Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ina wa’azi tare da matata Tabitha

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

A Dā, Ban Yi Imani da Wanzuwar Allah Ba

A Dā, Ban Yi Imani da Wanzuwar Allah Ba
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1974

  • ƘASAR HAIHUWA: MULKIN DIMOKURAƊIYYA NA JAMUS

  • TARIHI: BAN YI IMANI DA ALLAH BA

RAYUWATA A DĀ

An haife ni a wani ƙauye a jihar Saxony, a wata ƙasa da a dā ake kira Mulkin Dimokuraɗiyya na Jamus (MDJ). Na taso a cikin iyalin da ake nuna ƙauna sosai kuma iyayena sun yi mini tarbiyya mai kyau. Gwamnatin Kwaminisanci ne ake yi a ƙasar. Don haka, yawancin mutanen da ke jihar Saxony ba su damu da addini ba. Ban yi imani da wanzuwar Allah ba. Ni ɗan Kwaminis ne tun da aka haife ni har na kai shekara 18 kuma ban amince da wanzuwar Allah ba.

Dalilin da ya sa nake son Kwaminisanci shi ne don sun yi imani cewa dukan mutane ɗaya ne. Na kuma yi imani cewa idan za a raba arzikin ƙasa, ya kamata a yi raba-dai-dai domin kowa zai sami abin biyan bukata. Shi ya sa na shiga ƙungiyar Kwaminisanci na matasa. Da na kai shekara 14, na soma aiki a kamfanin da ake sarrafa tsofaffin takardu. Hukumomin da ke garin Aue sun ji daɗin aikin da nake yi kuma suka ba ni kyauta. Ta hakan ne na san wasu manyan-manyan ’yan siyasa a Jamhuriyar duk da cewa ni yaro ne a lokacin. Na ji kamar abin da nake yi shi ne daidai kuma zai sa na yi nasara a rayuwa.

Sai abubuwa suka soma canjawa. An rushe ganuwar Berlin a shekara ta 1989 kuma hakan ya wargaje gamin da ke tsananin ƙasashen da ke Kwaminisanci a Gabashin Turai. An soma rigima a ko’ina. Sai na zo na gane cewa ana rashin adalci a Jamhuriyar. Alal misali, ba a ɗaukan waɗanda ba sa goyon bayan Kwaminisanci da muhimmanci sosai. Me ya sa ake yin haka? Shin ba mu ’yan Kwaminis mun ce dukan mutane ɗaya ba ne? Ko kuwa ƙarya ne kawai suke yi? Hakan ya dame ni sosai.

Sai na canja maƙasudina kuma na soma koyan waƙa da kuma yin zane-zane. Ina so in zama mawaƙi. Don haka na shiga makarantar da ake koyar da waƙa kuma ina sa ran zuwa jami’a bayan haka. Ban da haka ma, na daina kasancewa da halaye masu kyau da na koya tun ina yaro. Abin da na fi so yanzu shi ne jin daɗin rayuwa. Hakan ya sa na soma neman mata. Amma waɗannan abubuwan ba su magance matsalolina ba. Ko hotunan da nake zanawa ma suna nuna cewa ina cikin tashin hankali. Mene ne zai faru a nan gaba? Me ya sa aka halicce mu?

Na yi mamaki sosai sa’ad da na sami amsoshin tambayoyin nan. Wata rana da yamma a makaranta, na zauna da wasu ’yan makarantarmu muna tattauna game da nan gaba. A cikinsu akwai wata yarinya mai suna Mandy * kuma ita Mashaidiyar Jehobah ce. A ranar, ta ba ni wata shawara mai kyau. Ta ce, “Andreas, idan kana so ka san abin da zai faru a nan gaba da kuma dalilin da ya sa aka halicce mu, ka je ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki.”

Ko da yake ina shakkar abin da ta ce amma na soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Mandy ta ce na karanta littafin Daniyel sura 2 kuma abin da na karanta ya ba ni mamaki. A wurin, an yi annabci a kan mulkoki da yawa da za su yi tasiri a rayuwar mutane daga zamanin dā har zuwa zamaninmu. Mandy ta kuma nuna mini wasu annabcin Littafi Mai Tsarki da za su faru a nan gaba. Yanzu na sami amsoshin tambayoyina! Amma sai na ce wa kaina, wai wane ne ya rubuta waɗannan annabcin, kuma wane ne zai iya faɗin abin da zai faru a nan gaba har ya faru da gaske? Ko dai Allah ya wanzu da gaske ne?

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

Mandy ta haɗa ni da wasu ma’aurata masu suna Horst da Angelika don su taimaka mini na fahimci Littafi Mai Tsarki sosai. Nan da nan na gane cewa Shaidun Jehobah ne kaɗai addinin da suke yawan amfani da sunan Allah, wato Jehobah. (Zabura 83:18; Matta 6:⁠9) Na koya cewa Jehobah Allah ya halicci ’yan Adam don su yi rayuwa har abada a aljanna. Littafin Zabura 37:9 ta ce: “Waɗanda ke sauraro ga Ubangiji, su ne za su gāji duniya.” Na yi farin ciki da na koyi cewa duk waɗanda suke bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su sami wannan albarkar.

Amma bin waɗannan ƙa’idodin ba su kasance mini da sauƙi ba. Na yi suna sosai sa’ad da nake waƙa kuma hakan ya sa ina da fahariya. Don haka, ina bukatar in kasance da sauƙin kai. Ban da haka, bai kasance mini da sauƙi na daina neman mata ba. Ina godiya don yadda Jehobah yake nuna jinƙai da kuma haƙuri ga waɗanda suke iya ƙoƙari don su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki!

Ni ɗan Kwaminis ne tun da aka haife ni har na kai shekara 18 kuma ban amince da wanzuwar Allah ba. Amma yanzu Littafi Mai Tsarki ya canja rayuwata. Abin da na koya ya sa na daina damuwa game da nan gaba kuma ya sa rayuwata ta kasance da ma’ana. Na yi baftisma a shekara ta 1993. A shekara ta 2000, na auri wata ’yar’uwa mai ƙwazo mai suna Tabitha. Muna amfani da lokacinmu wajen koya wa mutane Littafi Mai Tsarki. Mutane da yawa da muke haɗuwa da su a wa’azi ’yan Kwaminis ne kuma ba su yi imani da wanzuwar Allah ba. Ina jin daɗin koya musu game da Jehobah.

YADDA NA AMFANA

Iyayena sun yi mamaki sa’ad da na soma nazari da Shaidun Jehobah. Amma tun daga lokacin, sun ga yadda yin tarayya da Shaidu ta canja rayuwata. Ina murna cewa su ma yanzu suna karanta Littafi Mai Tsarki kuma suna halartar taro.

Ni da Tabitha muna jin daɗin aurenmu domin muna bin shawarar da Littafi Mai Tsarki take ba ma’aurata. Alal misali, bin ƙa’idar da ya bayar game da riƙon amana a aure tana ƙarfafa aurenmu sosai.​—Ibraniyawa 13:4.

A yanzu, na daina jin tsoron abin da zai faru a nan gaba. Ina farin cikin zama Mashaidin Jehobah don mutanen suna da kwanciyar hankali da haɗin kai. Kamar iyali muke kuma ba ma nuna bambanci. Abin da na yi imani da shi ke nan kuma nake so in cim ma a rayuwata.

^ sakin layi na 12 An canja sunan.