Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Zai Yiwu a Daina Zalunci a Duniya Kuwa?

Zai Yiwu a Daina Zalunci a Duniya Kuwa?

Shin an taɓa zaluntar ka ko kuma wani danginka? Kana tsoro cewa wani zai iya zaluntar ka? Zalunci ya zama “ruwan dare gama gari a duniya.” Ga wasu misalai.

WULAƘANTA MATA DA KUMA CIN ZARAFINSU: Wani rahoto na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce: “Kashi ɗaya cikin mata uku suna fama da wulaƙanci da kuma cin zarafi daga wurin mazansu.” Kuma rahoton ya ambata wani abin baƙin ciki. Ya ce: “Ɗaya cikin mata biyar za su faɗa cikin hannun ʼyan fyaɗe.”

ZALUNCI: An ba da rahoto cewa akwai rukunin ’yan ɓata gari fiye da dubu talatin a ƙasar Amirka. A wani ɓangaren Latin Amirka kuma, ana zaluntar kusan mutum ɗaya cikin uku.

KISA: Wani rahoto ya nuna cewa, an kashe mutane kusan dubu ɗari biyar a ɗaya daga cikin shekarun baya kuma wannan adadin ya fi na waɗanda ake kashewa a yaƙi. Kisan da ake yi a kudancin Afirka da kuma Amirka ta Tsakiya ya ninka wadda ake yi a duniya sau huɗu. A cikin shekara guda, an kashe mutane sama da dubu ɗari a Latin Amirka, a ƙasar Brazil kuma wajen dubu hamsin. Shin, za a iya daina kisa ko zalunci a duniya kuwa?

ZA A IYA KAWO ƘARSHEN ZALUNCI KUWA?

Me ya sa zalunci ya zama ruwan dare gama-gari a duniya? Ga wasu dalilai: nuna bambanci da yin renon yara a wurin da ake yawan faɗa da shaye-shaye da ƙin daraja rayukan mutane da kuma ƙyale ʼyan ɓata-gari su yi abin da suka ga dama.

Babu shakka, ana ƙoƙarin kawar da zalunci a wasu wurare a duniya. Alal misali, a birnin São Paulo, a ƙasar Brazil, an lura cewa kisa ya ragu da kashi tamanin bisa ɗari a cikin shekaru goma da suka shige. Duk da haka, ana kashe mutane goma cikin dubu ɗari a birnin. To, me kake ganin za a iya yi don a kawar da zalunci ko kisa?

Za a iya kawar da zalunci ko kisa idan ’yan Adam suka canja halayensu. Waɗanne halaye ke nan? Fahariya da haɗama da kuma son kai. Idan mutane suka daina irin waɗannan halayen kuma suka soma nuna ƙauna da ladabi da kuma mutunta mutane, za a daina zalunci.

Amma me zai iya taimaka wa mutum ya yi irin waɗannan canje-canjen? Ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce:

  • “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa.”—1 Yohanna 5:3.

  • “Ƙin mugunta shi ne tsoron Ubangiji.”—Misalai 8:13, Littafi Mai Tsarki.

Idan muna ƙaunar Allah kuma muna so mu kiyaye dokokinsa, za mu iya yin canji na gaske ba tuban muzuru ba. Amma hakan zai yiwu kuwa?

Ga misalin wani mai suna Alex, * wanda yi shekara  goma sha tara a fursuna a ƙasar Brazil don kashe-kashen da ya yi. Ya zama Mashaidin Jehobah bayan da aka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi a shekara ta 2000. Ya canja halayensa da gaske kuwa? E, kuma abubuwan da Alex ya yi sun dame shi sosai, shi ya sa ya tuba. Ya ce: “Ina ƙaunar Allah sosai domin ya gafarta zunubaina. Nuna godiya ga Jehobah don alherinsa da kuma ƙaunar da nake masa ne suka taimaka mini na canja salon rayuwata.”

Akwai wani mai suna César a ƙasar Brazil da ya yi shekara goma sha biyar yana fashi da makami. Me ya taimaka masa ya yi canji? Shaidun Jehobah sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi sa’ad da yake fursuna. César ya ce: “Lokaci na farko ke nan da na fahimci ma’anar rayuwa. Na koyi yadda zan ƙaunaci Allah da kuma abin da zan yi don kada in koma gidan jiya domin yin hakan zai ɓata wa Jehobah rai. Ba na so in nuna rashin godiya don alherinsa. Waɗannan abubuwan ne suka taimaka mini in canja salon rayuwata.”

Ka koyi abin da ya kamata ka yi don ka zauna a duniyar da babu zalunci

Me muka koya daga waɗannan misalan? Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka wa mutane su canja salon rayuwarsu da kuma ra’ayinsu. (Afisawa 4:23) Alex, da aka ambata ɗazu ya daɗa da cewa: “Abubuwan da na koya daga Littafi Mai Tsarki sun zama kamar wani ruwa mai tsabta da ke gangarawa a zuciyata kuma yana tsabtace tunanina. Ban taɓa tsammanin cewa zan iya daina irin waɗannan halayen ba.” Babu shakka, idan muka cika zuciyarmu da koyarwar Littafi Mai Tsarki, hakan zai taimaka mana mu wanke ko kuma share duk wani ra’ayin da bai dace ba. Kalmar Allah tana da ikon canja salon rayuwar mutum. (Afisawa 5:26) Sakamakon shi ne, mutanen da ke zalunci a dā kuma suke son kai za su iya canjawa su zama masu alheri kuma su riƙa zaman lafiya da mutane. (Romawa 12:18) Kuma za su sami kwanciyar hankali don suna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.—Ishaya 48:18.

Ban da haka, Shaidun Jehobah fiye da miliyan takwas a ƙasashe 240 sun gano abin da ke taimaka wa mutane su daina zalunci. Mutanen kabilu da kuma yanayoyi dabam-dabam sun koyi ƙauna da tsoron Allah. Sun kuma koyi yin ƙaunar juna da zaman lafiya. (1 Bitrus 4:8) Hakan ya tabbatar mana da cewa akwai lokacin da za a sami zaman lafiya a duniya gabaki ɗaya.

ZA A DAINA ZALUNCI NAN BA DA DAƊEWA BA!

Allah ya yi alkawari a cikin Littafi Mai Tsarki cewa zai kawo ƙarshen zalunci a duniya nan ba da daɗewa ba. Allah ya riga ya shirya “ranar shari’a da halakar mutane masu-fajirci.” (2 Bitrus 3:5-7) Ba za a ƙara zaluntar wani ba. Me ya sa muke da tabbaci cewa Allah zai kawo ƙarshen zalunci?

Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya tsani “mai-son zalunci.” (Zabura 11:5) Mahaliccinmu yana son adalci da salama. (Zabura 33:5; 37:28) Shi ya sa ba zai ƙyale zalunci ya ci gaba har abada ba.

Muna da tabbaci cewa a nan gaba, mutane za su zauna cikin lumana a duniya. (Zabura 37:11; 72:14) Zai dace ka bincika yadda za ka cancanci zama a duniyar da babu zalunci.

^ sakin layi na 14 An canja sunayen.