Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ʼYan Masoretes sun mai da hankali sosai wajen kofe Nassosi

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA AKA KĀRE LITTAFI MAI TSARKI

An Kasa Canja Sakon da Ke Cikin Littafi Mai Tsarki

An Kasa Canja Sakon da Ke Cikin Littafi Mai Tsarki

ƘALUBALE: Littafi Mai Tsarki bai ruɓe ba kuma ’yan hamayya sun kasa halaka shi. Duk da haka, wasu mafassara da masu kofe Littafi Mai Tsarki sun nemi su canja saƙon da ke cikinsa. A wasu lokuta, sun yi ƙoƙarin yin hakan don ya jitu da koyarwarsu. Ka yi la’akari da wasu misalai:

  • Wuraren ibada: A tsakanin ƙarni na huɗu zuwa ƙarni na biyu kafin zamanin Yesu, mafassaran juyin Samaritan Pentateuch sun saka furucin nan “a Tudun Gerizim ne za ka gina bagadi,” a ƙarshen Fitowa 20:17. Samariyawa sun yi wannan ƙarin gishirin ne don ya goyi bayan haikalin da suke so su gina a Tudun Gerizim.

  • Koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya: Ƙasa da shekara 300 bayan da aka kammala rubutun Littafi Mai Tsarki, wani marubuci da ya amince da koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya ya ƙara gishiri a littafin 1 Yohanna 5:7. Ya ce: “A cikin sama, akwai Uba da Kalma da kuma Ruhu Mai Tsarki: kuma su ukun ɗaya ne.” Amma babu wannan furucin a cikin rubutun Littafi Mai Tsarki na farko. Wani marubuci mai suna Bruce Metzger ya ce: “An fara samun waɗannan furucin a kofofin Littafi Mai Tsarki na Old Latin da [Latin] Vulgate daga ƙarni na shida.”

  • Sunan Allah: Mafassara da yawa sun cire sunan Allah daga Littafi Mai Tsarki cikin jituwa da dokar da Yahudawa suka kafa. Sun sauya sunan da laƙabi kamar su “Allah” da “Ubangiji.” Hakan bai dace ba domin ba Mahaliccinmu kaɗai ake kira da waɗannan laƙabin ba, amma ana kiran wasu mutane da allolin ƙarya, har ma da Shaiɗan da waɗannan laƙabin.—Yohanna 10:34, 35; 1 Korintiyawa 8:5, 6; 2 Korintiyawa 4:4. *

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA TSIRA: Da farko, ko da yake wasu mutanen da suka kofe Littafi Mai Tsarki ba su mai da hankali sosai ba ko kuma sun ɗan ƙara gishiri, amma da yawa daga cikinsu sun mai da hankali sosai. Wasu marubuta a tsakanin ƙarni na shida da goma bayan haihuwar Yesu sun kofe Nassosin Ibrananci, kuma aikin da suka yi ne ake kira juyin Masoretic a  yau. Tarihi ya nuna cewa waɗannan mutanen sun ƙirga kalmomi da kuma harufan da ke cikin Littafi Mai Tsarki don su tabbatar da cewa ba su yi wani kuskure ba. A duk inda suka ga cewa akwai kuskure a ainihin littafin da suke kofewa, suna ambata hakan a gefen littafin. Waɗannan mutanen sun ƙi su ƙara gishiri a cikin Littafi Mai Tsarki. Wani Farfesa mai suna Moshe Goshen-Gottstein ya ce: “Waɗannan mutanen sun gaskata cewa canja wani abu a cikin Littafi Mai Tsarki da gangan, laifi ne mafi girma.”

Na biyu, kofofin Littafi Mai Tsarki da yawa da muke da su a yau suna taimaka wa masana su gano kura-kuran da aka yi. Alal misali, limamai sun daɗe suna koyar da cewa juyin Littafi Mai Tsarki na yaren Latin ne na ƙwarai. Saboda haka, sai suka saka kalmomin nan da ba daidai ba da ke 1 Yohanna 5:7 da muka ambata ɗazun. Wannan ƙarin gishirin ya ma bayyana a juyin King James Version na Turanci. Amma mene ne aka lura sa’ad da aka gano wasu littattafai na Littafi Mai Tsarki? Bruce Metzger ya ce: “Kalmomin [da ke 1 Yohanna 5:7] sun bayyana a na Latin kawai, ba su bayyana a juyin (Syriac da Coptic da Armenian da Ethiopic da Arabic da kuma Slavonic) ba.” A sakamakon haka, juyin King James Version da aka buga kwana-kwanan nan ba ya ɗauke da waɗannan kalmomin.

Chester Beatty shafi na 46, Littafi Mai Tsarki da aka rubuta a takardar ganye a wajen shekara ta 200 B.H.Y.

Shin littattafai na dā na Littafi Mai Tsarki sun ba da tabbaci cewa ba a canja saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba? Saʼad da aka gano Naɗaɗɗun Littattafai na Tekun Gishiri a shekara ta 1947, masana sun sami zarafin gwada juyin Masoretic na Ibrananci da kuma wasu tsofaffin littattafai da aka kofa fiye da shekara dubu kafin lokacin. Wani cikin mutanen da suka yi bincike a kan Naɗaɗɗun Littattafai na Tekun Gishiri ya ce littafi guda “ya ba da tabbaci cewa Yahudawan da suka yi sama da shekara dubu ɗaya suna kofe Littafi Mai Tsarki, sun yi aiki mai kyau sosai kuma ba su ƙara gishiri ba.”

Laburaren nan Chester Beatty da ke birnin Dublin, a ƙasar Ireland yana ɗauke da littattafan ganye na kusan dukan littattafan Nassosin Helenanci, har da waɗanda aka rubuta a ƙarni na biyu bayan haihuwar Yesu, wato wajen shekara 100 bayan da aka kammala rubutun Littafi Mai Tsarki. Wani ƙamus mai suna The Anchor Bible Dictionary ya ce: ‘Ko da yake littattafan suna ɗauke da wasu sababbin bayanai game da Littafi Mai Tsarki, amma sun sa mun kasance da tabbaci cewa ba a canja saƙon da ke cikinsa ba.ʼ

“Littafi Mai Tsarki ne kaɗai littafi na zamanin dā da za mu iya furtawa da tabbaci cewa ba a canja saƙon da ke cikinsa ba”

SAKAMAKO: Kofofi da yawa na Littafi Mai Tsarki da kuma yadda suka daɗe sun inganta saƙon da ke cikinsa maimakon su ɓata shi. Wani mai suna Sir Frederic Kenyon ya ce game da Nassosin Helenanci: “A cikin dukan littattafan da aka taɓa wallafawa, Littafi Mai Tsarki ne littafin da ya fi kasancewa da bayanan da suka nuna cewa saƙon da ke cikinsa gaskiya ne, kuma babu mutumin da zai iya cewa an canja saƙon da ke cikinsa.” William Henry Green kuma ya ce game da Nassosin Ibrananci: “Littafi Mai Tsarki ne kaɗai littafi na zamanin dā da za mu iya furtawa da tabbaci cewa ba a canja saƙon da ke cikinsa ba.”

^ sakin layi na 6 Don ƙarin bayani ka duba sashe na 1 da 2 na ƙasidar nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah. Za ka iya samunsa a www.jw.org/ha.