Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Na Ji Jiki Sosai Kafin Na Yi Nasara

Na Ji Jiki Sosai Kafin Na Yi Nasara
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1953

  • ƘASAR HAIHUWA: OSTARELIYA

  • TARIHI: YA SHAƘU DA HOTUNAN BATSA

RAYUWATA A DĀ:

A shekara ta 1949, mahaifina ya ƙaura daga ƙasar Jamus zuwa Ostareliya. Ya zo neman aiki a kamfanin lantarki da kuma haƙa ma’adinai. A sakamakon haka, sai ya kama zama a ƙauyen Victoria. Bayan haka, sai ya auri mahaifiyata kuma aka haife ni a shekara ta 1953.

’Yan shekaru bayan haka, sai mahaifiyata ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Hakan ya sa na san Littafi Mai Tsarki tun ina ƙarami. Amma, mahaifina ba ya son addini sam-sam. Sai ya soma tsananta mata sosai don ya hana ta nazarin. Duk da haka, ta ci gaba da yin nazari a asirce kuma ta so abin da take koya sosai. A duk lokacin da mahaifina ba ya gida, tana yin amfani da zarafin wajen koya wa ni da ƙanwata Littafi Mai Tsarki. Tana yawan gaya mana game da yadda duniya za ta zama aljanna da kuma yadda za mu yi farin ciki idan muka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a.—Zabura 37:10, 29; Ishaya 48:17.

Sa’ad da nake ɗan shekara 18, na bar gida saboda rigimar mahaifina. Na yi imani da abubuwan da mahaifiyata ta koya mini daga Littafi Mai Tsarki, amma ban ɗauke su da muhimmanci ba. Saboda haka, ban yi amfani da su ba a lokacin. Sai na soma gyaran lantarki a kamfanin haƙa ma’adinai. Na yi aure sa’ad da nake ɗan shekara 20. Bayan shekara uku, sai matata ta haifi ’ya mace, kuma na sake yin tunani a kan abin da ya fi muhimmanci a rayuwata. Na san cewa Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka wa iyalinmu, saboda haka, sai na soma nazari da Shaidun Jehobah. Amma matata ba ta so hakan ba. Wata rana da na halarci taron Shaidun Jehobah, sai ta ce mini, in ban daina nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidu ba, za mu kashe aurenmu. Da yake na tsorata, sai na daina tarayya da Shaidun Jehobah. Amma daga baya, na yi da-na-sani don ban yi abin da ya dace ba.

Wata rana, sai abokan aikina suka nuna mini hotunan batsa. Na yi sha’awar abin da na gani, amma hakan ya dame ni sosai. Abin da na taɓa koya a cikin Littafi Mai Tsarki ya sa na san cewa Allah zai hukunta ni. Amma yayin da na ci gaba da kallon waɗannan hotunan, sai ya zama mini jiki sosai.

Daga wannan ranar har zuwa shekara 20 bayan haka, na ci gaba da nisanta kaina daga ƙa’idodin da mahaifiyata ta koya mini. Halayena  sun canja saboda abubuwan da nake kallo. Ina yawan yin ɗanyen magana da kuma wasan banza. Na kasance da ra’ayi marar kyau game da jima’i. Ko da yake ina da aure, amma ina sha’ani da wasu mata. Wata rana, na kalli kaina a madubi, sai na soma ƙyamar kaina don na riga na zubar da mutuncina.

Bayan haka, sai aurenmu ya mutu kuma hakan ya dame ni sosai. Na yi addu’a ga Jehobah da dukan zuciyata. Sai na soma nazarin Littafi Mai Tsarki, ko da yake shekara ashirin ke nan da na rabu da yin hakan. A wannan lokacin, mahaifina ya rasu kuma mahaifiyata ta riga ta yi baftisma ta zama Mashaidiyar Jehobah.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Ayyukana ba su jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba ko kaɗan. Amma a wannan lokacin, na ƙuduri niyyar samun kwanciyar rai da Littafi Mai Tsarki ya yi mana alkawarinsa. Na yanke shawarar daina ɗanyen magana da fushi da lalata da cacā da shaye-shaye da kuma sata a wurin aiki.

Abokan aikina ba su fahimci dalilin da ya sa nake so in yi waɗannan canje-canje ba. Sun yi shekara uku suna taƙura mini in koma gidan jiya. A duk lokacin da na yi ɗaya cikin abubuwan da nake yi a dā, kamar fushi ko ɗanyen magana, sai su soma ihu, suna cewa: “To fa! Joe ya dawo hankalinsa.” Hakan yana ɓata mini rai sosai kuma yana sa ni baƙin ciki.

Akwai hotunan batsa a ko’ina a wurin aikinmu. Abokan aikina suna yawan aika mana hotunan batsa ta kwamfuta, kamar yadda nake yi a dā. Ina neman in canja halayena na dā, amma sun ƙuduri niyyar hana ni yin waɗannan canje-canjen. A sakamakon haka, na nemi taimako daga wurin ɗan’uwan da ke nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Ya saurare ni sosai yayin da nake gaya masa dukan matsalolina. Ya nuna mini ayoyi da yawa na Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mini in yi nasara, kuma ya ƙarfafa ni in riƙa yin addu’a ga Jehobah a kai a kai don ya taimake ni.—Zabura 119:37.

Wata rana, sai na tattara dukan abokan aikina. Sa’ad da muka taru, sai na ce a miƙa giya wa abokan aikina biyu da suke neman su daina shaye-shaye. Amma sai dukansu suka soma ihu: “Haba! Yaya za ka ce haka bayan ka san cewa suna neman su daina shaye-shaye!” Sai na ce musu: “Ni ma ina ƙoƙarin yin canji.” Tun daga ranar, suka san cewa ina neman in daina kallon hotunan batsa kuma suka daina taƙura mini.

Da sannu-sannu, Jehobah ya taimaka mini in daina kallon hotunan batsa. A shekara ta 1999, na yi baftisma kuma na zama Mashaidin Jehobah. Na yi farin ciki sosai cewa Jehobah ya ba ni wani zarafin tsabtace rayuwata.

Yanzu, na fahimci dalilin da ya sa Jehobah ya tsani abubuwan da nake so a dā. Da yake shi Uba ne mai ƙauna, yana so ya kāre ni daga matsalolin da kallon hotunan batsa ke jawowa. Na fahimci gaskiyar kalmomin da ke Misalai 3:5, 6. Ayoyin sun ce: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: a cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suna kāre ni sosai kuma suna taimaka mini in yi nasara.—Zabura 1:1-3.

YADDA NA AMFANA:

A dā, ina ƙyamar kaina sosai, amma yanzu ina da mutunci da kuma kwanciyar hankali. Ina rayuwa mai tsabta kuma na san cewa Jehobah ya gafarta mini. A shekara ta 2000, na auri wata kyakkyawar mace mai suna Karolin da ke ƙaunar Jehobah sosai. Muna jin daɗin aurenmu sosai. Babban gata ne sosai kasancewa cikin ’yan’uwa Kiristoci na faɗin duniya masu ƙauna da kuma tsabta.