Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ME LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA MALA’IKU?

Bayani na Gaskiya Game da Mala’iku

Bayani na Gaskiya Game da Mala’iku

Za ka so ka san gaskiya game da mala’iku da inda suka fito da kuma abin da suke yi? Littafi Mai Tsarki ne zai iya ba mu amsoshi masu gamsarwa ga waɗannan tambayoyin. (2 Timotawus 3:16) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da hakan?

  • Kamar yadda Allah Ruhu ne, haka ma mala’iku su ma halittun ruhu ne kuma ba su da “nama da ƙasusuwa.” Mala’iku masu aminci suna zama a sama kuma suna da gatan zuwa gaban Allah.​—Luka 24:39; Matta 18:10; Yohanna 4:24.

  • A dā, mala’iku suna canja kamaninsu zuwa na mutane don su zo su yi aikin da Allah ya ba su a duniya. Amma bayan sun gama aikin, suna canja jikinsu kuma su koma sama.​—Alƙalawa 6:11-23; 13:15-20.

  • Ko da yake Littafi Mai Tsarki yana yawan nuna cewa mala’iku maza ne, amma babu namiji ko tamace a cikinsu. Ba sa aure kuma ba sa haifan yara. Ba a haifan mala’iku kamar yadda ’yan Adam suke yi. Jehobah ne da kansa ya halicce su, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya kira su “’ya’yan Allah.”​—Ayuba 1:6; Zabura 148:2, 5.

  • Littafi Mai Tsarki ya ambata “harsunan mutane da na mala’iku,” kuma hakan ya nuna cewa mala’iku ma suna da nasu yaren. Ko da yake a dā Allah ya yi magana da mutane ta wurin mala’iku, amma bai amince mu bauta ko kuma mu yi addu’a ga mala’iku ba.​—1 Korintiyawa 13:1; Ru’ya ta Yohanna 22:8, 9.

  • Da akwai dubun dubban mala’iku, wataƙila sun kai biliyoyi.​—Daniyel 7:10; Ru’ya ta Yohanna 5:11.

  • Mala’iku halittu ne da suke da “iko” sosai kuma sun fi ’yan Adam ƙarfi da kuma fahimi. Suna tafiya da saurin gaske fiye da yadda za mu iya tsammani.​—Zabura 103:20; Daniyel 9:20-23.

  • Duk da cewa mala’iku suna da iko da kuma fahimi sosai, da akwai wasu abubuwan da ba su sani ba kuma ba za su iya yi ba.​—Matta 24:36; 1 Bitrus 1:12.

  • An halicci mala’iku da halaye masu kyau sosai, kuma kamar ’yan Adam suna da ’yancin yin abu mai kyau ko marar kyau. Abin baƙin ciki shi ne, wasu mala’iku sun yi tawaye da Allah kuma suka daina bauta masa.​—Yahuda 6.