a kowane lokaci ya sa mu yi ƙarfin zuciya kuma ya ba mu hikima da zai taimaka mana mu kasance da tawali’u don mu ci gaba da ɗaukaka sunansa.

Jehobah ya albarkace mu a hidimarsa a lokacin zaman lafiya da kuma a lokacin wahala. Yanzu, muna farin cikin ganin ofishin Shaidun Jehobah a Linlongwe, da aka gama ginawa a shekara ta 2000. Ƙari ga haka, yanzu muna da sababbin Majami’un Mulki sama da 1,000 a ƙasar Malawi. Waɗannan abubuwa da Jehobah ya yi sun ƙarfafa ni da Lidasi sosai har ya sa mun ji kamar mu zuba ruwa a ƙasa mu sha. *

^ sakin layi na 7 Yanzu ba a gayyatar ’yan’uwa masu yara ƙanana su yi hidimar kula da da’ira.

^ sakin layi na 30 Don samun cikakken bayani game da tsanantawa da Shaidun Jehobah suka fuskanta a ƙasar Malawi, ka duba littafin nan 1999 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 171-223.

^ sakin layi na 34 Ɗan’uwa Nsomba ya mutu yayin da ake shirin wallafa wannan labarin. Ya yi shekara 83 a duniya.