HASUMIYAR TSARO Na 4 2016 | Yadda Aka Kāre Littafi Mai Tsarki

A cikin karnuka da yawa da suka shige, da abubuwa da dama sun halaka Littafi Mai Tsarki ko sakon da ke cikinsa. Amma me ya sa yadda aka kāre shi yake da muhimmanci a gare mu?

COVER SUBJECT

Labari Mai Muhimmanci

Babu wani littafi da ya dade yana gyara rayuwar mutane da yawa kamar Littafi Mai Tsarki. Shin za mu iya gaskata da Littafi Mai Tsarki?

COVER SUBJECT

Littafi Mai Tsarki Bai Rube Ba

Marubutan Littafi Mai Tsarki da wadanda suka kofe littafin sun yi amfani da ganye da kuma fatu wajen yin hakan. Ta yaya dubban littattafan Littafi Mai Tsarki na dā suka tsira har zuwa yau?

COVER SUBJECT

’Yan Hamayya Sun Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki

’Yan siyasa da malaman addinai da yawa sun yi kokarin hana mutane kasancewa da Littafi Mai Tsarki da buga ko kuma fassara shi, amma ba su yi nasara ba.

COVER SUBJECT

An Kasa Canja Sakon da Ke Cikin Littafi Mai Tsarki

Wasu mugayen mutane sun yi kokarin canja sakon da ke Littafi Mai Tsarki. Ta yaya kokarce-kokarcensu ya bi ruwa?

COVER SUBJECT

Me Ya Sa Aka Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki?

Me ya sa wannan littafin ya zama dabam da sauran littattafai?

Ka Sani?

Me ya sa yadda Yesu ya bi da kutare ya yi dabam da yadda wasu suka bi da su? Wadanne laifuffuka ne limaman Yahudawa suka ce za su iya sa a kashe aure?

Zai Yiwu a Daina Zalunci a Duniya Kuwa?

An taimaka wa mutane su daina zalunci. Abin da ya taimaka musu zai iya taimaka mana.

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Na Ji Jiki Sosai Kafin Na Yi Nasara

Ta yaya Josef ya daina kallon hotunan batsa kuma ya kasance da kwanciyar hankali?

Bincike Mafi Muhimmanci da Kake Bukatar Ka Yi

Darikoki dubbai na Kirista suna da ra’ayoyi dabam-dabam. Ta yaya za ka gane wanda yake koyar da gaskiya?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Shin Allah yana amfani da wata kungiya ce wajen jawo mutane wurinsa?

Ƙarin Abubuwan da Muke da Su

Littafi Mai Tsarki Daga Wurin Allah ne?

Marubutan Littafi Mai Tsarki da yawa sun ɗaukaka Allah game da abin da suka rubuta. Me ya sa?