Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA ZA MU JIMRE SA’AD DA WANI YA RASU

Laifi Ne A Yi Makoki?

Laifi Ne A Yi Makoki?

Ka taɓa yin ciwo na ɗan lokaci kuwa? Wataƙila ka warke da wuri har ma ka manta ko ka taɓa yin ciwo. Amma ba haka makoki yake ba. Wani littafi mai suna Healing a Spouse’s Grieving Heart da Dr. Alan Wolfelt ya rubuta ya ce: “Ba zai taɓa yiwu mutum ya ‘daina’ makoki ba.” Amma ya daɗa da cewa: “Bayan wani lokaci, kuma da taimakon wasu, makokin zai ragu.”

Alal misali, ka yi la’akari da yadda Ibrahim ya ji sa’ad da matarsa ta rasu. Da alama cewa ya ɗan jima kafin Ibrahim ya soma warwarewa. * Wani misali kuma shi ne Yakubu da aka ruɗe shi cewa wata dabba ta kashe ɗansa Yusufu. Ya yi makoki na “kwanaki da yawa” kuma danginsa ba su iya ta’azantar da shi ba. Shekaru da yawa bayan haka, Yakubu ya ci gaba da makoki don ɗansa Yusufu.​—⁠Farawa 23:2; 37:​34, 35; 42:36; 45:⁠28.

Ibrahim ya yi makoki sosai sa’ad da matarsa Saratu ta rasu

Mutane da yawa a yau suna makokin danginsu da suka rasu. Ka yi la’akari da misalai biyu na gaba.

  • “Mijina Robert, ya rasu a ranar 9 ga Yuli, 2008, sanadiyyar wata hatsari. A safiyar ranar da ya yi hatsarin, mun yi abin da muka saba yi. Bayan mun karya, mun yi sumba, muka rungumi juna kuma ya ce, ‘Yana so na, ni ma na ce ina son shi,’ bayan haka sai ya tafi aiki. Na yi shekaru shida ina makoki don rasuwarsa. Ina ganin ba zan taɓa daina makokin mijina ba.”​—⁠In ji Gail, mai shekara 60.

  • “Ko da yake matata ta rasu shekaru sha takwas yanzu, har ila ina kewarta kuma ina makokin ta. A duk lokacin da na ga wata halitta mai kyau, ina tunawa da ita domin na san cewa da a ce tana da rai, da ta so halittar sosai.”​—⁠In ji Etienne, mai shekara 84.

Babu shakka, yin makoki na dogon lokaci ba laifi ba ne. Yadda mutane suke makoki ya bambanta, don haka, ba zai dace mu yi fushi sa’ad da wani ya daɗe yana makoki ba. Kuma bai kamata mu ga kanmu da laifi don muna makoki na dogon lokaci ba. Ta yaya zan sami ta’aziya?

^ sakin layi na 4 Ishaƙu ɗan Ibrahim ma ya yi makoki na dogon lokaci. Kamar yadda muka gani a talifin “Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu” da ke wannan Hasumiyar Tsaro, Ishaƙu ya yi shekaru uku yana makokin mahaifiyarsa Saratu.​—⁠Farawa 24:⁠67.