Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda sunan Allah yake (wurin da aka yi maki) a Littafi Mai Tsarki na dā

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Allah yana da suna kuwa?

WASU SUN CE ba shi da suna, wasu kuma sun ce sunansa Allah ne ko kuma Ubangiji. Ƙari ga haka, wasu sun ce yana da sunaye da yawa sosai. Mene ne ra’ayinka?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.”—Zabura 83:18.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Allah ya ba kansa suna guda ɗaya tak ko da yake yana da laƙabi da yawa.—Fitowa 3:15.

  • Allah yana son mu san shi kuma shi ba wani da ba za mu iya saninsa ba ne.—Ayyukan Manzanni 17:27.

  • Sanin sunan Allah shi ne abu na farko da mutum zai yi idan yana son ya zama amininsa.—Yaƙub 4:8.

Shin laifi ne mu kira sunan Allah?

ME ZA KA CE?

  • E

  • A’a

  • Ya dangana ga yanayin

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

‘Ba za ka kama [wato kira] sunan Ubangiji Allahnka a banza ba.’ (Fitowa 20:7) Laifi ne mu yi amfani da sunan Allah a hanyar da ba ta dace ba.—Irmiya 29:9.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Ibrahim da Yesu sun san sunan Allah kuma sun yi amfani da shi.—Farawa 15:2; Yohanna 17:​25, 26.

  • Allah yana son mu yi amfani da sunansa.—Zabura 105:1.

  • Magabtan Allah suna ƙoƙari su sa mutane su manta da sunan Allah.—Irmiya 23:27.