Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA ZA MU JIMRE SA’AD DA WANI YA RASU

Yadda Za a Ta’azantar da Masu Makoki

Yadda Za a Ta’azantar da Masu Makoki

Ka taɓa rasa abin da za ka gaya wa wani da yake makoki? A wasu lokuta idan ba mu da na cewa, muna zuba ido ne kawai. Amma akwai wasu abubuwa masu kyau da za mu iya yi.

A yawancin lokaci, abin da kake bukata ka ce shi ne “Ka yi haƙuri.” A al’adu da yawa, hanyar nuna cewa ka damu da mai makoki shi ne rungumar shi ko kuma riƙe shi a kafaɗa. Idan mai makokin yana son ya yi magana, ka saurare shi. Abu mafi amfani shi ne taimaka wa iyalin, za ka iya ka ziyarce su kuma ka taya su yin wasu aikace-aikace kamar su dafa abinci da kula da yara ko kuma taimaka wajen yin shirye-shiryen jana’izar idan suna so. Waɗannan ayyukan da za ka yi za su iya ma fin abin da za ka faɗa.

Bayan wani lokaci, za ka iya samun zarafin faɗin wasu abubuwa masu kyau game da mamacin. Irin wannan hirar za ta iya sa mai makokin ya yi farin ciki. Alal misali, wata mata mai suna Pam ta rasa mijinta shekaru shida da suka shige. Ta ce: “A wasu lokuta, mutane sukan gaya mini wasu abubuwa masu kyau da maigidana ya yi da ban sani ba kuma hakan yana sa ni farin ciki sosai.”

 Masana sun gano cewa mutane sukan taimaka wa masu makoki a lokacin da aka musu rasuwa, amma bayan haka, sai kowa ya manta da su. Saboda haka, zai dace ka riƙa ta’azantar da mai makokin a kai a kai. * Masu makoki da yawa suna son hakan don yana taimaka musu su rage baƙin cikin da suke yi.

Ka yi la’akari da misalin Kaori, wata matashiya ‘yar ƙasar Jafan da take baƙin ciki sosai don mahaifiyarta ta rasu. Bayan shekara ɗaya da wata uku, sai yayarta ma ta rasu. Abin farin ciki shi ne aminanta sun ta’azantar da ita sosai. Wata daga cikin aminanta mai suna Ritsuko ta girme ta sosai. Wannan matar ta amince ta zama aminiyarta. Kaori ta ce: “A gaskiya ban so hakan ba. Ban so wata ta ɗauki matsayin mahaifiyata ba kuma ban taɓa tunanin cewa akwai wadda za ta iya yin hakan ba. Amma yadda matar ta bi da ni ya sa na kusace ta sosai. Kowane mako muna zuwa taro da kuma wa’azi tare. Takan gayyace ni don mu sha shayi tare kuma tana kawo mini abinci da kuma tura min wasiƙu da katuna. Hali mai kyau da ta nuna mini ya taimaka mini sosai.”

Shekaru sha biyu ke nan da rasuwar mahaifiyar Kaori, kuma ita da maigidanta suna wa’azi na sa’o’i saba’in kowane wata. Kaori ta ce: “Ritsuko ta ci gaba da kula da ni. Ƙari ga haka, nakan ziyarce ta kuma ina jin daɗin tarayya da ita sa’ad da na koma gida.”

Wani misali kuma shi ne na wata Mashaidiyar Jehobah da ke ƙasar Cyprus mai suna Poli, ita ma ta amfana daga taimakon da aka yi mata. Maigidan Poli mai suna Sozos kuma mutumin kirki ne da yake gayyatar marayu da gwauraye zuwa gidansa don su ɗan shaƙata ko kuma su ci abinci. (Yaƙub 1:27) Amma abin baƙin ciki shi ne, da Sozos ya kai shekaru 53 sai ya rasu sanaddiyar ciwon kansa na ƙwaƙwalwa. Poli ta ce: “Ban ji daɗin rasuwar maigidana da muka yi shekaru 33 da aure ba.”

Ka nemi hanyoyin da za ka ƙarfafa masu makoki

Bayan jana’izar, sai Poli ta ƙaura zuwa Kanada da autanta ɗan shekara 15 mai suna Daniel. A can, suka ci gaba da tarayya da Shaidun Jehobah. Poli ta ce: “Aminan da muka samu a nan ba su san abin da ya same mu da kuma irin yanayi mai wuya da muke ciki ba. Duk da haka, sun yi ta zuwa wurin mu da kuma taimaka mana. Mun ji daɗin wannan taimakon musamman sa’ad da ɗana Daniel yake kewar mahaifinsa sosai! Dattawan ikilisiyarmu sun taimaka wa Daniel sosai. Akwai ɗaya daga cikinsu da yake gayyatar Daniel a duk lokacin da ya gayyaci abokansa don shaƙatawa ko kuma su buga ƙwallo.” Poli da ɗanta suna bauta wa Jehobah da aminci har yau.

Babu shakka, akwai hanyoyi da yawa da za mu iya taimaka wa masu makoki kuma mu ta’azantar da su. Begen tashin matattu da Littafi Mai Tsarki ya yi maganarsa yana ƙarfafa mu sosai.

^ sakin layi na 6 Wasu sukan rubuta kwanan watan a kalandarsu don su riƙa tunawa da lokacin da ya kamata su ta’azantar da mai makokin.