Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sun Ba Da Kansu Da Yardar Rai a New York

Sun Ba Da Kansu Da Yardar Rai a New York

WASU ’yan shekaru da suka shige, Cesar da matarsa Rocio suna jin daɗin rayuwarsu a California, inda Cesar yana gyaran iyakwandishan da na’urar ɗuma ɗaki kuma matarsa tana aikin wucin gadi a ofishin likita. Suna da nasu gidan kuma ba su haifi yara ba. Amma, akwai wani abin da ya faru da ya sa suka canja tsarin rayuwarsu. Me ke nan?

A watan Oktoba na shekara ta 2009, ofishin Shaidun Jehobah da ke Amirka ya tura wa dukan ikilisiyoyin ƙasar wasiƙa cewa ana neman ƙwararru su cika fom don yin hidima a Bethel na ɗan lokaci don taimakawa da aikin faɗaɗa reshen Shaidun Jehobah da ke Wallkill, a jihar New York. Har ma an ce waɗanda shekarunsu sun shige na yin hidima a Bethel za su iya cika fom ɗin. Cesar da Rocio sun ce: “Da yake shekarunmu sun wuce na waɗanda ake gayyata, mun san cewa wannan dama ce na yin hidima a Bethel da ba za mu sake samu ba. Ba mu so wannan damar ta wuce mu ba.” Sai ma’auratan suka cika fom ɗin kuma suka aika nan da nan.

Wasu masu taimakawa da aiki a Warwick

Cesar da matarsa Rocio sun yi sama da shekara ɗaya suna jira, amma ba a gayyace su zuwa Bethel ba. Duk da haka, sun ɗauki matakin yin rayuwa mai sauƙi don su cim ma burinsu. Cesar ya ce: “Mun mai da garejinmu zuwa ɗaki don mu ba da hayar gidanmu. Sai muka ƙaura daga babban gidanmu mai ɗakuna bakwai da muka gina ’yan shekaru da suka shige kuma muka koma wani ƙaramin gida. Waɗannan canje-canje ya sa mun kasance da shirin yin hidima a Bethel idan aka gayyace mu.” Shin mene ne ya faru bayan haka? Rocio ta ce: “Bayan wata ɗaya da muka koma ƙaramin gidanmu, sai aka gayyace mu yin hidima a Bethel da ke Wallkill na ɗan lokaci. A bayyane yake cewa matakin da muka ɗauka na yin rayuwa mai sauƙi ya sa Jehobah ya albarkace mu.”

Jason da Cesar da William

SUN SAMI ALBARKA DON SADAUKARWA DA SUKA YI

Kamar Cesar da Rocio, ’yan’uwa da yawa suna yin sadaukarwa don su sa hannu a aikin gine-gine da  ake yi a Jihar New York. Da yawa a cikinsu suna aikin faɗaɗa reshe da ke Wallkill, wasu kuma sun sami gatan taimakawa a aikin gina hedkwata da ke Warwick. * Ma’aurata da yawa sun bar gidajensu da ayyukansu da wasu abubuwa don su ƙara ƙwazo a hidimarsu ga Jehobah. Shin Jehobah ya albarkace su don sadaukarwa da suka yi? Ƙwarai kuwa!

Way

Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Way, da ke gyaran wuta da matarsa Debra, da suka ba shekara 50 baya da ke zama a Kansas sun sayar da gidansu da yawancin abubuwan da suka mallaka kuma suka ƙaura zuwa Wallkill don su riƙa hidima lokaci-lokaci a Bethel. * Ko da yake yin hakan ya sa sun canja tsarin rayuwarsu, suna ganin cewa sadaukarwa da suka yi ya dace. Debra ta bayyana game da aikinta a Bethel cewa: “Wani lokaci sai in ji kamar ina cikin waɗanda ke yin gine-gine a hotunan Aljanna da ake nunawa a littattafanmu!”

Melvin da Sharon sun sayar da gidansu da kayayyakinsu a South Carolina don su taimaka da aikin da ake yi a Warwick. Ko da yake sadaukarwa da suka yi ba shi da sauƙi, ma’auratan sun ji daɗi cewa suna saka hannu a wannan aiki mai muhimmanci a tarihi. Sun ce: “Muna farin ciki sosai don mu san cewa muna yin aikin da zai amfani ƙungiyar Jehobah a faɗin duniya.”

Kenneth

Kenneth, wani magini da ya yi ritaya da matarsa Maureen da suka ba shekara 50 baya sun ƙaura daga California zuwa Warwick don su yi hidima a wurin. Kafin su ƙaura, sun gaya wa wata ’yar’uwa a ikilisiyar ta kula da gidansu kuma sun gaya wa danginsu su kula da mahaifin Kenneth da ya tsufa. Shin sadaukarwa da suka yi don su yi hidima a Bethel ya sa sun yi da-na-sani ne? Ko kaɗan! Kenneth ya ce: “Muna samun amfani sosai. Hakan yana nufin ba ma fuskantar ƙalubale ne? A’a, amma muna yin rayuwa mai ma’ana. Shawarar da muke ba wa ’yan’uwa da zuciya ɗaya ita ce, su yi irin wannan hidimar.”

YADDA SUKA SHAWO KAN ƘALUBALE

Yawancin ’yan’uwa da suka ba da kansu sun fuskanci wasu ƙalubale amma sun yi nasara. Alal misali, William da Sandra da suka ba shekara 60 baya suna jin daɗin rayuwarsu a Pennsylvania. Suna da Kamfanin ƙera kayan injin kuma mutane 17 ne suke yi musu aiki a wajen. Suna ikilisiya da suke tun suna ƙanana, kuma yawancin danginsu suna zama a yankin. Saboda haka, sa’ad da suka  sami zarafin yin hidimar lokaci-lokaci a Bethel da ke Wallkill, sun san cewa yin hakan yana nufin ban kwana da mutanen gida da kuma irin rayuwa da suka yi. William ya ce: “Babu shakka, ƙalubale mafi wuya da muka fuskanta shi ne barin gida.” Amma, bayan sun yi addu’a sosai, ma’auratan sun tsai da shawara su ƙaura, kuma ba su yi nadama ba. William ya ci gaba da cewa: “Ba za a taɓa iya gwada farin ciki da ake samu daga yin hidima tare da ’yan’uwa da ke Bethel da wani abu ba. Ni da matata Sandra ba mu taɓa yin farin ciki kamar haka ba!”

Wasu ma’aurata da suke aiki a Wallkill

An gayyaci Ricky, manajan aikin gine-gine a Hawaii, zuwa Warwick a matsayin mai hidimar lokaci-lokaci a Bethel. Matarsa Kendra tana so ya amince da gayyatar, amma suna da wata damuwa: Yaya za su yi da ɗansu Jacob, mai shekara 11? Suna tunani ko zai dace su ƙaura zuwa Jihar New York kuma ko ɗansu zai saba da yanayin wurin.

Ricky ya ce: “Abin da muka sa a kan gaba shi ne neman ikilisiya mai matasa masu dangantaka mai kyau da Jehobah. Muna son Jacob ya sami abokan kirki da yawa.” Amma ikilisiyar da suka je babu yara da yawa amma akwai masu hidima a Bethel da dama. Ricky ya ƙara da cewa: “Bayan da muka halarci taro na farko, na tambayi Jacob yadda yake ji game da sabuwar ikilisiyar, musamman da yake babu tsaransa a wurin. Sai ya ce mini, ‘Baba kada ka damu. Matasa masu hidima a Bethel ne za su zama abokaina.’”

Jacob da iyayensa suna jin dadin cudanya da masu hidima a Bethel da ke ikilisiyarsu

Hakika, matasa masu hidima a Bethel sun mai da Jacob abokinsu. Yaya hakan ya shafe shi? Ricky ya yi bayani cewa: “Wata rana, daddare da nake wucewa kusa da ɗakin ɗana, sai na ga cewa har ila wutar ɗakinsa yana kunne, na ɗauka zan kama shi yana wasan kwamfuta, amma sai na ga yana karanta Littafi Mai Tsarki! Sa’ad da na tambayi Jacob abin da yake yi, sai ya ce: ‘Ina kwaikwayon zama matashi da ya soma hidima a Bethel, kuma ina son in karance Littafi Mai Tsarki a cikin shekara ɗaya.’” Hakan ya burge Ricky da Kendra, don sun sami damar yin aiki a Warwick, ƙari ga haka, ƙaura da suka yi ya ba ɗansu damar ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah.—Mis. 22:6.

BA SU DAMU DA ABIN DA ZAI FARU BA

Luis da Dale

Babu shakka, za a gama aikin da ake yi a Wallkill da Warwick, saboda haka, waɗanda aka gayyata su taimaka da aikin sun san cewa ba su daɗe a wuraren ba. Shin waɗannan ’yan’uwa suna damuwa ainun game da inda za su je ko kuma aikin da za su yi ne? Ko kaɗan! Ra’ayinsu ɗaya ne da  na wasu ma’aurata biyu daga Florida da suka ba shekara 50 baya. John, wani manajan gine-gine da matarsa Carmen, waɗanda suka yi hidima na ɗan lokaci a Warwick sun ce: “Mun ga yadda Jehobah ya biya bukatunmu har zuwa wannan lokacin. Muna da tabbaci cewa, Jehobah bai kawo mu nan don ya yatsar da mu daga baya ba.” (Zab. 119:116) Luis, mai ƙera na’urorin kashe wuta da matarsa Quenia, sun yi hidima a Wallkill. Sun ce: “Mun riga mun shaida yadda Jehobah yake biyan bukatunmu. Ko da yake ba mu san ko ta yaya, ko a wane lokaci, ko yanayi zai yi hakan ba, muna da  tabbaci cewa zai ci gaba da kula da mu.”—Zab. 34:10; 37:25.

“ALBARKA MAI YAWAN GASKE”

John da Melvin

Yawancin ’yan’uwa da suka taimaka da aikin a New York suna da hujjoji da zai hana su yin haka. Amma, sun gwada Jehobah kamar yadda ya ce dukanmu mu yi: “Ku gwada ni, za ku gani, zan buɗe taskokin sama in zubo muku da albarka mai yawan gaske.”—Mal. 3:10, Littafi Mai Tsarki.

Shin za ka so ka gwada Jehobah kuma ya albarkace ka? Ka yi tunanin abin da za ka iya yi don ka sa hannu a wannan aiki mai muhimmanci da ake yi a New York ko kuma a gine-gine na ƙungiyar Jehobah da ake yi a wasu wurare. Ka yi addu’a a kan batun ka ga ko Jehobah ba zai albarkace ka ba.—Mar. 10:29, 30.

Gary

Dale, wani injiniyan gine-gine da matarsa Cathy, daga Alabama suna ba wa ’yan’uwa shawara su yi irin wannan hidimar. Sun ce: “Idan kana da ƙarfin zuciyar barin gida, za ka ga cewa ruhun Jehobah yana aiki.” Mene ne kake bukatar yi don ka yi wannan hidimar? Dale ya ce: “Kawai ka yi rayuwa mai sauƙi. Ba za ka taɓa yin da-na-sani ba!” Gary daga North Carolina ya yi shekara 30 a aikin gine-gine. Shi da matarsa Maureen sun ce aiki a Warwick albarka ce domin “suna haɗuwa da kuma aiki tare da ’yan’uwa maza da mata masu kirki da suka daɗe sosai suna hidima a Bethel.” Gary ya daɗa da cewa: “Hidima a Bethel tana bukatar mutum ya bi tsarin rayuwa mai sauƙi, kuma hakan shi ne irin rayuwar da ta fi kyau a wannan zamani.” Jason, ya yi aiki wa wani Kamfanin lantarki kuma shi da matarsa Jennifer sun fito ne daga Illinois. Sun ce yin aiki a Bethel da ke Wallkill yana kamar yadda rayuwa za ta kasance a sabuwar duniya. Jennifer ta ƙara cewa: “Sanin cewa Jehobah ya amince da dukan abin da kake yi da kuma cewa adashe ne don shirin da yake yi mana a nan gaba, abin farin ciki ne sosai. Jehobah zai albarkace ka fiye da yadda kake tsammani.”

^ sakin layi na 6 Ka duba littafin nan, 2014 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 12-13.

^ sakin layi na 7 Masu zuwa hidima a Bethel lokaci-lokaci suna zama a gidajen haya kuma su ne ke kula da kansu yayin da suke aiki a Bethel rana ɗaya ko fiye da hakan a mako.