Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA ZA MU JIMRE SA’AD DA WANI YA RASU

Yadda Za Ka Sami Ta’aziya

Yadda Za Ka Sami Ta’aziya

Akwai shawara da yawa a kan wannan batun. Amma ba dukansu ba ne suke da amfani. Alal misali, wasu za su ce kada ka yi kuka ko ka nuna cewa kana baƙin ciki. Wasu kuma za su ce ka yi kuka kuma ka nuna kana baƙin ciki sosai. Littafi Mai Tsarki ya ba da wata shawara mai kyau da wasu ‘yan bincike na zamani suka yarda da ita.

Wasu al’adu suna da ra’ayin cewa duk namijin da ya yi kuka ba jan namiji ba ne. Shin abin kunya ne a yi kuka a cikin jama’a? Likitoci sun ce zub da hawaye sa’ad da ake makoki ba laifi ba ne. Kuma yin makoki zai taimaka maka ka ci gaba da rayuwa kome tsananin baƙin cikin da kake yi. Za mu yi wa kanmu lahani idan muka ƙi yin kuka. Littafi Mai Tsarki bai goyi bayan ra’ayin nan cewa laifi ne a yi kuka ko kuma jan namiji ba ya kuka ba. Ka yi la’akari da Yesu. Ko da yake yana da ikon ta da amininsa Li’azaru daga mutuwa, ya yi kuka a cikin jama’a!​—⁠Yohanna 11:​33-35.

Makoki yakan iya sa mutum ya riƙa fushi musamman idan rasuwar ta zo ba zato ba tsammani. Mai makokin zai iya yin fushi idan wasu da yake gani da mutunci suka yi wani furucin da bai dace ba. Wani mutum mai suna Mike daga Afirka ta Kudu ya ce: “Ina ɗan shekara 14 a lokacin da mahaifina ya rasu. Sa’ad da ake jana’izarsa, wani limamin cocin Angilika ya ce Allah yana son mutane masu kirki ne a sama shi ya sa yake ɗaukan su da sauri. * Hakan ya ba ni haushi sosai don har ila, muna bukatar mahaifinmu ya kasance da mu. Yanzu shekaru 63 bayan rasuwar mahaifina, ina baƙin ciki.”

A wasu lokuta mutane sukan ga kamar suna da laifi. Alal misali, mutumin da yake makokin zai iya yin tunani cewa, ‘Wataƙila da bai rasu ba da a ce na yi abu kaza,’ musamman idan rasuwar ta faru ba zato ba tsammani. Ƙari ga haka, za ka iya ganin kanka da laifi idan wataƙila kun yi gardama kafin ya rasu.

Idan kana yin irin wannan tunanin kuma kana fushi, bai kamata ka ɓoye hakan a zuciyarka ba. A maimakon haka, ka gaya wa amininka da zai saurare ka kuma ya tabbatar maka da cewa haka masu makoki suke yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aboki kullayaumi ƙauna ya ke yi, kuma an haifi ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.”​—⁠Misalai 17:⁠17.

Aminin ƙwarai da mutum zai kasance da shi shi ne Mahaliccinmu Jehobah. Ka gaya masa dukan damuwarka don ‘yana kula da kai.’ (1 Bitrus 5:⁠7) Ƙari ga haka, ya yi alkawari cewa duk waɗanda suka yi hakan za su sami “salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta.” (Filibiyawa 4:​6, 7, Littafi Mai Tsarki) Har ila, ka dogara ga Allah da kuma Littafi Mai Tsarki don ya taimaka maka ka rage baƙin cikin da kake yi. Ka rubuta wasu nassosin da za su iya ƙarfafa ka. (Ka duba akwatin da ke ƙasa.) Za ka iya haddace wasu  cikin nassosin. Kasancewa da waɗannan nassosin a zuciya zai iya taimaka maka musamman daddare sa’ad da kake tunani kuma ka kasa yin barci.​—⁠Ishaya 57:⁠15.

A kwana-kwanan nan, matar wani mutum da za mu kira shi Jack ta rasu sanadiyyar cutar kansa. Jack ya ce a wasu lokuta yana fama da kaɗaici sosai. Amma addu’a tana taimaka masa. Ya ce: “Sa’ad da na yi addu’a ga Jehobah, sai in ji sauƙi. Sau da yawa nakan tashi daddare kuma in kasa yin barci. Amma idan na karanta nassosi kuma na yi bimbini a kansu tare da gaya wa Jehobah yadda nake ji, sai na sami kwanciyar hankali kuma hakan yana sa in yi barci.”

Mahaifiyar wata matashiya mai suna Vanessa ta rasu sanadiyyar rashin lafiya. Ita ma yin addu’a ya taimaka mata. Ta ce: “A wasu lokutan da nake baƙin ciki sosai, ina kiran sunan Jehobah kawai kuma in zub da hawaye. Jehobah ya ji addu’ata kuma ya taimaka mini sosai.”

Wasu masana sun ce abin da zai iya taimaka shi ne ba da kai wajen yin ayyukan da za su iya taimaka wa jama’a. Yin irin waɗannan ayyukan za su iya sa mutumin da ke makoki ya kasance da farin ciki kuma ya ɗan manta da yanayin da yake ciki. (Ayyukan Manzanni 20:35) Kiristoci da yawa da suke makoki sun gano cewa taimaka wa mutane yana sa su sami ta’aziya sosai.​—⁠2 Korintiyawa 1:​3, 4.

^ sakin layi na 5 Littafi Mai Tsarki bai koyar da hakan ba, amma ya faɗi dalilin da ya sa mutane suke mutuwa.​—⁠Mai-Wa’azi 9:11; Yohanna 8:44; Romawa 5:⁠12.