Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ME LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA MALA’IKU?

Yadda Mala’iku Suke Taimaka Maka

Yadda Mala’iku Suke Taimaka Maka

Mala’iku masu aminci sun damu da ’yan Adam kuma suna yin nufin Jehobah. Sa’ad da Allah ya halicci duniya, mala’iku sun “yi waƙa, dukan ’ya’yan Allah kuwa suka yi sowa don farin ciki.” (Ayuba 38:​4, 7) Tun asali, mala’iku suna ‘ɗokin ganin’ abubuwan da za su faru a duniya a nan gaba.​—1 Bitrus 1:11, 12, Littafi Mai Tsarki.

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a wasu lokuta, mala’iku suna kāre bayin Allah don a cika nufin Allah. (Zabura 34:7) Alal misali:

  • Sa’ad da Allah yake so ya halaka birnin Saduma da Gwamarata, ya aika mala’ikunsa su taimaka wa Lutu da iyalinsa su bar birnin.​—Farawa 19:​1, 15-26.

  • A ƙasar Babila ta dā, an jefa Ibraniyawa uku cikin wuta don su mutu, amma Allah “ya aiko mala’ikansa, ya ceci bayinsa.”​—Daniyel 3:​19-28.

  • Da Daniyel ya kwana a cikin ramin zakunan da aka jefa shi ciki, ya ce ya tsira ne domin ‘Allahnsa ya aiko mala’ikansa, ya rufe bakin zakunan.’​—Daniyel 6:​16, 22.

Mala’iku sun daɗe suna taimaka wa bayin Allah

MALA’IKU SUN TAIMAKA WA KIRISTOCI A ƘARNI NA FARKO

Akwai lokacin da mala’iku suka taimaka wa Kiristoci a ƙarni na farko a aikin da suka yi don a cika nufin Jehobah. Alal misali:

  • Sa’ad da aka saka manzannin Yesu a cikin kurkuku, wani mala’ika ya buɗe ƙofar kurkukun kuma ya ce su je su ci gaba da yin wa’azi a haikali.​—Ayyukan Manzanni 5:17-21.

  • Wani mala’ika ya umurci manzo Filibus cewa ya bi wata hanyar hamada da ta fito daga Urushalima zuwa Gaza. Me ya sa? Domin ya yi wa’azi ga wani Bahabashe da ya je ibada a Urushalima.​—Ayyukan Manzanni 8:26-33.

  • Sa’ad da Allah yake so waɗanda ba Yahudawa ba su zama Kiristoci, wani sojan Roma mai suna Karniliyus ya ga wahayi. A wahayin, wani mala’ika ya ce masa ya gayyaci manzo Bitrus zuwa gidansa.​—Ayyukan Manzanni 10:3-5.

  • Da aka saka manzo Bitrus a kurkuku, wani mala’ika ya fitar da shi daga cikin kurkukun.​—Ayyukan Manzanni 12:1-11.

 YADDA MALA’IKU SUKE TAIMAKA MAKA

Ko da yake ba mu da tabbaci cewa Allah yana amfani da mala’ikunsa don ya taimaka wa mutane kamar yadda ya yi a dā. Amma Yesu ya ce game da zamaninmu: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’an nan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:14) Ka san cewa da taimakon mala’iku ne mabiyan Kristi suke yin wannan aikin?

Mala’iku suna taimakawa a wa’azin da ake yi a faɗin duniya

Littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa mala’iku za su riƙa taimaka wa mutane a faɗin duniya su koyi game da Jehobah da kuma nufinsa. Manzo Yohanna ya ce: “Na ga wani mala’ika kuma yana firiya a tsakiyar sararin sama, yana da bishara ta har abada wadda za ya yi shelarta ga mazaunan duniya, ga kowane iri da ƙabila da harshe da al’umma; da babbar murya kuwa ya ce, ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja; gama sa’ar hukuncinsa ta zo: ku yi sujada ga Wanda ya yi sama da duniya da teku da maɓulɓulan ruwaye.” (Ru’ya ta Yohanna 14:​6, 7) Abubuwan da suke faruwa a yau sun nuna mana cewa mala’iku suna taimakawa a wa’azin da muke yi. Hakika, mala’ikun Allah suna “murna” sa’ad da wani ya tuba kuma ya komo ga Jehobah.​—Luka 15:10.

Amma mene ne zai faru bayan an kammala wa’azin da ake yi a zamaninmu? “Rundunonin sama,” wato mala’iku za su goyi bayan Yesu Kristi wanda shi ne Sarkin sarakuna, a lokacin da zai yi “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka” da ake kira Armageddon. (Ru’ya ta Yohanna 16:​14-16; 19:​14-16, LMT) Yayin da Yesu yake hukunta “waɗanda . . . sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu,” mala’iku masu iko ne za su halaka su.​—2 Tasalonikawa 1:7, 8.

Don haka, ka kasance da tabbaci cewa mala’iku sun damu da kai. Sun damu da waɗanda suke so su bauta wa Allah, kuma Jehobah yana amfani da su don ya ƙarfafa bayinsa a duniya da kuma kāre su.​—Ibraniyawa 1:14.

Saboda haka, dukanmu muna da tambaya mai muhimmanci da ya kamata mu yi tunani a kai. Za mu saurari wa’azi kuma mu yi abin da aka gaya mana? Shaidun Jehobah a yankinku za su yi farin cikin taimaka maka ka amfana daga taimakon da mala’ikun Allah suke yi.