Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

‘Kada Ka Ji Tsoro, Zan Taimake Ka’

‘Kada Ka Ji Tsoro, Zan Taimake Ka’

A CE kana tafiya a kan titi da dare sai ka ji sawun wani mutum yana bin ka a baya. Da ka tsaya, sai shi ma ya tsaya. Sa’ad da ka soma tafiya da sauri, sai shi ma ya soma bin ka da sauri. Sai ka ruga a guje zuwa gidan wani abokinka da ke kusa. Abokinka ya buɗe kofa kuma ya ce ka shiga ciki. Sai hankalinka ya kwanta.

Wataƙila ba ka taɓa samun kanka a cikin irin wannan yanayin ba, amma wasu abubuwa da ke ci maka tuwo a ƙwarya za su iya sa ka damuwa sosai. Alal misali, shin kana fama da wani hali marar kyau da za ka so ka daina? Kana fama da rashin aiki duk da ƙoƙarin da kake yi wajen neman aiki? Kana tsoron matsalolin da ke tattare da tsufa ko kuma wani rashin lafiya? Ko kuma wani abu dabam yana sa ka baƙin ciki?

Duk wata damuwar da kake ciki, za ka so a ce kana da abokin da za ka bayyana masa damuwarka kuma ya taimaka maka a lokacin da ya dace, ko ba haka ba? Shin kana da irin wannan abokin? Hakika, Jehobah ya zama irin wannan abokin ga Ibrahim kuma zai so ya zama abokinka kamar yadda aka ambata a littafin Ishaya 41:8-13. Ƙari ga haka, a aya ta 10 da ta 13, Jehobah ya yi wa duk wanda yake bauta masa wannan gayyatar: ‘Kada ka ji tsoro; gama ina tare da kai: kada ka yi fargaba; gama ni ne Allahnka: ni ƙarfafa ka: na taimake ka. . . . Gama ni Ubangiji Allahnka zan riƙe hannun damanka, in ce maka, kada ka ji tsoro, zan taimake ka.’

BA ZAN BAR KA BA

Waɗannan kalaman suna da ban ƙarfafa, ko ba haka ba? Ka yi ƙoƙari ka ga kanka a wannan yanayin da aka kwatanta a waɗannan ayoyin. Ayoyin ba sa nufin cewa Jehobah zai riƙe hannunka kuma ku riƙa tafiya tare, don idan ka riƙe hannun mutum kuma kuna tafiya tare, hannun hagunka ne zai riƙe hannun damarsa. Amma a nan Jehobah yana amfani ne da ‘hannun damarsa na adalci’ don ya riƙe “hannun damanka,” wato kamar yana cire ka daga wani mawuyacin yanayi a rayuwa. Ƙari ga haka, yana ƙarfafa ka da waɗannan kalaman: ‘Kada ka ji tsoro, zan taimake ka.’

Kana ɗaukan Jehobah kamar Uba da aboki mai ƙauna da zai taimake sa’ad da kake shan wahala? Yana ƙaunarka, ya damu da kai kuma ya kuɗiri aniya zai taimake ka. Sa’ad da kake cikin mawuyacin yanayi, Jehobah yana so ka dogara da shi domin ba zai taɓa barin ka ba. Hakika, shi mai taimakonka ne na kurkusa a lokacin “wahala.”—Zab. 46:1.

SA’AD DA MUKE DAMUWA GAME DA ZUNUBIN DA MUKA YI A DĀ

Wasu suna yawan damuwa game da kurakuran da suka yi a dā kuma suna ganin cewa Allah bai  gafarta musu ba. Idan ka sami kanka a cikin irin wannan yanayin, ka yi la’akari da wannan bawan Allah mai suna Ayuba, wanda ya tuna da ‘laifin ƙuruciyarsa.’ (Ayu. 13:26) Dauda marubucin wannan zabura ya kasance da irin wannan ra’ayin kuma ya roƙi Jehobah cewa: “Kada ka tuna da zunubaina na ƙuruciya, ko laifofina.” (Zab. 25:7) Dukanmu ajizai ne don mun “yi zunubi” kuma mun “kasa . . . ga darajar Allah.”—Rom. 3:23.

An rubuta Ishaya sura 41 don mutanen Isra’ila na dā. Sun yi zunubi sosai kuma saboda haka Jehobah ya sa aka kai su bauta a Babila. (Isha. 39:6, 7) Duk da haka, Allah ya san cewa lokaci na zuwa da yawancinsu za su tuba kuma zai cece su. (Isha. 41:8, 9; 49:8) Hakazalika a yau, Jehobah yana irin wannan tunanin game da waɗanda suka tuba da gaske kuma suna so su faranta masa rai.—Zab. 51:1.

Ka yi la’akari da labarin Takuya, * da yake ƙoƙarin daina halayen banza da suka ƙunshi kallon hotunan batsa da kuma wasa da al’aurarsa. Ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba ya yi ƙoƙarin ya daina amma ya kasa. Yaya ya ji? Ya ce: “Na ji kamar ba ni da daraja ko kaɗan. Amma sa’ad da na roƙi Jehobah ya gafarta min zunubaina, ya taimaka mini.” Ta yaya Jehobah ya yi hakan? Dattawan da ke ikilisiyarsu Takuya sun gaya masa cewa ya kira su a duk lokacin da ya kalli hotunan batsa ko kuma ya yi wasa da al’aurarsa. Ya ce: “Gaya musu bai da sauƙi, amma a duk lokacin da na yi hakan, suna ƙarfafa ni.” Bayan haka, dattawan suka gaya wa mai kula da da’ira ya kai wa Takuya ziyarar ƙarfafawa. Mai kula da da’irar ya gaya masa: “Ban zo ganin ka ba gaira ba dalili ba. Na zo ne don dattawa suna son in zo nan. Sun zaɓe ka don suna so a ziyarce ka.” Takuya ya ce: “Ni ne mai zunubi, amma Jehobah ya yi amfani da dattawa don ya taimaka min.” Takuya ya sami ci gaba har ya zama majagaba kuma yanzu yana hidima a ofishin Shaidun Jehobah. Jehobah zai taimaka maka kamar yadda ya taimaka wa wannan ɗan’uwan.

SA’AD DA MUKE DAMUWA GAME DA RASHIN AIKI

Rashin aiki yana sa mutane da yawa alhini. Wasu sun rasa aikinsu kuma sun kasa samun wani aiki. Shin yaya za ka ji idan aka ƙi ba ka aiki a duk inda ka je neman aiki? A irin wannan yanayin, wasu sukan daina ganin kansu da daraja. Ta yaya Jehobah zai iya taimaka maka? Wataƙila ba zai yi maka tanadin wani aikin nan da nan ba, amma zai taimaka maka ka tuna da abin da Sarki Dauda ya rubuta: “Dā yaro na ke, yanzu kuwa na tsufa: Amma ban taɓa gani an yar da mai-adalci ba, ko kuwa zuriyarsa suna roƙon abincinsu.” (Zab. 37:25) Hakika, kana da daraja a gaban Jehobah, kuma zai yi amfani da ‘hannun damarsa na adalci’ ya tanadar maka da abin da kake bukata don ka ci gaba da bauta masa.

Ta yaya Jehobah zai iya taimaka maka idan ka rasa aikinka?

Wata ’yar’uwa mai suna Sara a Kolombiya ta shaida yadda Jehobah yake taimakon bayinsa. Ta yi aiki da wani kamfani da ake biyan ta albashi mai tsoka. Amma tana so ta ƙara yin hidima a bautar  Jehobah, saboda haka, ta yi murabus kuma ta soma hidimar majagaba. Amma ba ta sami aikin wucin gadi da take so ba. Sai ta buɗe shagon sayar da ayis kirim amma jarinta ya kare kuma ta rufe shagon. Sara ta ce: “Na yi shekara uku ban da aiki, amma na gode wa Jehobah cewa na jure yanayin.” Hakan ya taimaka wa Sara ta mai da hankali ga ainihin bukatunta maimakon sayan dukan abin da take so. Ƙari ga haka, ta daina damuwa game da yadda za ta sami abin biyan bukata. (Mat. 6:33, 34) Da shigewar lokaci, manajan kamfanin da ta yi aiki a dā ya ce ta koma yin aikinta na dā a kamfanin. Ta ce za ta yi aiki a kamfanin ne kawai idan ya rage lokacin da take aiki don ta sami lokacin yin ayyukan da suka shafi ibada. Ko da yake ba a biyan Sara albashi mai tsoka kamar dā, amma ta ci gaba da hidimar majagaba. A ƙarshe ta ce: “Na san cewa Jehobah ne ya taimake ni.”

JIN TSORON MATSALOLIN DA KE TATTARE DA TSUFA

Wani abu kuma da yake sa mutane damuwa ainun shi ne tsoron matsalolin da ke tattare da tsufa. Mutane da yawa suna damuwa sosai don suna ganin cewa idan suka yi murabus, ba za su sami isashen kuɗi biyan bukatunsu ba. Ƙari ga haka, sukan yi alhini game da matsaloli na rashin lafiya da za su iya fuskanta yayin da suke tsufa. A yawancin lokaci, sukan ji kamar Dauda da ya roƙi Jehobah cewa: ‘Kada ka yashe ni cikin kwanakin tsufa; kada ka yar da ni lokacin da ƙarfina ya ƙare.’—Zab. 71:9, 18.

Ta yaya bayin Jehobah za su kasance da kwanciyar hankali sa’ad da suka tsufa? Suna bukatar su ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarsu kuma su dogara ga Allah cewa zai biya bukatunsu. Idan a dā sun yi rayuwar jin daɗi, za su bukaci su sauƙaƙa rayuwarsu kuma su yi amfani da ɗan ƙaramin abin da ke hannunsu. Da shigewar lokaci, za su saba da cin “abinci na ganye” maimakon cin naman ‘sa’ mai kitse, kuma hakan zai iya inganta lafiyarsu. (Mis. 15:17) Idan ka mai da hankali ga faranta wa Jehobah rai, ka tabbata cewa zai biya bukatunka a lokacin da ka tsufa.

José da Rose tare da Tony da Wendy

José da Rose sun yi shekaru 65 suna hidima ta cikakken lokaci. Sun yi jinyar mahaifin Rose wanda yake bukatar kulawa a kowane lokaci. Ƙari ga haka, an yi wa José tiyata saboda cutar kansa kuma yana fama da jinyar. Shin Jehobah ya taimaka wa waɗannan ma’aurata masu aminci kuwa? Hakika. Amma ta yaya ya yi hakan? Jehobah ya yi amfani da wasu ma’aurata, wato Tony da matarsa Wendy, da ke cikin ikilisiyar. Sun ba su gidan da za su zauna. Shekaru da yawa kafin wannan lokacin, Tony ya lura da yadda José da Rose suke zuwa wa’azi babu fashi. Himmar da suka nuna ya burge shi ba kaɗan ba. Yadda waɗannan ma’aurata suka ba da kansu don bauta wa Jehobah ne ya motsa Tony da Wendy su taimaka musu, kuma sun yi shekara 15 suna taimaka wa José da Rose. Yanzu waɗannan ma’aurata sun tsufa kuma suna ganin cewa Jehobah ne ya yi amfani da Tony da Wendy don ya taimaka musu.

Allah yana miƙa maka ‘hannun damarsa na adalci’ don ya taimake ka. Shin za ka amince da taimakonsa kuwa? Ya yi alkawari cewa: ‘Kada ka ji tsoro, zan taimake ka.’

^ sakin layi na 11 An canja wasu sunaye.