Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA KARƁI KYAUTA MAFI DARAJA DAGA ALLAH?

Yaya Za Ka Nuna Godiya don Kyauta Mafi Daraja?

Yaya Za Ka Nuna Godiya don Kyauta Mafi Daraja?

‘Ƙaunar Almasihu gare mu ita ke mallakarmu, . . . Ya mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda ke raye, kada su yi zaman ganin dama nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su.’2 Korintiyawa 5:14, 15, Littafi Mai Tsarki.

IDAN aka ba mu kyauta mai daraja sosai, ya kamata mu nuna godiya. Yesu ya nanata amfanin yin hakan bayan da ya warkar da maza goma da suke fama da wata mummunar cuta da babu maganinta a lokacin. A cikin mazan goma, guda ɗaya ne kawai “ya komo, yana ta ɗaukaka Allah da murya mai ƙarfi.” Sai Yesu ya ce: “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina taran?” (Luka 17:12-17, LMT) Mene ne darasin? Muna iya saurin manta abubuwa masu kyau da mutane suka yi mana!

Kyautar fansa ba kamar kowace irin kyauta ba ce. Babu wata kyauta da ta fi wannan daraja a duniya. Amma ta yaya za ka nuna godiya ga abin da Allah ya yi maka?

  • Ka san Wanda ya ba da kyautar. Ba haka kawai ne fansar za ta ba ‘yan Adam rai na har abada ba. Amma, sa’ad da Yesu yake addu’a ya ce: ‘Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.’ (Yohanna 17:3) Idan ka ji cewa wani ya cece ka sa’ad da kake yaro, shin ba za ka so ka san game da wannan mutumin da kuma dalilin da ya sa ya cece ka ba? Wanda ya ba mu wannan fansar, wato Jehobah Allah, yana so mu san shi kuma mu ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu cewa: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.”Yaƙub 4:8.

  • Ka ba da gaskiya ga fansar. “Wanda yana ba da gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada.” (Yohanna 3:36) Mene ne ba da gaskiya yake nufi? Yana nufin yin abubuwan da suka nuna cewa mun ba da gaskiya ga hadayar Yesu. (Yaƙub 2:17) Alal misali, idan aka ba ka kyauta, kyautar ta zama naka sa’ad da ka miƙa hannu ka karɓe ta. Hakazalika, kana bukatar ka amince da fansar Yesu. Ta yaya? Ka koyi game da yadda Allah yake so ka yi rayuwa kuma ka bi abin da kake koya. * Ka roƙi Allah ya gafarta maka kuma ya ba ka lamiri mai kyau. Sa’ad da kake yin addu’a ga Allah, ka kasance da tabbaci cewa fansar Yesu za ta kawo salama da farin ciki a nan gaba ga duk wanda ya ba da gaskiya ga fansar!Ibraniyawa 11:1.

  • Ka halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Yesu ya kafa wani idi da za a riƙa yi kowace shekara don tunawa da fansa. Game da idin, ya ce: “Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.” (Luka 22:19, LMT) Shaidun Jehobah za su yi taron tunawa da mutuwar Yesu a ranar Talata, 11 ga Afrilu, 2017, bayan faɗuwar rana. Taron na awa ɗaya ne kawai kuma za a yi jawabin da zai bayyana dalilin da ya sa mutuwar Yesu take da muhimmanci da kuma yadda za ta kawo mana albarka a yanzu da kuma nan gaba. A shekarar da ta shige, mutane kusan miliyan 20 ne a faɗin duniya suka halarci wannan taron. Muna farin cikin gayyatar ka don mu nuna godiya tare ga kyauta mafi daraja daga Allah.

^ sakin layi na 7 Nazarin Littafi Mai Tsarki ne zai taimaka maka ka san Allah kuma ka kusace shi. Ka tambayi Shaidun Jehobah su gaya maka yadda za ka yi hakan ko kuma ka shiga dandalinmu na www.jw.org/ha.