Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU | RIFKATU

“Zan Tafi”

“Zan Tafi”

RIFKATU ta zauna a kan rakumi tana lura da yadda rana take faɗiwa. Ta soma sabawa da zama a kan rakumi bayan sun yi makonni suna tafiya. Sun yi tafiyar ɗarurruwan mil daga Haran kuma sun nufi arewa masu gabas. Wataƙila ba za ta sake ganin danginta ba. Babu shakka, tana ta tunanin yadda rayuwarta za ta kasance da yake sun kusa isa garin da za su je.

Matafiyan sun wuce garuruwan da ke ƙasar Kan’ana kuma sun kai Negeb, wuri mai haɗari sosai. (Farawa 24:62) Babu mamaki, Rifkatu ta ga tumaki a wurin domin akwai ciyawa sosai da dabbobi za su iya ci. Amma yin noma zai yi wuya don yanayin ƙasar. Dattijon da ke mata ja-gora ya san wurin sosai. Yana farin ciki don yana da albishirin da zai gaya wa Ubangidansa. Wane albishiri ke nan? Rifkatu ce za ta zama matar Ishaƙu. Babu shakka, Rifkatu ta yi tunani: ‘Wace irin rayuwa ce zan yi a wannan ƙasar? Wane irin mutum ne angona Ishaƙu, tun da yake ba mu taɓa ganin juna ba? Zai so ni idan ya gan ni? Ni fa, zan so shi idan na gan shi?’

Ba a saba irin wannan auren a wasu ƙasashe a duniya ba. A wasu wurare kuma hakan ba baƙon abu ba ne. Ko daga ina ka fito, babu shakka za ka amince da cewa Rifkatu ba ta san irin yanayin da za ta shiga ba. Babu shakka, tana da ƙarfin zuciya da kuma bangaskiya. Muna bukatar waɗannan halayen sa’ad da yanayinmu ya canja. Akwai wasu halaye masu kyau da Rifkatu take da su da mutane da yawa a yau ba su da su.

‘KUMA ZAN ƊIBA WA RAƘUMANKA’ RUWA

Canjin da Rifkatu ta fuskanta a rayuwarta ya soma ne a lokacin da ta yi wani abu da ta saba yi. Ta yi girma ne a birnin Haran da ke yankin Mesopotamiya ko kuma kusa da birnin. Halin iyayenta ya yi dabam da na yawancin mutanen da suke Haran. Ba sa bauta wa allahn wata mai suna Sin. A maimakon haka, suna bauta wa Jehobah.​—Farawa 24:50.

Rifkatu kyakkyawar budurwa ce amma kyanta ba na fuska ba ne kawai. Ita mai ƙwazo ce kuma tana da ɗabi’a mai kyau. Ko da yake iyalinta suna da kuɗi sosai kuma suna da bayi, ba su bi da ta ita kamar gimbiya ba, a maimakon haka, sun koya mata yin aiki da ƙwazo. Rifkatu tana aiki sosai kamar su ɗebo ruwa yadda wasu mata suke yi a dā. Da yamma, takan ɗauki tulu ta je rijiya don ta ɗebo ruwa.​—Farawa 24:​11, 15, 16.

Wata rana da yamma da take ɗiban ruwa, sai wani dattijo ya yi sauri zuwa wurinta, ya ce: “Ki ba ni ruwa kaɗan, ina roƙonki, daga cikin tulunki, in sha.” Abin da dattijon ya roƙa bai fi ƙarfinta ba! Rifkatu ta lura cewa mutumin ya yi tafiya mai nisa kuma ya gaji. Nan da nan sai Rifkatu ta sauƙe tulunta kuma ta ba mutumin ruwa mai sanyi ya sha. Ta lura cewa yana da rakuma goma a gefe kuma ba a ɗebo musu ruwan da za su sha ba. Ƙari ga haka, ta ga yadda dattijon yake kallonta da fara’a kuma ta yi iya ƙoƙarinta don ta yi masa karimci. Sai ta ce masa: “Zan ɗiba wa raƙumanka kuma, har su gama sha.”​—Farawa 24:​17-19.

Ka lura cewa Rifkatu ba ta ce za ta ba rakuman ruwa kawai ba, amma ta ce har sai ruwan ya ishe su. Idan rakumi yana ƙishirwa, zai iya shan fiye da galan 25, wato wajen rabin duro na ruwa. Kuma idan rakuman guda goma suna jin ƙishirwa sosai, Rifkatu za ta yi aiki tuƙuru don ta shayar da su. Kuma labarin ya nuna cewa rakuman sun ji ƙishi sosai. * Amma kana ganin Rifkatu ta san cewa rakuman suna jin ƙishi sosai ne a lokacin da ta ce za ta ba su ruwa? A’a. Duk da haka, ta yarda ta nuna wa wannan dattijon karimci. Shi kuma ya yi farin ciki da hakan. Sai ya yi ta kallonta sa’ad da take kai da kawowa don ta ba rakuman ruwa su sha.​—Farawa 24:​20, 21.

Rifkatu tana da ƙwazo da kuma karimci

Mu ma za mu iya amfana sosai daga labarin Rifkatu. Muna rayuwa a zamanin da son kai ya zama ruwan dare gama gari. Kamar yadda aka annabta, mutane sun zama “masu-son kansu,” kuma ba sa son su taimaka wa wasu. (2 Timotawus 3:​1-5) Ya kamata Kiristocin da suke son su guji halin son kai su yi la’akari da yadda wannan budurwar ta yi ta kai-da-kawowa don ta ba rakuman ruwa.

Babu shakka, Rifkatu ta lura cewa wannan dattijon yana kallonta. Kuma yana kallon ta ne domin ya cika da mamaki da kuma farin ciki. Sa’ad da Rifkatu ta gama shayar da rakuman, sai dattijon ya ba ta kyautar kayan ado na zinariya. Sai ya tambaye ta: “ ’Yar wanene ke? Ki faɗa mani, ina roƙonki. Ko da akwai wurin da za mu sauka a cikin gidan ubanki?” Sa’ad da ta ba shi amsa, sai ya daɗa farin ciki. Ita ma da farin ciki ta ƙara da cewa: “Muna da yalwar ingirici da harawa har da ɗakin sauka kuma.” Wannan babban gayyata ne domin dattijon yana tare da wasu. Sai ta sheƙa da gudu zuwa gida don ta gaya wa mahaifiyarta abin da ya faru.​—⁠Farawa 24:​22-28, 32.

Hakika, iyayen Rifkatu ne suka koya mata yin karimci. Yawancin mutane ba su da irin wannan halin a zamanin nan ko da yake hali ne mai kyau da ya kamata mu yi koyi da shi. Kasancewa da bangaskiya ga Allah zai sa mu zama masu karimci. Jehobah mai karimci ne kuma yana ba kowa abin biyan bukata, saboda haka, yana son mu yi koyi da shi. Jehobah zai yi farin ciki idan muka nuna karimci har ga talakawa.​—⁠Matta 5:​44-46; 1 Bitrus 4:⁠9.

“KA ƊAUKA WA ƊANA ISHAƘU MATA”

Waye ne dattijon nan da yake baƙin rijiya? Shi bawan ɗan’uwan kakan Rifkatu ne mai suna Ibrahim. Saboda haka, baban Rifkatu, wato Bethuel ne ya karɓe shi a gidansa. Wataƙila sunan wannan bawan Eliezer ne. * Baban Rifkatu ya ba wannan bawan abinci amma ya ƙi ci, sai da ya gaya masa dalilin zuwansa. (Farawa 24:31-33) Babu shakka, za ka iya yin tunanin yadda yake masa magana da farin ciki da yake ya ga yadda Jehobah yake goya masa baya don ya cim ma maƙasudinsa. Ta yaya?

Ka yi tunanin yadda Bethuel, baban Rifkatu da kuma ɗan’uwanta Laban, suke saurarawa sa’ad da Eliezer yake ba su labarin abin da ya faru. Ya gaya musu cewa Jehobah ya albarkaci Ibrahim sosai a Kan’ana kuma Ibrahim da Saratu sun sami ɗa mai suna Ishaƙu, wanda zai zama magaji. Ibrahim ya ba shi wani aiki mai muhimmanci, wato ya nemo wa Ishaƙu mata daga danginsa da ke Haran.—Farawa 24:34-38.

Ibrahim ya sa Eliezer ya rantse cewa ba zai nemo wa ɗansa Ishaƙu, mata daga matan Kan’ana ba. Me ya sa? Domin Kan’aniyawa ba sa bauta wa Jehobah. Ibrahim ya san cewa Jehobah zai hukunta waɗannan miyagun mutanen a nan gaba. Don haka, ba ya son ɗansa da yake ƙauna ya yi abota da waɗannan mutanen da ba su da ɗabi’a mai kyau. Ya kuma san cewa ɗansa yana da matsayi mai muhimmanci wajen sa nufin Allah ya tabbata.—Farawa 15:16; 17:19; 24:​2-4.

Eliezer ya gaya musu cewa sa’ad da ya isa rijiyar da ke kusa da Haran, sai ya yi addu’a ga Jehobah don ya zaɓa wa Ishaƙu mata. Ta yaya ya yi hakan? Ya ce Allah ya sa matar da Ishaƙu zai aura ta zo ɗiban ruwa a rijiyar. Kuma idan ya roƙe ta ruwan sha, ta ba shi da kuma rakumansa. (Farawa 24:​12-14) Wace ce ta zo ta yi dukan waɗannan abubuwan? Rifkatu ce! Ka yi tunanin yadda Rifkatu ta yi farin ciki, yayin da ta ji Eliezer yana gaya wa iyalinta wannan labarin.

Bethuel da kuma Laban sun ji daɗin labarin da Eliezer ya ba su. Sai suka ce: “Al’amarin nan daga wurin Ubangiji yake.” Kamar yadda suka saba yi a al’adarsu, sai suka amince a ɗaura wa Rifkatu da Ishaƙu aure. (Farawa 24:​50-54) Shin hakan yana nufin cewa Rifkatu ba ta da na cewa ne a wannan batun?

A ‘yan makonni da suka shige, Eliezer ma ya ce wa Ibrahim: “Wataƙila macen ba za ta yarda ta biyo ni ba.” Sai Ibrahim ya ce masa: ‘Ka kuɓuta ke nan daga rantsuwar.’ (Farawa 24:​39, 41) Ita ma Rifkatu tana da zaɓi ko a gidan mahaifinta. Eliezer ya yi farin ciki sosai da nasarar da Jehobah ya ba shi. Shi ya sa washegari da safe, ya ce a ba shi Rifkatu nan da nan don ya koma ƙasar Kan’ana. Amma iyalinta sun so ta ɗan zauna aƙalla na kwana goma. Daga baya, sai suka ce: “Bari mu kira yarinyar, mu ji a bakinta.”​—⁠Farawa 24:⁠57.

Wannan babbar shawara ce da Rifkatu take bukatar ta tsai da. Me za ta ce? Kana ganin za ta bi ra’ayinta mahaifinta ne da kuma ɗan’uwanta da suka ce ta ɗan zauna na kwana goma? Ko kuma za ta bi ra’ayin wannan bawan kuma ta ɗauki wannan a matsayin babban gata, da yake Jehobah yana goyon bayansa? Amsar da ta bayar ya nuna yadda ta ji game da babban canjin da ya faru a rayuwarta farat ɗaya. Ta ce: “Zan tafi.”—Farawa 24:58.

Hakika, ta nuna hali mai kyau sosai. Za mu iya koyan darussa daga labarin Rifkatu ko da yadda ake aure a yankinmu ya yi dabam. Abin da ya fi mata muhimmanci ba ra’ayinta ba ne amma na Allahn da take bauta masa, Jehobah. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da shawarwari masu kyau game da aure. Ya nuna irin mata ko mijin da za mu aura da kuma yadda za mu zama miji ko kuma macen kirki. (2 Korintiyawa 6:​14, 15; Afisawa 5:​28-33) Ya kamata mu bi misalin Rifkatu kuma mu riƙa yin abubuwa yadda Allah yake so.

“WANE NE MUTUMIN CAN?”

Iyayen Rifkatu sun albarkace ta. Sai Rifkatu da wata da ta yi rainonta tun tana ƙarama, mai suna Deborah da wasu ‘yan mata suka bi Eliezer da mutanensa. (Farawa 24:​59-61; 35:⁠8) Kafin a ce kwabo, sun bar Haran. Wannan tafiya ce ta mil 500 (kilomita 800) ko fiye da hakan, kuma wataƙila sun yi makonni uku suna tafiyar. Tafiyar ba ta da sauƙi. Ko da yake Rifkatu ta saba ganin rakuma, amma ba za mu iya ce ta ƙware a hawan su ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa iyalinsu makiyaya ne ba masu zuwa kasuwanci a kan rakuma ba. (Farawa 29:10) Masu koyan hawan rakumi suna yawan cewa sun gaji, bayan sun zauna a kan rakumi na ɗan lokaci!

Babu shakka, Rifkatu ta yi ta tambayar Eliezer, wasu abubuwa game da Ishaƙu da kuma iyalinsu. Ka yi tunanin yadda wannan dattijo yake mata bayani game da alkawarin da Jehobah ya yi wa amininsa Ibrahim, sa’ad da suke shan ɗumi daddare. Ya gaya mata cewa Allah ya yi wa Ibrahim alkawarin ɗa wanda zai sa mutanen duniya duka su sami albarka. Ka yi tunanin yadda Rifkatu ta ji sa’ad da ta fahimci cewa Jehobah zai cika alkawarinsa ta wurin wanda za ta aura, wato Ishaƙu da kuma ita.​—Farawa 22:​15-18.

Rifkatu tana da halin da ake ƙarancinsa sosai a yau, wato tawali’u

A ƙarshe, ranar da muka kwatanta a farkon wannan talifin ta zo. Yayin da matafiyan suka kusan wuce Negeb kuma gari ya soma duhu, sai Rifkatu ta hango wani mutum yana tafiya cikin daji yana tunani. Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa da ganin sa, sai Rifkatu “ta sauka daga bisa raƙumin,” wataƙila ba ta ma jira rakumin ya kwanta ba. Sai ta tambaye shi: “Wane ne mutumin can da ke zuwa daga saura garin ya tarye mu?” Da aka gaya mata cewa Ishaƙu ne, sai ta yi lulluɓi da mayafinta. (Farawa 24:​62-65, Littafi Mai Tsarki) Me ya sa? Wataƙila hakan alamar ladabi ne ga mijin da za ta aura. Wasu a yau za su iya ganin cewa hakan tsohon yayi ne. Babu shakka, maza da mata za su iya koyan darasi daga tawali’un da Rifkatu ta nuna domin wannan hali ne da kowa yake so, ko ba haka ba?

Ishaƙu yana wajen shekara arba’in kuma bai daina makokin mahaifiyarsa Saratu da ta rasu shekaru uku da suka shige ba. Hakan ya nuna cewa Ishaƙu mutumi ne mai tausayi sosai. Babu shakka, mata mai ƙwazo da karimci da kuma tawali’u da Allah ya ba shi, ta dace da shi sosai. Yaya suka bi da juna? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya kuwa ƙaunace ta.”—Farawa 24:67; 26:8.

Muna son halin da Rifkatu ta nuna ko da yake ta rayu wajen shekaru 3,900 da suka shige. Ba abin da za mu ce sai da mu yaba mata don ƙarfin halinta da ƙwazonta da karimcinta da kuma tawali’unta, ko ba haka ba? Saboda haka, ya kamata dukanmu maza da mata, matasa da tsofaffi, ma’aurata da kuma waɗanda ba su yi aure ba mu yi koyi da bangaskiyarta!

^ sakin layi na 10 Yamma ya riga ya yi a lokacin. Amma labarin bai nuna cewa Rifkatu ta daɗe a baƙin rijiyar ba. Kuma bai ce kafin ta koma gida iyayenta sun riga sun yi barci ba ko kuma sun turo wasu su zo neman ta ba.

^ sakin layi na 15 Wataƙila Eliezer ne wannan bawan ko da yake ba a ambata hakan a Littafi Mai Tsarki ba. A lokacin da Ibrahim ba shi da ɗa, ya so ya sa Eliezer ya zama magajinsa. Hakan ya nuna cewa Eliezer ne bawan da Ibrahim ya fi yarda da shi kuma shi ya girme sauran. Wannan kwatancen ya yi daidai da na bawan da ke wannan labarin.—Farawa 15:2; 24:​2-4.