Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Why We Observe the Lord’s Evening Meal

Why We Observe the Lord’s Evening Meal

Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.” —1 KOR. 11:24, Littafi Mai Tsarki.

1, 2. Mene ne Yesu ya yi a daren 14 ga Nisan ta shekara ta 33? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

FARIN wata yana haskaka Urushalima a wannan daren 14 ga Nisan ta shekara ta 33 daga zamanin Yesu. Yesu da manzanninsa sun gama Idin Ƙetarewa, wato bikin tuna da yadda aka ’yantar da Isra’ila daga bauta a ƙasar Masar shekaru 1,500 da suka shige. A wannan lokacin da Yesu yake tare da amintattun manzanninsa guda 11 ne ya gabatar da wani tsarin cin abinci mai cike da ma’ana. Wannan tsarin ya shafi mutuwar da Yesu zai yi kafin ƙarshen ranar * kuma za a riƙa yin irin wannan taron kowace shekara don tuna da mutuwarsa.—Mat. 26:1, 2.

2 Yesu ya yi addu’a sai ya ba wa manzanninsa gurasa marar yisti, ya ce: “Ku karɓa, ku ci.” Ya ɗauki ƙoƙon ruwan inabi, ya sake yin addu’a, sai ya ce: “Dukanku ku sha daga cikinsa.” (Mat. 26:26, 27) Waɗannan abubuwa ne kawai Yesu ya ba wa manzanninsa, amma akwai abubuwa da dama da zai gaya musu a wannan dare mai muhimmanci.

3. Waɗanne tambayoyi ne za a ba da amsarsu a wannan talifin?

 3 Ta hakan ne Yesu ya kafa taron tuna mutuwarsa, wanda kuma ake kira “Jibin Ubangiji.” (1 Kor. 11:20) Wasu za su iya yin waɗannan tambayoyin: Me ya sa muke taron Tuna Mutuwar Yesu? Mene ne gurasar da ruwan inabin suke wakilta? Ta yaya za mu yi shiri don taron Tuna Mutuwar Yesu? Wane ne ya kamata ya ci gurasar kuma ya sha ruwan inabin? Yaya ya kamata Kiristoci su ɗauki begen da suke da shi bisa ga Littafi Mai Tsarki?

ABIN DA YA SA MUKE TARON TUNA MUTUWAR YESU

4. Mene ne mutuwar Yesu ta tanadar mana?

4 Da yake mu ’ya’yan Adamu ne, mun gāji zunubi da mutuwa. (Rom. 5:12) Babu ɗan Adam ajizi da zai iya fansar ransa ko kuma na wasu. (Zab. 49:6-9) Yesu ne kaɗai zai iya ba da fansar da Allah zai amince da ita, kuma ya yi hakan sa’ad da ya sadaukar da kamiltaccen ransa. Bayan ya tashi daga matattu, ya koma sama kuma ya bayyana a gaban Allah, hakan ya sa mun sami ceto daga zunubi da mutuwa da kuma damar samun rai na har abada.—Rom. 6:23; 1 Kor. 15:21, 22.

5. (a) Ta yaya muka san cewa Allah da Kristi suna ƙaunar ’yan Adam? (b) Me ya sa ya kamata mu halarci taron Tuna Mutuwar Yesu?

5 Ta wajen tanadar da fansa, Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar ’yan Adam. (Yoh. 3:16) Yesu ya sadaukar da ransa kuma hakan ya nuna cewa yana ƙaunarmu. Wannan ba abin mamaki ba ne don sa’ad da Yesu yake sama a matsayin “gwanin mai-aiki,” yana ƙaunar “’yan Adam”! (Mis. 8:30, 31) Ya kamata mu nuna godiya ga Allah da kuma Ɗansa ta halartan taron Tuna Mutuwar Yesu kuma mu bi wannan umurnin da ke cewa: “Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.”—1 Kor. 11:23-25, LMT.

MENE NE GURASAR DA RUWAN INABIN SUKE WAKILTA?

6. Yaya ya kamata mu ɗauki gurasa da ruwan inabi na taron Tuna Mutuwar Yesu?

6 Sa’ad da Yesu ya gudanar da taron tuna da mutuwarsa, bai mai da jikinsa gurasa ba kuma bai mai da jininsa ruwan inabi ba. A maimakon haka, ya ce game da gurasar: “Wannan yana nufin jikina.” Game da ruwan inabin kuma, ya ce: “Wannan yana nufin jinina na alkawari, wanda za a zubar a madadin mutane da yawa.” (Mar. 14:22-24, NW) A bayane yake cewa gurasar da ruwan inabin alamu ne.

7. Mene ne gurasar da ake amfani da shi a taron Tuna Mutuwar Yesu yake wakilta?

7 A wannan lokacin biki mai muhimmanci na shekara ta talatin da uku, Yesu ya yi amfani da gurasa marar yisti da ya rage bayan Idin Ƙetarewa. (Fit. 12:8) A wani lokaci, Littafi Mai Tsarki, yakan kwatanta aibi ko zunubi da yisti. (Mat. 16:6, 11, 12; Luk. 12:1) Saboda haka, ya dace da Yesu ya yi amfani da gurasa marar yisti don ya kwatanta jikinsa marar zunubi. (Ibran. 7:26) Irin wannan gurasar ne ake amfani da shi a taron Tuna Mutuwar Yesu.

8. Mene ne ruwan inabi da ake amfani da shi a taron Tuna Mutuwar Yesu yake wakilta?

8 Ruwan inabin da Yesu ya yi amfani da shi a ranar 14 ga Nisan na shekara ta 33 yana wakiltar jininsa, hakan ma yake da ruwan inabin da ake amfani da shi a yau a taron Tuna Mutuwar Yesu. A Golgotha, bayan garin Urushalima ne aka zubar da jininsa don “gafarar zunubai.” (Mat. 26:28; 27:33) Da yake gurasa da ruwan inabi suna wakiltar hadayar da Yesu ya miƙa a madadin ’yan Adam masu biyayya kuma muna godiya domin wannan ƙauna da ya nuna mana, ya dace mu shirya da kyau don taron Tuna Mutuwar Yesu da ake yi a kowace shekara.

 YADDA ZA MU YI SHIRI

9. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa yin karatun Littafi Mai Tsarki da aka tsara don Tuna da Mutuwar Yesu? (b) Yaya kake ji game da fansar?

9 Ta wajen bin tsarin karatun Littafi Mai Tsarki don Tuna Mutuwar Yesu da ke cikin ƙasidar Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana, muna iya yin bimbini a kan abin da Yesu ya yi a daren da ya mutu. Hakan zai taimaka mana mu shirya zuciyarmu don taron Tuna Mutuwar Yesu. * Wata ’yar’uwa ta ce: “Muna ɗokin halartar taron Tuna Mutuwar Yesu. Kowace shekara taron yana ƙara kasancewa da muhimmanci a gare mu. Na tuna sa’ad da ake jana’izar mahaifina . . . , mutuwarsa ya sa na fahimci muhimmancin fansar. . . . Hakika, na san dukan nassosin, kuma zan iya bayyana su! Amma lokacin da mahaifina ya mutu ne na fahimci muhimmancin fansar da kuma yadda za ta amfane mu a nan gaba.” Hakika, sa’ad da muke shiri don taron Tuna Mutuwar Yesu, ya kamata mu yi bimbini a kan yadda hadayar Yesu ya ’yantar da mu daga zunubi da kuma mutuwa.

Ka yi amfani da abubuwan da aka tanadar wajen yin shirin don taron Tuna Mutuwar Yesu (Ka duba sakin layi na 9)

10. Ta yaya yin shiri don taron Tuna Mutuwar Yesu ya kamata ya shafi hidimarmu?

10 Wata hanya kuma da za mu iya yin shiri don taron Tuna Mutuwar Yesu shi ne ta ƙara ƙwazo a wa’azi, wataƙila ta wajen yin hidimar majagaba na ɗan lokaci sa’ad da lokacin ya kusa. Idan muka gayyaci ɗaliban Littafi Mai Tsarki da kuma wasu zuwa taron Tuna Mutuwar Yesu, za mu yi marmarin yin magana game da Allah da Ɗansa, da kuma albarkar da waɗanda suke faranta wa Jehobah rai za su samu.—Zab. 148:12, 13.

11. Ta yaya wasu Korintiyawa suka ci gurasar da kuma sha ruwan inabin a hanyar da ba ta dace ba?

11 Yayin da kake shiri don taron Tuna Mutuwar Yesu, ka yi la’akari da abin da manzo Bulus ya rubuta ga Kiristoci da ke ikilisiyar Korinti. (Karanta 1 Korintiyawa 11:27-34.) Bulus ya ce duk wanda ya ci gurasar kuma ya sha ruwan inabin a hanyar da ba ta dace ba zai “zama da laifi cikin jikin Ubangiji [Yesu Kristi] da jininsa.” Saboda da haka, ya kamata wanda aka shafa shi da ruhu mai tsarki ya “auna kansa” kafin ya ci gurasar da kuma sha ruwan inabin. In ba haka ba, “shari’a yake ci, ya sha wa kansa.” Wannan dalilin  ne ya sa Korintiyawa da yawa suka zama ‘raunana, masu cuta’ kuma wasu kaɗan sun yi “barci,” wato sun ɓata dangantakarsu da Allah. Wataƙila, wasu sun yi ciye-ciye da shaye-shaye ainun kafin ko kuma a lokacin taron Tuna Mutuwar Yesu shi ya sa ba sa cikin hayyacinsu kuma ba su natsu ba. Saboda haka, Allah bai amince da su ba don sun ci gurasar kuma sun sha ruwan inabin a hanyar da ba ta dace ba.

12. (a) Mene ne Bulus ya kwatanta taron Tuna Mutuwar Yesu da shi, kuma wane gargaɗi ne ya yi wa masu cin gurasar da kuma shan ruwan inabin? (b) Mene ne ya kamata mai cin gurasar da kuma shan ruwan inabin ya yi idan ya yi zunubi mai tsanani?

12 Bulus ya kwatanta taron Tuna Mutuwar Yesu da cin abinci tare da ’yan’uwa kuma ya gargaɗi Korintiyawa cewa: “Ba ku da iko ku sha ƙoƙon Ubangiji duk da na aljanu ba: ba ku da iko ku tara ci daga table na Ubangiji, da na aljanu ba.” (1 Kor. 10:16-21) Idan wanda yake cin gurasar da kuma shan ruwan inabin a lokacin taron Tuna Mutuwar Yesu ya yi zunubi mai tsanani, ya kamata ya nemi taimakon dattawa. (Karanta Yaƙub 5:14-16.) Idan ya “tuba,” da gaske kuma bayan haka, ya ci gaba da cin gurasar da shan ruwan inabin, hakan zai nuna cewa hadayar Yesu tana da daraja a gare shi.—Luk. 3:8.

13. Me ya sa zai yi kyau mu yi addu’a game da begen da Allah ya ba mu?

13 Yayin da muke shiri don taron Tuna Mutuwar Yesu, zai dace mu yi addu’a cikin natsuwa game da begen da muke da shi. Ba bawan Jehobah da ya yi baftisma ko kuma mabiyin Ɗansa mai aminci da zai so ya ƙi daraja hadayar Yesu ta wajen cin gurasa da kuma sha ruwan inabi a taron Tuna Mutuwar Yesu idan bai tabbata ba cewa shi shafaffe ne ba. Saboda haka, ta yaya mutum zai san ko ya dace ya ci da kuma sha ko kada ya yi hakan?

WANE NE YA KAMATA YA CI GURASAR KUMA YA SHA RUWAN INABIN?

14. Wace alaƙa ce ke tsakanin sabon alkawari da cin gurasa da kuma shan ruwan inabi a taron Tuna Mutuwar Yesu?

14 Waɗanda suke cin gurasa da kuma sha ruwan inabin a taron Tuna Mutuwar Yesu sun tabbata cewa suna cikin sabon alkawari. Yesu ya ce game da ruwan inabin: “Wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina.” (1 Kor. 11:25) Allah ya annabta ta bakin Irmiya cewa zai yi wani sabon alkawari da ya bambanta da alkawarin da ya yi da Isra’ilawa. (Karanta Irmiya 31:31-34.) Allah ya yi sabon alkawari da Isra’ila na Allah. (Gal. 6:15, 16) Hadayar Yesu ne ya tabbatar da wannan alkawari ta jinin Yesu. (Luk. 22:20) Yesu shi ne mai shiga tsakani a wannan sabon alkawarin, kuma amintattun shafaffu da aka yi wannan alkawarin da su za su je sama.—Ibran. 8:6; 9:15.

15. Su wane ne aka yi Alkawari na Mulki da su, kuma wane gata ne za su samu idan suka kasance da aminci?

15 ’Yan’uwa da suka cancanta su ci gurasa da kuma sha ruwan inabi a taron Tuna Mutuwar Yesu sun san cewa an yi Alkawari na Mulki da su. (Karanta Luka 12:32.) Mabiyan Yesu shafaffu da suka ci gaba da kasancewa da aminci a gare shi kuma suka fuskanci gwaji, za su yi mulki tare da shi a sama. (Filib. 3:10) Da yake an yi Alkawari na Mulki da su, amintattun shafaffu za su yi sarauta tare da Kristi a sama har abada. (R. Yoh. 22:5) Saboda haka, ya dace waɗannan ’yan’uwan su ci gurasa kuma su sha ruwan inabi a taron Tuna Mutuwar Yesu.

16. Ka ɗan bayyana ma’anar Romawa 8:15-17.

16 Waɗanda ruhu mai tsarki ya shaida musu ne kawai ya kamata su ci gurasa kuma su sha ruwan inabi a wannan taron. (Karanta Romawa 8:15-17.) Ka lura cewa Bulus ya yi amfani da wannan kalmar yaren Aramaic, wato “Abba,” wanda yake nufin  “Uba!” Kamar yadda yaro zai kira mahaifinsa “baba” da kuma “Uba” don yana ƙaunarsa kuma yana girmama shi. Ta ruhu mai tsarki, waɗannan sun zama “’ya’yan Allah.” Ruhun Allah ya shaida wa ruhunsu kuma hakan ya sa sun san cewa su shafaffu ’ya’yan Allah ne. Ba wai sun daina sha’awar zama a duniya ba kawai. Sun tabbata cewa za su yi sarauta tare da Yesu a Mulkin sama idan sun kasance da aminci har mutuwa. A yau, kaɗan suka rage daga cikin mabiya Kristi 144,000 da suka sami “shafewa” daga wurin Jehobah, Allah “mai-tsarki.” (1 Yoh. 2:20; R. Yoh. 14:1) Ruhu mai tsarki ne ya sa suke kira “Abba, Uba.” Babu shakka, suna moran dangantaka ta musamman da Allah!

KA ƊAUKI BEGENKA DA MUHIMMANCI

17. Wane bege ne shafaffu suke da shi, kuma yaya suka ɗauki wannan begen?

17 Idan kai shafaffen Kirista ne, begen zuwa sama batu mai muhimmanci ne da za ka riƙa yin addu’a a kai. Sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya yi maganar ‘ɗaura aure’ na Ango da ke sama, wato Yesu Kristi, kana gani kanka cikin waɗanda za su zama ‘amaryar’ Kristi. (2 Kor. 11:2; Yoh. 3:27-29; R. Yoh. 21:2, 9-14) Sa’ad da Allah ya bayyana ƙaunarsa a cikin Littafi Mai Tsarki ga shafaffun ’ya’yansa, sai ka ga cewa hakan ya shafe ka. Ƙari ga haka, sa’ad da Jehobah ta Kalmarsa ya ba wa shafaffun ’ya’yansa umurni, ruhu mai tsarki yana motsa ka ka bi umurnin don ka fahimci cewa batun ya shafe ka. Ruhun Allah zai shaida maka cewa za ka je sama.

18. Wane bege ne “waɗansu tumaki” suke da shi, yaya kake ji game da wannan begen?

18 A wani ɓangaren kuma, idan kana cikin “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki,” Allah ya ba ka begen zama a duniya. (R. Yoh. 7:9; Yoh. 10:16) Kana so ka yi rayuwa har abada a Aljanna, kuma kana farin cikin yin bimbini a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da rayuwa a duniya a nan gaba. Kana ɗokin lokacin da za ka yi rayuwa cikin salama tare da iyalinka da sauran mutane masu adalci. Kana marmarin lokacin da ba ƙarancin abinci da talauci da wahala da rashin lafiya da kuma mutuwa. (Zab. 37:10, 11, 29; 67:6; 72:7, 16; Isha. 33:24) Kana ɗokin marabtar waɗanda za a ta da daga matattu da begen yin rayuwa a duniya har abada. (Yoh. 5:28, 29) Babu shakka, kana farin ciki cewa kana da begen yin rayuwa a duniya! Ko da yake ba ka cin gurasar da kuma shan ruwan inabin a taron Tuna Mutuwar Yesu, amma kana halartar taron don ka nuna godiyarka ga fansar hadaya ta Yesu Kristi.

ZA KA HALARCI TARON KUWA?

19, 20. (a) Mene ne za ka yi don ka sami rai na har abada? (b) Me ya sa za ka halarci taron Tuna Mutuwar Yesu?

19 Ko da kana da begen zuwa sama ko kuma na kasancewa a duniya ne, za ka iya yin rayuwa har abada ne kawai idan ka ba da gaskiya ga Jehobah Allah da Yesu Kristi da kuma fansar. Ta wajen halartan taron Tuna Mutuwar Yesu, za ka sami zarafin yin bimbini a kan begenka da kuma yadda mutuwar Yesu take da muhimmanci a gare ka. Saboda haka, ka ƙudiri niyyar kasancewa ɗaya daga cikin miliyoyin mutane da za su halarci taron Tuna Mutuwar Yesu bayan faɗuwar ranar Jumma’a, 3 ga Afrilu, 2015, a Majami’un Mulki da kuma wasu wurare a faɗin duniya.

20 Halartan taron Tuna Mutuwar Yesu zai sa ka ƙara kasancewa da godiya ga fansar hadaya ta Yesu. Sauraron jawabin cikin natsuwa zai iya motsa ka ka nuna cewa kana ƙaunar maƙwabtanka ta wajen gaya musu abin da ka koya game da ƙaunar Jehobah da kuma nufinsa ga ’yan Adam. (Mat. 22:34-40) Saboda haka, ka yi iya ƙoƙarinka don ka kasance a taron Tuna Mutuwar Yesu.

^ sakin layi na 1 A al’adar Ibraniyawa, faɗuwar ranar yau zuwa faɗuwar ranar gobe shi ne kwana ɗaya.

^ sakin layi na 9 Ka duba ƙasidar nan, Taimako don Nazarin Kalmar Allah, sashe na 16.