Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Za a halaka dukan makaman yaƙi

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Za a sake zaman lafiya a duniya kuwa?

Me za ka ce?

  • E

  • A’a

  • Wataƙila

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

A Mulkin Allah, Yesu zai kawo “salama mai-yawa, har sai wata ya faɗi,” wato har abada.​—Zabura 72:7.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Za a halaka masu mugunta, hakan zai sa masu adalci “su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”​—Zabura 37:10, 11.

  • Allah zai sa a daina yin yaƙi a dukan duniya.​—Zabura 46:8, 9.

Zai yiwu a kasance da kwanciyar hankali yanzu kuwa?

Wasu sun yi imani cewa . . .ba zai yiwu a kasance da kwanciyar hankali ba idan har an ci gaba da yin rashin adalci a duniya. Mene ne ra’ayinka?

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

Ko a yanzu ma, waɗanda suke yin nufin Allah za su iya kasancewa da ‘salama ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka.’​—Filibiyawa 4:6, 7.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Allah ya yi alkawari cewa zai cire dukan rashin adalci da wahala, kuma ya “sabonta dukan abu.”​—Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5.

  • Za mu kasance da kwanciyar hankali idan muka “ƙulla dangantaka da Allah.”​—Matta 5:​3, New World Translation.